page 07

1.1K 73 0
                                    

Shigowa tayi gidan tana ta faman cika tana batsewa,ga mamakinta kuwa baya falon,haka yakuma tunzurata matuka,bedroom dinta tashiga ta soma safa da marwa tana tunanin ta ina zata bullo masa,tsam tamike tanufi bedroom dinshi inda ta tarar yana danne dannen wayarshi,shigowarta besa yadena abinda yake yiba sema kara kaimi da yyi,tsaye tamasa aka tana ta faman huci,"lallai Elmoudan kacika mara mutunci."tace tana wani girgije girgirje,be dago ido ya kalleta ba saboda yadda zuciyarshi ke mishi zafi,domin tabbas idan ya biye mata seya daka mata tsinannan duka wanda aganinshi abin Allah wadai ne,"na tabbatar da kunnuwane keji ba idanuwa ba,dan haka daka kalleni dakada ka kalleni uwarsu daya ubansu daya".ko gezau beyi ba kamar badashi take magana ba,daga bisani ma hajiyarshi yakira,"salamualaikum hajiya..."be ankara ba yaji an fizge wayar daga kunnenshi;"wato nika mayar mahaukaciya koh?ina magana kana danne dannen waya sabida banida mutunci da daraja a idanuwanka right?".har yanxu be dago kanshi ya kalleta ba bare tayi tunanin ze amsa ta,mikewa yyi Ya fizge wayar shi sannan yajata har kofar dakin nashi ya jefar tareda saka ma kofar key yadawo yyi zamansa,yana zama kiran hajiya yashigo wayarshi ,banji metace sejinayi yace"ehh inaga network problem ne"...yachigaba da fadin"hajiya kada kidamu pls wallahi end of this week zanzo Inshaallah"...murmushi yyi "toh hajiya"..jim yyi nawasu seconds kafin yace"tace agaidaki"..."haba hajiya kada kice haka mana,dagske nake"..."ameen"naji yace sannan ya kashe wayar tareda dorata kan chess drawer ya tsunduma kogin tunani,tabbas abinda hajiyarshi tafada gaskiya ne,toh meyasa takeyin hakan?a iya zaman su ya tabbatar da shine keyin haquri ba ita ba,shine ke maida komai ba komai ba duk don su zauna lafiya,amma sabida raini she even have the guts to blurnt on me after sharrin data min awurin uwarta,Tabbas Inteesaar tagama raina ni to the extreme core,but she should be very careful because the outcome of her craziness won't be a nice one.yana gama wannan tunanin ya dauki wayarshi yasoma dannawa badon hankalinshi nakai ba,shide yasan yan watannin nan akwai abinda ke damunshi amma ko kashe shi za'ayi baze iya cewa ga damuwarshi ba bayaga matsalarsu da Inteesaar,"Allah ka kawo min saukin radadin da zuciyata kemin"yace yana me lumshe idanuwanshi,bugun haukar daake ma kofarshi ce yasa ya bude idanuwanshi yana kallon kofar da mamaki,Inteeesaar nada hankali kuwa?ya tambayi kanshi yana girgiza kai domin takai shi kololuwa wurin fushi da ita,mikewa yyi tsam ya fita barandar dakin domin jin saukin bugun,kamar amafarki yahangi daya daga cikin yayan Alhaji Suleiman na safa da marwa a barandar dakin,tsayawa yyi yana kallon yadda take tafiya kwata kwata ba irin ta low class babes ba,duk da kankantar shekarunta bashi ze hana ta rikatama kowane irin namiji lissafi ba dubaga ita ba doguwa bace sosai sannan ba gajera ba but fallen in the middle,Caramel ce in complexion,Tanada kyawun daba kowa kedashi ba sede sihirtacce ne,duk kallon dazaki mata kara kyau takeyi ba irin Wannan kyawun me daukar hankali ba sedaga baya ka fara gano munin mutum ba,Allah ya azurtata da figure 8 feature but she's very slim,she's just an epitome of beauty,she has a sweet aura about her,Jidderh can be defined as sweet,caring,loving,silent but talkative as you get to know her,vibrant,elegant,loyal,respect and lots much more,tunani yakeyi metake tunani haka har daze sa ta cikin damuwar nan ?kasani ko tunanin saurayinta take?Noo ya amsa kanshi da kanshi,that isn't possible,yama za'ayi hakan tafaru?no way yace yana kuma kallon sashen da take ,yadade yana kallonta har seda ta shige daki ta rufe barandar,shiko jingina yyi dabango yana sauke wasu irin numfashi kafin daga bisani yakoma cikin dakinshi,alokacin ma har Inteesaar tayi bugun harta gaji ta dena.
*********************
Tabangaren Jidderh kuwa zuciyarta ce taketa faman tsananin harbawa,tana tunanin meyasa ze kirata kawai don ya kalleta?sassanyar ajiyar zuciya ta sauke ahankali domin batasan ta karasa falonsu ba,fadan dataji Mami nayi ne yadawo da ita daga duniyar tunanin data tafi,cikeda rudu take tambayar meke faruwa?cikin dakushashshiyar murya Aneesah tasoma labarta mata cewar Kishiyar Mami ce takuma kira tana tsinewa Mamin albarka Ba irin zagin dabata mata,gamida cin mutunci,wata zazzafar iska Jidderh ta fizgar sannan tace"hope de bbu wanda yakulata?"..ahankali suka girgiza mata kai,itakuma takarisa inda Mamin ke zaune ta zauna tareda rike hannun Mamin tana murzawa ahankali gamida fadin  "Mami dan girman Allah kiyi haqurin nan damuka sanki dashi kichigaba,dan Allah kiyi hakuri ki manta da abinda yafaru yanzu,Tabbas nasan it really hurts amma dan Allah kiyi hakuri,innallaha maassabirin,Mami haquri daya daga cikin kayan marmari ne dabashi da bishiya,se mutum yakai yakawo sannan yakeda wannan irin,Mami idan kaf mutanen duniya zasu taru akanki wallahi babu wanda ya isa acikinsu yamiki abinda Allah be kadarta ba,nufina anan shine Allah yazama gatanki,Allah baze bari acucekiba kodan maraicin iyayenki da kike ciki sannan abu mafi a'ala shine bakya zalunci don haka Allah baze taba barin wasu mugaye suyi nasara akanki ba,nasan haquri nada ciwo dole se an jure an jajirce,Allah ubangiji yasa sanadiyyar haqurin dakikayi yagina miki gida a aljannah,inshaallah babu wanda ya isa yamiki wani mugun abu wallahi don haka ki kwantar da hankalinki domin babu abinda ta isa tamiki"Nannauyan Numfashi Mami tasauke sannan tace "shikenan Allah na nan"tana kaiwa nan ta mike ta wuce bedroom dinta cikeda tsananin bakin ciki,dalilin haka yasa Jidderh fitowa baranda domin samun peace of mind.Tabangaren Inteeesaar kuwa dakin ta takoma tanata faman kuka mai tsuma zuciyar duk wani me sauraro,ita de Allah yagani tana son Elmoudan amma meyasa  yake mata haka?share hawayen dake zubowa daga idanuwanta tayi gamida neman layin aminiyarta Ziyada,unfortunately tajita akashe dahaka bacci barawo ya sace ta da tunani kala kala cikin ranta..Washegari,yau take Friday,Cikin wata brown din shadda wadda tasha aiki Elmoudan yasaka da milk din hula,kyawunsa yadada fitowa tayadda me karatu baya zato,be tsaya bi takan Inteesaar ba yafice abinsa,akofar gida yaga Jidderh na neman mai adedeta sahu kwata kwata bata lura da mutum ba seji tayi ance "hauwa'u "cikin muryarsa mai tsananin zaqi da sa mutum abinda beyi niyya ba,kasa amsa shi tayi saboda yadda yafeta da idanu,"muje"kawai yace sannan yakoma cikin motarshi,ganin basu Aneesah yasa Jidderh yanke shawarar binshi,baya zata shiga kamar jiya setaji yace"kizo nan"ahankali kamar meyin rada,gabanta ne yyi mugun faduwa sannan yyi maganar cikin daure fuska babu halin tamasa gardama,jiki bbu kwari ta shiga gaban motar yaja aguje kamar ze tashi sama,"kin sani latti"...yace batareda ya kalleta ba.(toh ina ruwana ni tunda bani nace kadauke niba?)kamar yasan metace yakuma cewa"koda yake bake kikace na daukeki ba ra'ayin kaina ne"gabantane yakuma faduwa,karde ace yaji metace ne?runtse idanuwanta tayi batareda tace komai,"ke ina miki magana kinyi min shiru?.."..girgiza kai tayi sannan tace a'a,wani uban tsaki yasaki daga nan be kuma cewa komai har suka karisa makarantar,yanaji tamasa thank you amma ko kallon inda take beyi ba yakuma jan motarshi da mataiyacin gudu kamar ze tashi sama.

LABARIN JIDDERH Where stories live. Discover now