page 09

1.2K 61 0
                                    


   Shiga gidan yyi yana mamakin Me Ziyada tazo ta kulla masa?share gumin kan goshinsa yyi sannan ya cire hularsa ya ajiyeta agefe,Sam be yarda da Ziyada ba inba haka ba what brought her to his house?lallai Inteesaar agaisheki yafada yana jinjina kai,tana ganin kamar tana da wayau batasan ita wawiya bace,ta sakankance da k'awar dake kokarin ruguza alakarsu,ta aminta da k'awar datake kawo masa farmaki bbu dare bbu rana Ta aminta da k'awar dake bibiyar mijinta,wannan wacce irin rayuwace?shin taya zata aminta da k'awa haka har ya kaiga bbu abinda batasaniba tsakaninshi da Inteesaar?why is Inteesaar so insane that she couldn't control her ego?meyasa bataza bar ma ranta sirrinta ba?meyasa ta kasance me bude cikinta ga k'awa?batasan cewar ana zaton wuta a makera bane zaa ganta a masaka??,batasan yadda rayuwar nan tazama bane??,kana zaune da mutum tsakani da Allah amma shi yasaka wani kulli cikin ransa.Baze bari abu yatafi out of control ba ze sanar mata da wacece Ziyada da irin mugun nufinta garesu,Sannan baze gajiya ba har se ya raba Ziyada da matar shi inde har yanason ya zauna lafiya kafin su haukata shi,domin yaga Ziyada dak'arfinta take forcing kanta gareshi while Inteesaar se azabar kishi bbu caring,gabanshi ne yafadi  daya tuna azabar kishin Inteesaar,yanzu yasan tabbas ya shaida mata abinda ke faruwa shize kwana aciki,sannan idan yabarta Ziyada ka iya blackmailing dinshi awurin Inteesaar din idan har be biya mata mummunan bukatarta ba na soyyayh da ita a matsayinta na aminiyar matarshi,shi yana zaman zamanshi Inteesaar tajawo masa masifa.Zama yyi kan daya daga cikin couches din dasuka mamaye falon yana sauke ajiyar zuciya,wani irin sara kanshi keyi sabida yadda things ke fallen apart arayuwarshi,runtse idanuwanshi yyi ahankali bayan ya jingina da kujerar kamar me yin bacci,takun ta yake gani in slow,yadda take magana da tafiya da sauransu is different from the whole women he has ever set his eye's on,though he watched thousands of movies with zillion numbers of queens and princesses but he has never seen someone as cute as her,ahankali ya soma bude idanuwanshi sabida bayason yachigaba da tunanin kowa cikin ranshi besides so yake yasamu peace of mind,duk da dinbin farin cikin dayake ciki na ziyartar mahaifiyarshi,he can't really wait to see her,tuna yana da tafiya agabanshi yasashi mikewa yabar falon yana tunanin me suka tsaya cewa haka da Inteesaar bata shigo gidan ba har yanzu?daga kafada yyi in I don't care attitude sannan yafada bathroom domin yin wanka da sauransu.Tabangaren su Inteesaar kuwa kallon mamaki Ziyada ta bita dashi kafin daga bisani tace"what's wrong with your husband?"...shiru Inteesar tayi tareda kafe Ziyada da idanuwa,"inteesar meke damun mijinki ne?".har yanzu kallon Ziyadar takeyi batareda tace komai ba amma kasan zuciyarta yyi mata dadi na share Ziyada da Elmoudan yyi,ahankali ta furta"may be bai jiki bane".."did you heard just what you said?".zaro idanuwa Inteesar tayi sannan tace"no vex,zan mishi magana"..."gaskiya gwara ki masa domin wannan ba dabi'a ce"..."rufe min bakinki awurin,mijin nawa ne mara dabi'a?"..."yi haquri kinsan idan naji haushi nakan fadi maganganu marasa fasali ".."bbu komai"kawai Inteesar takuma cewa,Ziyada ce ta nisa tace"nikam wai yaushe zaku shirya ne da mijinki?".."ranar daya bani haquri yagane mistakes dinshi".."wllhi ke kam bakida hankali,lefin uban me ya miki?".."yar iska dan ba ke bace,besides ko ni ce da lefi ay shiya kamata yabani haquri."..."says who?".."says my mother"..."sorry to say that your mother isn't helping matters,nide zan miki abu guda daya amatsayin temako kila hakan ka iya ku shirya"..."fada min ina jinki ".."zan rinqa dafo miki abinci da safe da yamma,wannan shine temakon dama".da murmushi Inteesar tace"are you kidding me?".."no I am serious"daka tsalle Inteesaar tayi tana ta faman murna kamar wadda akama albishir dawani babban abu,"me zanyi in biyaki dashi yake aminiyata?"tafadi hawaye nafita daga idanuwanta,"your love and trust "jinjina kai Inteesar tayi irin I Grant you dinnan sannan suka rabu kamar su dawwama ahaka,seda Ziyada tabar gidan sannan Inteesar takoma ciki alokacin takejin haushin Elmoudan na share Ziyada da yyi.yana fitowa daga toilet tashiga dakinshi,shigowarta besa ya koda daga idanuwansa ba,ahankali ta taka har gabansa takafeshi da idanuwa,Kallo daya yamata ya watsar yasoma tafiya gaban mirror dinshi yana goge kanshi da dan karamin towel,be ankara ba yajita ta rungumesa ta baya tana sauke ajiyar zuciya dawata shesheka alamar kuka,ji yyi wani iri daga farko domin koba komai yasan ya gara ta,Allah de yasa tashiryu kada akoma gidan jiya,saka hannuwanshi yyi yadawo da ita ta gabanshi yasoma cupping face dinta cikin siririyar muryashi yace"cry no more"cikeda nutsuwa yyi maganar,girgiza kai tayi tachigaba da zubarda hawaye,tsayawa yyi yana kallonta batareda yace komai ba domin he has nothing to say for now.share mata hawayen yashiga yi ahankali sannan ya zaunar da ita agefen gadonshi ya chigaba da shafe shafenshi,bai kuma ankara ba yakumaji ta rungumeshi ta baya tana sauke ajiyar zuciya domin alokacin tabar kukan,numfashi ya sauke yajuyo da ita suna facing juna "what's wrong with you?"yace dakyar domin miskilancin nashi ya tashi."Ahmed I am tired of this ignoring ".ahankali tayi maganar shikuma har ze bude baki yyi magana yaji ta tokare shi awuya dole ya sakar mata murmushi kawai,"nikam rashin maganar nan taka se inga kamar baka haqura bane".."dama kin bani haquri?"yace yana kallon kwayar idanuwanta,"toh kayi haquri"..kallonta yakumayi sannan yace"it's alright "kawai yachigaba da harkar gabansa,"your food is ready"abinda be taba jiba kenan tun farkon aurensu "my food is ready "yakuma maimaitawa cikin rudani,Dakewa yyi yace"bayan nayi takeaway?.".."kar kace bazaka ciba pls"..kallonta yakeyi cikeda mamaki sannan zuciyarsa takasa gasgata inteesar din  Tabbas there's something behind this her sudden repentance, girgiza kai yyi yace''ok wait for me"yachigaba DA sabgar gabansa domin be yarda DA ziyada ba sannan shi bema yarda DA abincin DA inteesar take ikirarin ta girka masa ba. Cikin wata coffee din doguwar rigar jallabiya yasaka wacce ta dada fito DA tsantsar kyawunsa. Perfumes Ya feshe ilahirin jikinshi dashi kafin daga bisani yakalli inteesar yace"zanje masjid"be jira amsarta ba yafice daga gidan yana mamakinta.Jidderh nashiga gida ta tarar dasu Aneesah basu dawo daga school ba which means sunada lectures din 6,dakin mami tashiga nan ma bata tarar DA ita ba, Afalo ta zauna ta zabga tagumi tareda tsunduma kogin tunani, Me Ya Ahmed ke nufi DA abinda yake yi? Miye manufarsa? Kasa amsa tambayar tayi sabida rurin DA Nokia phone dinta keyi, ganin me kiran yasata picking tareda karawa akan kunnenta. "Ina kofar gidanku"yace kawai sannan Ya kashe wayar. Mikewa tayi tafita dayake akwai Hijab ajikinta, bayan sun gaisa ne Ya miko mata P&Q din data aikeshi yasiyo mata a kasuwa, hatta juya zata shige gida taji muryar DA ko amafarki bazata manta ba, ahankali Ya furta"Hawwa'u tsaya"sannan Ya maida dubansa ha Rabi'u yace"waye kai? ". "Ina yini? "Rabi'u yace sannan yachigaba DA fadin"sunana Rabi'u ". "Miye hadinka DA ita? ". DA mamaki suke kallon elmoudan, Amma ganin ba wasa yake dasu ba yasa Rabi'u cewa"ga gidanmu can, mahaifiyata kawar mahaifiyarta ce, ganin daka min anan bakomai Ya kawoni ba fa ce sako Dana bata ".. Numfashi Elmoudan yasauke ahankali kafin yace"wani sako? ".. "P&Q na siyo mata a Igbo road "yana gama fadin haka yabar wajen sabida bakaramin bata mai rai elmoudan yyi ba, itama fuu tajuya zata shiga gida taji Ya ambaci sunanta cikin sigar DA bawanda yataba kiranta dashi, ahankali tajuyo tana facing dinshi, shikuma cikin dakewar zuciya yace"Hawwa'u ki daure kiyi karatu mai zurfi kinji ko? ". Ahankali tace"toh"... Kafeta DA idanuwa yyi yana ta faman kallonta which she feels uncomfortable, suna cikin wannan yanayin segasu Aneesah sun dawo daga school, gaban Jidderh ne yyi mugun faduwa sbd tsananin fargaba, ahankali suka gaisheshi cikin muryarsu mai sanyi sannan suka shiga gida fuskarsu dauke DA mamaki, jidderh ce tace dashi "se anjima"ganin bashida niyyar cewa ta tafi, girgiza mata kai yyi Itakuma tafada gida DA sauri, yakai ten minutes tsaye akofar gidan kafin daga bisani Ya shige nashi gidan. Afalo Jidderh ta tarar dasu Aneesah, cikin dakewar zuciya tamusu sannu DA zuwa, Sumy ce tafara cewa"Miye hadinki DA Elmoudan? Sannan me Ya tsayar daku tare akofar gida? ". Cikin muryarta mai sanyi tasoma fadin"Rabi'u ne yace infita in karbi p&q din dana aikeshi yasiyomin Shine fah Elmoudan Ya tsayar dani muka gaisa"... Direct sisters dinta sukace"bamu yarda ba"for the first time dasuka taba karyata ta, ahankali ta sauke ajiyar zuciya tace"shikenan, idan baku yarda ba kwa iya tambayar Rabi'u domin tafiyarshi kenan kuka dawo"... "Malama bawani Rabi'u dazamu tambaya, abinda nake son fada miki shine watch your moves wllhi, bbu ruwanki DA mijin Inteesar daga haka bazan Kuma cemiki komai ba domin kinsan sauran"acewar Jasmine sannan suka mike suka bar falon, Mamakin sune Ya cikata takasa gasgasta cewar su kansu sister's dinta zargin dasuke mata kenan inaga en waje? Dole ta dakatar DA duk wata hulda dake hadata DA Elmoudan domin ba inda ze kaita ze tashar dana sani, motar shima tadena shiga sannan koya kirata tadena amsawa bare har wasu suyi tunanin akwai wani Abu a tsakaninsu.Tabangaren Elmoudan kuwa yana shiga gida Ya zauna afalon Kasa yana tunanin irin kallon DA sisters din Jidderh sukayi masa, kwata kwata kallon be kwanta mishi ba, yana cikin wannan yanayin yaji Inteesar ta rungumesa ta baya, "kadawo kenan"tace masa, "ehh "yace Itakuma tajashi har zuwa dinning area ta zaunar, ba ason ranshi yaci abincin data zuba masa ba sedan hankali Ya kwanta. Bedroom straight suka wuce bayan yagama cin abincin, trolley dinshi Ya jawo yazuba kaya set 4,"DA mamaki Inteesar tace dashi "tafiya zakayi? ".. "Ehh zani Kaduna, ko zaki jene? ".. "Ehh zani".. "Then zuba kayanki". DA mamaki yake kallon ta cewar zata bishi Kaduna Kuma tasan sarai inda zasuje, itama bakaramin dakewa tayi ba tace zataje din.Shigowar Alhaji Suleiman gidan kenan Wanda yyi dede DA shigowar Mamin, be daga ido Ya kalleta ba itama kanta asama tawuce shi a tsakar gidan, girgiza kanshi yyi irin zaki Sani dinnan sannan yawuce masjid domin lokacin isha ake kira, Afalo ta tarar DA su Jidderh dake tsumayen jiranta, zama tayi alamar ta gaji sosai sannan tace"wata mata ce tayi siyyayar ban mamaki yau a shago shine abinda Ya tsayar dani"DA murmushi suka ce Allah karo kasuwa, basu rufe baki ba sukaji Sallamar Inteesar cikin falon, shigowa tayi ta zauna tafara gaida mami sannan ta amsa gaisuwar Sumy kawai tareda Dage kai, "mami dama tafiya zamuyi shine nazo inmiki sallama"cewar Inteesar, "ayyerh Allah Ya kiyayae hanya ".. "Amin"tachigaba DA fadin"ran Monday inshaallah zamu dawo"... "Allah dawo daku lafiya"cewar mami, yar hira suka Dan taba sannan Inteesar ta koma gida, fitarta keda wuya abbansu jidderh yashigo  falon yana masifar dadewar mami a shago, "wallahi duk sanda kika Kara kaiwa wannan lokacin kindena zuwa shagon, shashasha kawai mara kamin kai"yachigaba DA fadin"Jidderh Ina abincin ne? ". DA kallo. Mami tabishi batareda tace komai ba ta mike ta shige bedroom dinta. Washegari karfe 7 su Elmoudan suka Kama hanyar kaduna sede mu musu fatan Allah Ya tsare yakuma kiyaye.

LABARIN JIDDERH Where stories live. Discover now