page 48

866 49 0
                                    


  Tamkar amafarki ashnoor takeji ana kwalla  musu kira abinda ya bata mamaki kenan,bude idanu tayi ahankali jin muryar yayansu ta karad'e gidan,mikewa tai zaune tana gyara daurin dankwalinta,hakan yayi daidai da fitowar baby daga toilet,da mamaki tace da ashnoor "ashnoor lafiya kuwa yaya yake mana wannan kiran?"..girgiza kai ashnoor tai cikeda fargaba tace"waya sani"..ajiyar zuciya baby ta sauke sabida gabadaya tagama firgicewa tace"mu je kafin yazo ya tarar damu anan"
Jiki babu kwari  suka fita zuwa falo inda sukaga elmoudan ya hade girar sama data kasa sannan ya zauna yana musu kallo kasa kasa,"ku zauna mana"yafadi ganin sun tsaya cirko cirko agabanshi,saurin mikewa inteesar tayi tasoma fadin"kaga abinda nake fada maka ko?".hannu ya daga mata kana yace"dakata!ban ce kiyi magana ba".wani kallo ashnoor ta wurga ma Inteesaar ganin cewar ita ce sanadiyyar wannan kiran da yayansu yayi musu.zama sukayi kansu na kallon kasa batareda sunce komai ba,daurewa yayi yasoma fadin"baby,ashnoor banason shashanci kunji ko?yakamata kusan cewar iya adadin biyayyar dazakumin shi zakuma inteesar kasancewarta mata ta,ban yarda ku rainata ba sabida yin hakan   tamkar kun wulakanta ni ne,kuma fa aure zakuyi kuma na tabbatar baza kuso k'annen mijinku suyi maku haka ba"yachigaba da fadin"abu na karshe shine ku fuskanceta kubata haquri,"ke kuma inteesar ki yafe musu"ya maida akalar maganar ga inteesar,wani bude hanci tayi tana wani murmushi kasa kasa,zuciyarta na helata cewar tayi aiki me kyau kuma kad'an suka gani.baby ce tace"yi haquri "tafadi agajarce...adakile inteesar ke fadin"kowa yayi nagari kansa"kalmar data batawa Ashnoor rai kenan taki cewa komai,kallon ta elmoudan yyi yace"ashnoor ban isa isaki abu kiyi ba ko?I know quite alright inteesar tayi perceiving abinda yafaru tsakaninku ba daidai ba but I'm still ordering you as your elder brother,apologise to her"furucin yayansu yamata dadi,ahankali tace"yi haquri",kallonta kawai Inteesar keyi cikeda k'iyayya tama kasa amsata,wani kallo ta wurga ma elmoudan cikeda takaicin furucinsa wato nufinshi tayima kannenshi sharri,barin falon tayi tamkar iska zata dauketa sabida sauri yayinda Ashnoor tabi bayanta dawata muguwar harara.Atare suka mik'e zuwa bedroom dinsu kowacce da abinda take sakawa cikin ranta,sede ganin hajiya cikin bedroom din nasu yasasu kallon juna cikeda firgici,tabbas fada hajiya zata kara musu.Zama sukayi  a kasa bayan sunyi sallama,amsawa tayi sannan tace"ban hanaku zubewa agabana ba tamkar wasu masu roqon gafara, c'mon ku zauna kan gadon"tafada sounding more serious,suna dar dar suka zauna idanuwan baby har sun fara kawo kwalla,arayuwarta bata kaunar abinda ze batawa hajiya rai haka ashnoor ita ma gabadaya yanayinta ya canja.ahankali hajiya tasoma fadin"banyi zaton zaku zama masu raina nagaba dasu ba,akullum ina nuna muku illar yin hakan,meyasa kuka zagi Inteesar?ko ba don kasancewarta matar yayanku ba a'a kasancewarta ta gaba daku,karkusa zuciyata tafara zargin kode aikin banza na zauna ina yin shekara da shekaru wurin tabbatar da kun samu cikakkiyar tarbiyya?meyasa zaku watsa min kasa a ido?"..banda sharar kwalla ba abinda Baby ke yi yayinda jikin Ashnoor yayi mugun sanyi,murya na rawa ashnoor ke cewa"wllh hajiya bamu zageta ba"nan ashnoor ta kwashe komai tafada ma hajiya,tabbas bayanan ashnoor sun gamsar da hajiya,ajiyar zuciya ta sauke ahankali tana kuma tausayawa rayuwar d'anta,sha 're tunanin tayi da fadin"kunga de banason abinda ze ja mana matsala,tunda abin yazama haka  ku shirya zuwa gidan kawu mallam kawai,nafasa kanon"cikeda murna suka amsata da toh,fita tayi daga bedroom dinsu zuwa nata inda ta tarar da elmoudan zaune yana duba wani magazine,shigowarta yasashi fadin"hajiya ina kikaje?".."dakinsu baby"ta amsa shi agajarce sannan tachigaba da fadin"elmoudan na canza shawara,gidan kawu Mallam su Ashnoor zasu je kamin in dawo daga tafiyar,waro ido elmoudan yayi yana tunanin kila hajiya taji haushin sharrin da inteesar tayi musu dazu shiyasa ta hanasu binsu,"meyasa??"ya daure ya tambayeta,"sabida banason matsala?".."wacce matsala kike gudu na zamansu agidana?".."kafini sani elmoudan"tabashi answer straight forward,numfashi ya sauke kana yace"haba Hajiya!yanxu akan abinda yafaru ne yasa kika canza ra'ayi?"..ya tambaya yana narai narai da idanu,"ehh elmoudan,bazan dena ce mata ehh ba har seka dena min tambayoyi"tana kaiwa nan ta shiga toilet ta barshi nan jugum yanata faman tunani.Fitowarta daga toilet ya dawo dashi daga duniyar tunanin daya tafi,in a pleading manner yarinqa ba hajiya baki da haquri harta amince sutafi kanon akaro na biyu.da murnarshi ya wuce site dinsu inda ya tarar da inteesar nata sheka bacci  abinda ya hana fada mata dasu ashnoor zasu koma kano kenan...dafe kirji Aneesah tayi tasoma fadin"subhanallah meke damunki?"agigice tayi ma Jidderh tambayar,ganin batada shirin cewa komai yasa ta koma ta shaidama su Mami,da gudu Mami ta shiga dakin tana tana me zubewa akasa ta rungumo Jidderh tana fadin"meya faru kike kuka?ko bakyason Ahmed din ne?"girgiza kai ta shigayi ahankali,dakyar tafurta"a'a kawai de ina kukan wata rana fa rabuwa zamuyi ko?".kwantar mata da hankali suka yi sannan ta tabbatar musu da ta amince da Ahmed waziri,arashin uwa akanyi uwar daki shiyasa ta amince da Ahmed din tana gudun kada tayi saki  na dafe domin opportunity yana zuwa once in a lifetime.
Washegari da misalin karfe sha daya suka baro kaduna,tamkar am wa inteesar mutuwa haka ta yi jugum jugum,fahimtar hakan yasa su Ashnoor kame bakinsu daga yin surutu kowani shirme daka iya zame musu matsala.karfe uku daidai suka shigo kano su Ashnoor se kalle kalle sukeyi tamkar yau ce rana tafarko dasuka taba zuwa,Bunas kitchen direct yawuce yayi musu  takeaway sannan suka yi hanyar gida.Kallon Ziyada mamansu keyi cikeda mamakin ganin yadda ta rame sannan tayi baki cikin dan lokaci kalilan,"damuwar me kika jefa kanki aciki?wani mummunan abu kike shirin aikatama kanki?,Ziyada me kikeso kizama?"ajere tayi mata tambayoyin yayinda hawaye suka soma ambaliya akan fuskar Ziyada,majina taja sannan tasoma fadin "Wannan tambayoyin nada nasaba da inteesaar,wllhi ta sanadinta nashiga wannan halin"takarashe maganar tana me rushewa da kuka.gumi ne ya wanke fuskar maman Ziyada,cikeda son jin karin bayani ta kafe Ziyada da ido batareda tace komai ba,ajiyar zuciyar Ziyada tayi sannan tachigaba da cewa "mama nasan na cuci inteesar sannan na zalinceta,amatsayina na aminiyarta be dace nayi yunkurin cin amanarta ba,amma yaya zanyi bayan rayuwata na gurin wanda take tare dashi,yaya zanyi aduk lokacin da ciwon sosnshi ya taso min?ina jin tamkar wacce bazata rayu ba aduk lokacin da kibiyar sonshi ta cake ni,mama ki fada min taya zan chigaba da kawance da inteesar?tayaya zan chigaba da sauraron dukkan sirrukanta amatsayina na me kaunar mijinta...."."yi min shiru!"maman Ziyada ta dakatar da ita cikeda fada,yayinda tsantsar mamakin diyarta na samu wurin zama azuciyarta,hakika bata taba zaton ziyada can be so stupid kamar haka ba,tayaya zata bari hakan ta faru in the first place."kinci amanar kawancenku,kinci amanar aminiyarki sannan kin bani kunyah,Ziyada how can you even think of doing that?".cikeda wani irin gigitaccen kuka Ziyada ke fadin"mama sanadiyyar haka ya sa nabar kano gabadaya,sanadiyyar haka yasa na dena amfani da tsohon simcard dina,mama wllhi bazan zalunci inteesar ba duk da afari ba abinda banyi ba na inga hankalinshi ya karkata gareni amma abin yaci tura,don dole na haqura nayi moving on amma tunaninsa qaruwa yayi maimakon yaragu cikin raina..."wawan Marin da mamanta ta sharara mata ne ya dakatar da ita babu shiri,dafe kuncinta tayi tana ta faman rafka uban kuka tamkar wacce uwarta ta mutu,sosai tausayin diyarta ya shigeta amma bazata huta ba harse taga Ziyada ta fita daga rayuwar inteesar fita ta har abada sannan bazata gushe ba wurin ganin babu wata alaqa dazata kara hadasu.wayarta ta dauka tai dialling numbern inteesar wadda ke kwance afalo tana kallo yayinda su Ashnoor ke  yan share share,elmoudan kuma na zaune tamkar yana danna waya nan ko hankalin shi naga tunanin Jidderh,cikeda farin ciki tayi picking wayar sede jin yadda maman Ziyada ke magana yasata tayi saurin miqewa zaune,"daga yau banason ki kara kirana gameda Ziyada,sannan na kunce duk wasu ties dake tsakaninku da ita,banyarda ki nuna kinsanta ba koda ahanya,sannan kada kiyi yunkurin tamabaya ta dalili domin umarni nake baki amatsayina na wadda ta haifeki,kawancenku baze yiwu ba da wannan nake miki saduwar alheri"tana kaiwa nan takashe wayarta tabar inteesar a k'ame takasa koda motsi,tafi karfin minti goma zaune awurin batareda elmoudan yyi noticing halin datake ciki ba,numfashi ta sauke da karfi tuno takaddamar datayi akan Ziyada da Elmoudan,tabbas ba wani bane ya rabata da Ziyada fa ce elmoudan,cikeda wani kullutun bakin ciki daya tokare mata wuya ta mike tanufi inda yake sede kafin tafara magana yayi picking call din Yusrah secretary dinshi,"hello yusrah,hope komai yana tafiya daidai?ehh nadawo,gobe inshallah zanzo"..ta dayan bangaren yusrah tasoma fadin"kayi haquri sir amma yazama dole in fada maka,hakika bazan so in zama me shiga tsakanin miji da mata   ba but I have to tell you this,jiya da safe matarka ta kirani tayi min zagin da ba'a taba min ba hardasu threatening dina,Hakika Allah abin tsorone amma gaskiya matarka ma abar tsoro ce,banason fitina arayuwata kuma wallahi ashirye nake in ajiye aikina kamar yadda ta bukata if care is not taken"kallon inteesar yakeyi cikeda bakin ciki da fushi,mikewa yayi yay closing gaf din dake tsakaninta dashi tareda cafko gashin kanta yana muzurai,ihun datasaki yasa su Ashnoor fitowa falon babu shiri.

*

LABARIN JIDDERH Where stories live. Discover now