page 10

1.1K 69 0
                                    


                Da matsanancin ciwon kai jidderh ta tashi dubaga kusan kwana datayi azaune, sannan ga damuwar tafiyar DA elmoudan yyi,kwata kwata ranta bbu dadi, har mamakin kanta tayi saboda ta Gaza fahimtar yadda takeji acikin ranta, ganin bbu sarki se Allah yasa ta mike tafita falo inda ta tarar da su Mami na breakfast, har kasa ta tsugunna tagaida mamin sannan tagaida su Sumy, harta mike Mami tace da ita"zauna inasonyin magana dake"yadda mamin tayi maganar yasa hantar cikinta kadawa, gabanta Ya fadi gawani gumi dasuke yar tsere  akan fuskarta, numfashi mai nauyi ta sauke sannan takalli sashen dasu Sumy suke, kallon dasuke mata Ya tabbatar mata cewar sune suka fadawa mami wani Abu.Dakallo kawai take binsu mai cikeda mamaki, mami ce tasoma fadin"banason rashin kamin kai gamida rashin hankali. Kinji Nik0? "Da mamaki take kallon mamin wadda tachigaba da fadin "baze yiwu ki lalata zumuncin dake tsakanina da inteesar ba,baze yiwu ahada baki dani acuci inteesar ba, sannan bazan goyi bayan aci amanarta ba". Shiru mamin tayi tana kuma kallon jidderh da kanta ke sauke kasa tana fidda numfashi kasa kasa, "Ba se na maimaita miki yadda inteesar tadaukeni amatsayin uwa ba, ba se nafada miki irin girmama ni da mutuntani datake yiba domin agaban idanki take gudanar dasu, da ace kinada hankali da tun farko kin haramtawa kanki mijinta, dubaga yadda take hidimtawa gidan nan gabadaya bawai ni kadai ba, wallahil azim bazan bari son zuciyarki ya  rabani da ita ba domin ba kece kika hadamu ba.Ina gargadinki da babbar murya, kifita harkar mijinta. "Se anan Mami tayi shiru tachigaba da karya warta, harda Jidderh ta bar wajen sekuma tafasa ta kuma zama tana fadin"Mami meya kawo waennan maganganun? Sannan Ina tabbatar miki da koma waye yafada miki wallahi ba gaskiya bane, narantse bbu komai tsakanina da Elmoudan se gaisuwa da mutunta juna. "Tana gama fadin haka ta mike takoma bedroom dinsu kanta nawani sara mata, kwanciya tayi ruf da ciki tana sauke numfashi, can kuma hawaye suka soma zarya akan fuskarta wanda tagaza tsaidasu, barinsu tayi su zuba KO hakan ka iya sa su rage radadin cikin zuciyarta, a en watanninnan bata san meke damun rayuwarta ba, tabbas tasan tana cikin damuwa amma KO yanka ta zaayi bazata iya fadin ga takamaimai abinda ke damunta ba.runtse idanuwanta tayi masu zubar da hawaye,yanda yake magana dayanda yake tafiya ne ke dawo mata in slow, da murmushinsa me sa zuciya abinda batayi ba,da yanda yake furta sunanta kadai Ya ishi ya tabbatar da shidin na daban ne, shi din halinshi mai wuyar ganewa ne sannan baka iya figuring out idan yana son abu KO baya sonsa, murmushi tayi data tuno sa duk da zuciyarta nacikin tsananin rudani, yaushe zuciyarta Zata  samu nutsuwa da wanda take muradi? Babu wannan rana Jidderh, zuciyarta ta amsa ta, nan da nan hawaye suka wanke mata fuska,hoton Fuskarshi kawai take kallo acikin zuciyarta tana ayyana irin begensa datakeyi da yadda akayi sonshi yayi mata wannan kamin karen mahaukaciyar, taya akayi tafada tarkonshi? Taya akayi tafada kogin sonshi? Taya akayi ta tsunduma kanta cikin mayen son mutumin da be san tanayi ba?tabbas son maso wani koshin wahala  ne wanda ba inda ze sauketa se tashar wulakanci, wani irin matsananin kukane ya kufce mata, ahankali take rera sautin kukan me tsuma zuciyar duk wani me sauraro, ta dade tana kukan kafin daga bisani ta share hawayenta tana sauke ajiyar zuciya, wani irin balain son ganinshi zuciyarta keyi, dason jin kalaminsa, ahankali takai hannunta kan zuciyarta dake bugawa da sauri da sauri wai ko hakan ka iya sa ta danji sanyi cikin ranta.Tabbas so bemata adalci ba, sannan be kyauta mata ba, taya zaayi zuciyarta taso elmoudan? Bayan an haramta mata ita? Taya zaayi zuciyarta ta aminta da Elmoudan ze sota in return? Kasancewar ta baka mara kyau? Kasancewar ta karamar yarinya shikuma amatsayinshi  na hadadden mutum me takama da kudi gawani kwarjini da kamala ta daban, ko ba a fada mata ba tasan cewar yafi karfinta kawai shishigi ne irin na zuciyarta, inba haka ba miye na kaunar mutumin daya wuce da ajinta? Hawaye suka kuma zubowa suna bin kuncinta domin tasan wahalar banza takeyi Elmoudan baze taba kaunarta ba.Hakika tana cikin gararin so wanda ba abinda yakamata tayi daya wuce addua, jiki babu kwari ta mike ta dauro alwala ta sallaci sallar duha, duk yadda tadanne zuciyarta akan Elmoudan kasawa tayi har seda ta mike ta leka gidanshi ta window kodan zuciyarta ta rage zugin datake mata. Tabangaren su Elmoudan kuwa suna tafiya suna hira jefi jefi, juyawar dazeyi yaga inteesar tayi bacci, murmushi yyi yachigaba da driving dinshi Tunanin yarinyar yasomayi, yana tuna yadda take tafiya da yadsa  take furta kalamanta a natse batareda hayaniya ba, uwa uba sihirtaccen kyanta gamida kyawawan dabiun ta daba kowacce mace kedashi ba, sauke ajiyar zuciya yyi yana tunanin ta inda ze bullowa wannan lamarin domin son Jidderh da numfashinsa yake tafiya, kamanta alqawarin dakama inteesar? Ya tambayi kanshi da kanshi sede kafin ya ba kanshi amsa yaji wayarshi na ruri, picking yyi sannan yyi slowing down agefen titi, "hello"yace sbd number ce takirasa, "dafatan katashi lfy ya abin alfaharina"da mamaki yake sauraron wannan shirmen acewarshi, "kanaji na? Tachigaba da fadin nasan zakayi mamakin kiran dana maka bayan kana tare da aminiyata " jin ta ambaci aminiya yasashi kashe wayar sannan yyi blocking numbern yanata faman buga tsaki, har suka isa kaduna Inteesar bata farka ba seda zasu shiga gidan su Elmoudan dake malali,.Da murmushi yadubeta yace "sannu dafarkawa, kuma kin farka adede "murmushi ta mayar masa alokacin yyi parking, be karasa kashe injin motarshi ba yaga sisternshi Ashnoor da Cousin dinshi Baby sunzo da saurin su, yana fita suka rungumeshi atare suna masa sannu da zuwa, be kula suba sabida fushin dayakeyi dasu narashin zuwa gidanshi dabasayi amatsayinshi na yayansu, butt suka bude zuka zara trolley din sukayi ciki dashi batareda sun kalli sashen da inteesar take ba dubaga hade ran datayi, Elmoudan dalura dakowanne acikinsu amma bece komai shima yashiga ciki dasauri, afalo yaga Hajiya na zaune fuskarta dauke da murmushi, shima murmushin ya sakar mata sannan yakarisa inda take ya rungume tareda kwanciya akanta sekace wani karamin yaro. Batareda damuwa ba tace"haba babana kada ka karyani mana bakasan ka girma bane? Tachigaba dacewa"koda yake yi zamanka tunda babu magaji a yanzu "murmushi gabadaya sukayi banda inteesar data rakube agefe, dakyar ta iya ce da Hajiya"Ina yini yagida? "Lafiya kawai hajiya tace cikeda fara arta, wani mugun kallo ya watsa ma Ashnoor da baby amma sukayi biris dashi kamar basu ganshi ba, "yaran nan bakuda kunyah ko? Baku iya gaisuwa ba right? "Se asannan suka gaisheshi sannan suka hada da inteesar. "Hajiya fushi nake da Ashnoor da Baby".. "Subhanallah mesuka yi? "... "Basu taba kawomin ziyara ba sannan basa kirana awaya, zan iya sanin dalili? ".. Murmushi hajiya tayi tace"basuda wasu dalili kuwa ".. "Kai hajiya inji wa? "Suka fada atare suna zumburo baki, "inji ni"tace tana nuna kanta, girgiza kai Elmoudan yyi tareda yin kwafa yace"nasaka ku a blacklist wllhi sena sassaba muku?mara kunyah ban isa ku kawo min ruwa bako? ". Suna dariya suke fadin "bayan wanda ke gabanka "shima dariyar yyi domin besan da kayan ciye ciye agabansa ba, "ku kai trolley din site dinshi mana "cewar hajiya, ba musu suka nufi site din Elmoudan da akwatin. Suna fita hajiya takalli inteesar tace "yaya mutan gidan? Hope su mamanku na lafiya". Amaimakon tavata amsa seta mata murmushi kawai batareda tace komai ba, akufule Elmoudan ya mike zaune yace"bakiji hajiya na magana bane? "Shima shiru tamasa, kallon hajiyar yyi cikeda kunyah itakuma ta dauke kanta gefe, mikewa tayi tafita daga falon nata tana fadin "kuci abincin ku huta kunji ko? "Elmoudan ne kawai ya amsa da toh banda inteesar dakamar ruwa ya cinyeta, cikeda tsananin fada yajuyo yana dubanta"wato hajiya kike ma banza  sabida bakida mutunci ko? Ahaka kikeson auren mu ya dore? Toh wallahi kinyi kadan ki raina min mahaifiya dan haka kafin nabude idona narufe kinbar wurin nan domin ba hajiya haquri, idan kuma ba haka ba wallahi ba abinda ze hana inmiki abinda zaki dauki tsahon shekaru kina mamaki.

LABARIN JIDDERH Where stories live. Discover now