page 59

1.2K 64 6
                                    


  "Jidderh pls answer me"ya fada tamkar zaiyi kuka,dagowa tayi tazuba jajayen idanunta cikin nashi sannan tace"na'am"..ajiyar zuciya ya sauke yana kallon yadda yanayinta ya canza alokaci d'aya,bai ankara ba yaga hawaye na zubowa daga idanuwanta abinda yabashi matukar mamaki kenan,arikice yake fadin"meya faru?me na miki?..kasa furta masa koma tayi sema kokarin cusa kanta datayi cikin gwiwowinta..saurin riko ta yayi ya rungume yana jin wani irin abu na shigarsa,hakika bazai fasalta yadda ruhinshi Yake ba a wannan lokaci,zubar hawayenta tamkar zubar garwashi ne acikin zuciyarshi,runtse idanu yayi yana bubbuga bayanta ahankali alamar rarrashi,samun kanta tayi da yin shiru banda ajiyar zuciyar datake saukewa,hab'arta yariqe yana kallon yadda tasoma bata kwalliyarta da kuka,murya can kasa yace"kinga zaki bata kwalliyarki tun kafin ince kinyi kyau ko?"dan turo baki tayi tace "tun dazu bakace nayi ba sai yanzu?na yafe",hakan yasanyashi sakin wani malalacin murmushi,har cikin zuciyarshi yake jin dadin yadda take sakewa dashi,yace"kiyi haquri amma  natabbatar miki kinfi  matan wurin nan yin kyau"ta dago idanta da sauri kana ta zubesu cikin nashi cikin mamaki dakuma kunyar furucinsa,samun kanta tayi dacewa"ba wani nan,kawai dai kana fad'i ne"yace"dagaske nakeyi "..tace"toh karantse"d'an waro ido yayi yace"yanzu akan wannan maganar ma sainayi rantsuwa?"had'e rai tayi gamida cuno baki tana kokarin fita daga motar yayi saurin riqeta gam yana sakin wani kayataccen murmushi na musamman wanda yafidda tsantsar kyawunsa,juyowa tayi dasauri ta kai dubanta gareshi,kasa dauke idanunta tayi akanshi sabida wani masifaffen kyau dataga yakara mata,yana kallon cikin idanunta yace"Wallahi kinfi dukkan matan dake wurin nan kyau,ki yarda dani "..yadda yayi maganar yasata jin kunyah,kawar da fuskarta tayi daga gareshi batareda tace komai ba,yana murmushi yace"juyo mana"shiru tamasa yayinda zuciyarta ke tsananin harbawa,yakuma cewa"juyo mana!"nan ma shiru tamasa sai dai blushing datakeyi,bata taba tsammanin hakan zaya shiga tsakaninsu ba,yakuma fadin"kada kiyi min wannan horon pls"yadda yayi maganar tamkar zayayi kuka,saurin juyowa tayi da mamakin furucin shi,zuwa yanzu takasa gane yadda relationship dinsu ke rikidewa yana komawa wani abu na daban wanda yasha bambam da na baya,iskar bakinshi yayi amfani da ita wurin hure mata lashes dinta hakan yasanyata  yin farrrrrrrrr da ido sannan ta lumshe tana mai sunkuyar da kanta k'asa,murmushi yayi kana yace"inason kifada min gaskiyar abinda ke ranki Jidderh,kada kiyi kwauron baki kinji?"gyad'a masa kai tayi ahankali sannan yace" ina ganin tamkar bayan ahwaz akwai wani cikin rayuwarki Jidderh!"gabanta ne yayi mummunan faduwa,ta waro ido tana kallonshi tama kasa furta komai,ya Allah! karde yagane ina sonshi ne?wata azababbiyar kunyah ce ta lullubeta tama kasa bashi amsa har lokacin,kokarin saka idanunshi cikin nata yakeyi kafin yakuma mata tambayar,ganin ta sunkuyar da kanta kasa yasa yayi murmushi gamida cewa"Inteesaar!"hantar cikinta ce tayi mugun kadawa,arikice ta dago da fuskarta ta saka idanunta cikin nashi cikeda fargaba tace"na shiga uku!"yace"kin shiga uku ko mun shiga uku?!yayi kokarin Dakewa tamkar da gaske,bata ankara ba taji yace"kibani amsar tambayata"wani kallo tamishi tace"baka bukatar amsar tambayarka awannan lokacin,pls kasan yadda zakayi,she might think muna cheating dinta abayan idon tane"yadda take maganar yabashi dariya matuka amma yadake gamida cewa"not until se kin  bani amsar tambayata "..kallonshi takumayi da sauri sannan tace"ahwaz nakeso!shi kaidai zuciyata take kauna kuma take muradin aure..."saurin katseta yayi dacewa"ya isheni haka"yana mai runtse idanu,tamkar shigar adda yaji maganar tata,shi yau yaga ta kanshi,wata zuciyar tace to kai meyasa bazaka bayyana mata sirrin dake ranka ba?,meyasa bazaka fada mata irin illar da sonta yamaka ba?,meyasa bazaka shaidamata irin yadda sonta ya fatattaka zuciyarka da abinda ta kunsa ba?meyasa bazaka nuna mata irin matsananciyar soyayyarka gareta ba wacce ta dade danqare azuciyarka tahanaka sukuni?shin wai har sai yaushe zaka tashi daga wannan mafarkin naka dabai da amfani wanda bazai fisshe kaba?miye aciki dan kace  kana sonta?miye aciki dan kayi takara da abokinka wurin bayyana kaunarku ga mace d'aya?shin haramun ne aikata hakan ko kuma yasaba ma al'ada?meyasa kake son cigaba da wahalar da kanka akan yarinyar dabazata taba qinka ba,tabbas ko ranar aurenta da ahwaz kace kana sonta tana iya saka almakashi ta datse batun ahwaz ta aureka,toh meyake hanaka sanar da ita?.ganin ya zurfa cikin tunani yasa tace"yaya !kama manta inteesar na kusa ko?"..adan firgice yace"inteesar kuma ah ina?"yadda yayi maganar ya tabbatar mata da wasa yakeyi akaron farko,turo baki tayi gamida fizge hannunta tace"kaiko?"kafin yayi magana MC yasoma kiran Hauwa Jidderh Suleiman domin bada thanksgiving,hakan yasanyasu fitowa daga cikin motar jiki babu kwari,bai damu ba ya riko mata hannu har suka shiga hall din lamarin daya tunzura Inteesar da ahwaz kenan,tun shigowarsu masu hotuna ke daukarsu pictures dan duk atunaninsu couples ne.Itade suman tsaye kawai tayi domin ta tabbatar inteesar tagansu ayanayin dasuke,wata zuciyar tace ga ahwaz ma,nan take gabanta ya fadi,saurin zare hannunta tayi daga nashi wanda hakan yayi dai dai da miko mata mic da MC yayi,kallon mutanen dake wurin tayi taji wata kunyah ta kamata,kasa cewa komai tayi saida elmoudan yace"c'mon Jidderh zaki iya".tace"are you sure?"murmushi yayi ya gyada mata kai,itama murmushin tayi ta sunne kanta kasa sannan tafara magana,"Alhamdulillah da Allah yakawo mu wannan rana mai cikeda tarin albarka da ni'imomi,Ashnoor da Baby are more like a sister's to me,i've been through it all with them in times of laughter and tears,you know honestly I couldn't ask more of friends,May your homes be filled with laughter and your hearts with love,Ladies and gentlemen thanks for coming,may you have a wonderful journey back home."dakyar ta iya bada wannan speech din dubaga yadda take tun asali ita bamai son hayaniya bace ko yin magana abainar jama'a,addua takeyi Allah yasa dai batayi blunder ba.wurin amaren taje aka rinqa musu pics elmoudan ma yaje a chigaba dayi dashi,Dj ne yabada kida duk suka fito stage harda amaren ana rawa,liki Jidderh kawai keyi tana juyi dan Sam ba gwanar rawa bace,hakan datakeyi yakuma birge elmoudan sabida arayuwarshi ya tsani yaga mace na rawa aganinshi rashin kamin kaine,rafar dubu daya ya juye mata akai,da mamaki take kallonsa shikuma banda murmushi da murna ba abinda yakeyi.juyawa tayi tachigaba dama amaren liki yayinda wani saurayi ya shiga tsakaninsu da elmoudan,yan dari biyar biyar yake lika mata batareda tasani ba,elmoudan fah???wai wai wai fasalta yadda yakeji alokacin abu ne mai wuyar fassarawa.ji yakeyi tamkar ya rufe saurayin da duka awurin,kasa haquri yayi ya fita daga stage din,niyyar fita daga hall din yayi gabadaya sai yaga Inteesar ta zurfa cikin tunani da alama taga ya riqe hannun Jidderh ne,bai damu da mutanen dake wurin ba dayake ma daukacin mutanen hankalinsu naga amaren yasashi bata wata wawiyar runguma,tsamtsam ya rungumeta yana sauke ajiyar zuciya,hakan yasanyata fashewa da kuka,yanzu zuciyarta tayi weak sosai,bazata iya masa zancen ba,kukan ta yasanyashi sauri dago da fuskarta yana kallon kwayar idanunta,ahankali yakai lips dinshi kan kuncinta ya licking kayanshi not giving a damn!,bai damu da foundation din dake fuskar ba,wani sanyine yake ratsata murya can kasa tace"I love you"yace"I love you more babe".zama yayi yana fuskantar ta yayinda yaji saukin radadin da zuciyarshi keyi,kallonshi kurum takeyi tamkar yau tafara sashi a idanunta haka shima,murmushi yayi yace"I love sweetheart"tace"I love you darling"d'aga gira daya yayi yace"I can see kin shirya"murmushi kawai tayi .yace"I love you very own"tace"I love you handsome "yace"I love you pretty"tace"I love habibee"yace "I love you habibtee"d'an waro ido tayi tace"ban yarda ba kana kwaikwayana"dariya yayi domin yadda tayi maganar ba karamin burge shi tayi ba .riko hannunta yayi yace"ina sonki inteesar,son dabaze kamantu koya fasaltu ba,ina sonki with every fibre of my being,ina miki son da ban taba ma wata diya mace ba, I love you so very much mummyn lovely unborn dinmu"yafada yana mai dora dayan hannunshi kan mararta,hakika fasalta yadda take farin ciki a wannnan lokaci baya yiwuwa ba,tace"inasonka beyond your expectations,ina sonka ina sonka ina sonka daddyn unborn dinmu"saurin mikar da ita yayi yafita daga hall din domin yana bukatar shutting bakinta da passionate kiss,he's short of words kuma babu abinda yakamata ayi irin kiss a wannan time din da kalamai sukayi karanci.Komai sukeyi akan idanun Jidderh ne,hakika takasa hana kanta zubarda hawaye,hawayene sosai suke zuba daga idanunta tamkar an bude famfo,saurin zama tayi jin kafafunta na rawa alamar bazasu iya daukar taba awannan lokaci,kifa kanta tayi da table ta fashe da kuka,kuka irin wanda ta dade bata yiba cikin tarihin rayuwarta,kuka ne mai tsuma zuciyar mai sauraro,kuka ne na bakin cikin da takaici gamida tsananin kishi,shin yaya zatayi da rayuwarta?ina zata saka kanta taji sanyin,saurin fita daga hall din tayi a akan idon ahwaz,saurin binta yayi sedai koda ya fita bai ganta ba,wani wuri mara haske tasamu ta zauna without minding koda akoi wani mugun abu awurin,tanajin zata iya mutuwa idan batayi wannan kukan ba isasshe,kuka tarinqayi tamkar her life depends on it.Elmoudan kuwa yana cikin motar shi da inteesar yayinda jikinta ke akan nashi.Head dinta ya cire daga kan nata doguwar sumarta mai kamshin gaske ta warwaro kasa,shakar kamshin turaren gashin yakeyi yana kuma jin kaunar inteesar na kafa sabon gurbi acikin zuciyarsa,juyowa tadanyi tace dashi"sweetheart ina jin bacci"yayi murmushi yace"okay go to sleep"yafada yana mai kissing forehead dinta,tace"I mean mutafi gida"yace "your wish is my command,uwargidan ahmed"murmushi tayi amaimakon ta b'acin rai abinda yabashi mamaki kenan,bai san sanda yayi shutting bakinta da wani arnen kiss ba,giving her the kiss of her life,it was short but yet an unforgettable one,yana maida numfashi yace "gaskiya kamata mu koma gida,bari in kira jidderh"murmushi tayi tace "okay karku dade"hannunta yamanna kiss sannan yasa veil yarufe mata gashinta kana yafita ya bude front seat dawowa yayi ya dauketa tamkar baby ya maida ta gaba yayi mata stretching kujerar yadda zata huta. Kallonshi kawai takeyi tana jin wani sanyi aranta.akofar hall din yaga ahwaz na waige waige,ganin elmoudan yasashi hade rai matuka,sarai elmoudan yagane me ahwaz yake nufi amma yayi biris dashi ya ce"ina jidderh"cikeda takaici ahwaz ke fadin"ban san sanda kazama so heartless ba ahmed,baka da imani bakada tausayi,kasan sarai halin da yarinyar nan ke ciki kaine sila amma kasa kafa ka shure komai,Allah bazai barka ba"yana kaiwa nan yanufi inda yayi parking motarshi,yabar elmoudan cikeda mamaki,yakasa gane inda maganar ahwaz din ta nufa,bai gane shine silar shiga halin datake ciki ba?awanne halin take?ganin baida amsar tambayeshi yasa yayi dialling wayarta,tamkar bazata dauka ba tayi picking,yace"kina ina?"agajarce,tace"waje"itama agajarce"yace"waje a ina?"babu bata lokaci ta kwatanta masa,tun kafin ta ajiye wayar ma ya karaso,"mekikeyi awannan wurin?"banza tayi mishi tanajin wani haushinsa,zama yayi akusa da ita tayi saurin mikewa,shima mikewar yayi yana son mata magana tasoma tafiya,baida abinyi banda jawota dayayi,cikeda dukkan karfin da Allah ya mata take kokawar kwace kanta,gam yariqe tayadda bazata iya kwacewa ba,murya can kasa yace"calm down  jidderh"maganarshi bata sa dena ba hakan yasanyashi rungumeta tsam tayadda ko motsi bata iyawa,cikin kuka tace"ka sakeni ni,you're hurting me"yace"bazan sake kiba har se kin fada min me ahwaz yake nufi na nine silar jefaki cikin halin dakike ciki,Jidderh kina sona ne?"jin tambayar tayi tamkar amafarki.takasa gasgata maganar,yakuma cewa"dan Allah kibani amsa"Dakewa tayi tace"inajin yayi misunderstanding din issue dinne"tafada domin over her dead body tafurta ma wani d'a namiji kalmar so as small as she is.Wani irin bak'in ciki ne ya ziyarce shi...sakinta yayi yace"muje"kawai agajarce yanufi mota yayinda take bin bayanshi wata zuciyar na cewa meyasa kika fasa fada masa?shiga bayan motar tayi ta zauna yayinda ya zauna agaba shikuma,yasoma driving inteesar tafarka,da murmushi yace"intee dear kin farka?"tace"sweetheart pounded yam nake craving mawa"ya d'an waro ido yace"no problem dear.zamu tsaya mu siya."murmushi tayi shima ya daure yasakar mata nashi.

Karfe daya da rabi na dare yashigo part din hajiya,jidderh yagani akwance da alamar tayi kuka.babu kowa falon sai ita kadai,zama yayi akusa da ita yana kallon fuskarta,farkawa tayi taga mutum agabanta,saurin tashi tayi tace"yaya lafiya?"..babu kunyah yace"nakasa bacci ne...zuciyata na raya min idan ban ganki ba tofah kwanan zaune zanyi?"da mamaki tace"taya za'ayi zuciyarka ta raya maka hakan?"yace"sabida irin kaunar datake miki.jidderh ina sonki son dabaze rubutu koya fasaltu cikin littafi ba."sakin baki tayi yayinda adaidai lokacin wasu hawayen farin ciki suka soma zubo mata.


LABARIN JIDDERH Where stories live. Discover now