page 62

1.3K 73 18
                                    


     Misalin karfe sha biyu yan daurin aure suka gama watsewa sede har wannan lokacin babu wanda yasan bidirin da akeyi na daura aure da elmoudan,Sallah raka'a biyu duka amaren sukayi agida,sosai sukayi addu'ar zaman lafiya tsakaninsu da angwayensu.Abbansu Jidderh ne ya shigo gidan fuskarshi dauke da annashuwa,fasalta yadda yakeji bata lokacine,bai taba tunanin zai aurar da yaranshi alokaci d'aya ba,dakyar ya kusa cikin gidan yana hagen yadda zaya kira Mami,Anty mariya ce tazo wucewa yakirata,da murmushi take fadin"uban amaren hudu,Allah yasanya alheri".."amin"yace yana murmushi kafin yachigaba da cewa"kira min Fatima".."toh"tace ta nufi cikin gidan,batafi mintuna biyar da shiga gidan ba Mami tafito ta sameshi,cikin dan dakewar fuska yace"ina son magana dake"..tace"bismillah"ya nisa sannan yace"mu shiga falona"babu musu tabi bayanshi sede zuciyarta ta shiga tsananin fargaba,mekuma ya faru?kawai take tambayar kanta harta karasa falon,zama sukayi yasoma fadin"inason kiyi ma alamarin duban tsanaki,ki saka aranki hakan daya faru shine abu mafi alheri,bana son tashin hankali ya faru bayan na fada miki maganar"shiru tayi kurum tana juya maganganunshi akan mizanin hankalinta.kallonta yakumayi sannan yace"Bada ahwaz aka daura ma Jidderh aure ba fa ce da Ahmed mijin Inteesaar mak'ocinmu,ina son fita hakkin kine shiyasa na shaida miki,ita kuma Jidderh bana so koda wasa ta san da wannan zancen sabida wasu dalilai"arud'e gamida firgice Mami tace"innalillahi wa'inna ilaihi raji'un,mijin inteesar dina?"kasa chigaba da maganar tayi sabida wani kullutu daya tokare mata wuya,murya can kasa take fadin"haba abbansu Jidderh,meyasa zakayi min haka?meyasa zaka warware alaqar dake tsakanina da inteesar?meyasa zakaci amanar Inteesar?meya sa baka fada min ba tun  farko?taya hakan ma yafaru?taya ma zaka daura ma diyata aure da Ahmed?wannan auren ne sakayyar daza muma inteesar?abban Jidderh kayi tunani,auren nan baze yiwu ba".kallontta kawai yakeyi da mamaki,murya asama yace"da Ahmed mijin Inteesaar na daurama diyata aure,zama babu fashi kuma kada ki kuskura kikara min wannan tambayoyin naki marasa fasali".Cikin sauri take fadin"meyasa zakayi min haka?taya yata zata zauna da inteesar amatsayin kishiya?"kallonta yayi yace"nagama magana,sauran ya rage naki,nide na fada miki koda wasa kada naji kin fada ma Jidderh ko wani"yana gama fadin haka yabar falon yana buga babbar rigarshi,bayanshi tabi da kallo tana mamakin wannan lamarin,shin dawani ido zata kalli inteesar?.jiki a mace elmoudan yashiga gidanshi duk don kada inteesar ta fahimci yana cikin farin ciki mara fasaltuwa. A bedroom ya tarar da ita azaune tana bin karatun Qur'ani,shigowarshi yasata saurin katsewa ta dubeshi da murmushi kana tace"ango kasha kamshi"d'an waro ido yayi sannan ya hade rai yana kallonta kawai batareda yace komai ba yasamu wuri yazauna,da mamaki take kallonshi tana cewa"angon Jidderh lafiya?"kuma kallonta yayi batareda yace komai ba,dariya tayi tace"ko jidderhn kakeso in kira maka?"jawota yayi zuwa jikinshi ya rungume abarshi yana bubbuga bayanta ahankali,murya can kasa yace"meyasa zakuyi min haka?"."me mukayi?"..cikin fushi yace "Meyasa zaku hada baki kuyi min aure?"wani kayataccen murmushi tayi tace "sabida farin cikinka,rayuwarka bazata taba iya zama daidai ba batareda Jidderh,tazama wani jigo acikin rayuwarka,amatsayina na matarka mai kaunarka yazama dole in samo maka farin cikin dakake kokarin rasawa bayan inada ikon yin hakan.nasan kana yimin kara ne kuma nagode kwarai,fatana Allah ya zaunar damu lafiya cikin so,kauna da aminci,Ni Inteesar namaka alqawarin Insha Allah bazan taba zama mai baka matsala ba cikin zaman mu kuma nasan Jidderh ma bazata taba tayar maka da hankali ba"takarashe maganar tana fadin"you've to be thankful to Allah daya baka Inteesar and Jidderh cikin rayuwarka"hakika yakasa yadda da furucin inteesar,kallonta kawai yakeyi wani sonta na kuma shigarshi,tabbas itama tazama wani jigo acikin rayuwarshi,ya tabbatar bazai iya rayuwa babu ita aciki ba,taya ma zaya iya repaying wannan halaccin data masa?ajiyar zuciya yasauke batareda yayi murmushi ba yace"Inteesar farin cikinki kawai nake bukata  inteesar,dan Allah idan kinada matsala da wannan auren kifada min domin a warware shi tun ba aje ko'ina ba"murmushi tayi tace"farin cikinka shine nawa my forever,sannan farin cikinka baze iya cika ba batareda jidderh ba,we'll live a peaceful life full of love,tranquillity,and tolerance Insha Allah."Cikin kwayar idanunta yake kallo yana gasgata maganganun nata,tabbas Auren Inteesar is the best thing that could ever happen to his life,murya na rawa can kasa yace"Fasalta yadda kike acikin zuciyata abu ne mai matukar wahala Inteesar,tabbas da za a tsaga jinin jikina dazakiga naki yana ta gudana,Aurenki shine abu mafi girma daya taba faruwa dani,kin zame min garkuwa kuma fitilar dake haska rayuwata da mafi hasken haske,taya zan iya saka miki wannan halaccin dakika min?hakika bazan boye miki ba ina son jidderh sabida babu boye boye atsakaninmu,kin zamto matata,mai bani shawara and youre my bestfriend,gudun rashin kwanciyar hankalin ki yahanani bayyana sirrin dake raina,kada kiga hakan amatsayin karya alqawari duk da nasan my Inteesar ta zama malama,wallahi tun kafin inyi miki alqawarin nake kaunar Jidderh sede don cika miki alqawari yasa ban taba furtawa ba,nagode kwarai inteesar,nagode da wannan karamcin dakika min,bazan taba mantawa ba"hawaye ne ya soma gangarowa daga idanuwanta,hakika wata bala'yar'iyar wutar kishi ce ke balbala cikin zuciyarta,sai dai wannan lokacin tayi kokarin danne kishin tanuna babu komai,kishi halas ne dan dukkanin wata mace nada kishi sede wasu na tafiyar danasu cikeda jahilci,zage zage,rashin kunyah,makirci,munafunci da wasu ke yi amatsayin kishi ba komai bane fa ce shirme da rashin sanin ciwon kai.Tace"na rigada na shaidama hajiya komai kuma tayi farin cikin abinda na aikata,Elmoudan nasan kai adaline,Allah yataya is riko Amin,yau za'a kawo amarya ko?"murmushi yayi yace"ni ina nasani?amaryar ma tabasan dani aka daura ba"..inteesar tace"yeah yakamata itama abata surprise"cupping fuskarta yayi yace"I love you sweetheart,can't imagine life without you"..tana dariya tace"same dear,kaje kuyi magana ,yaushe za'a kawo mana amaryar mu?ni nama fison akawota yau din da aka shirya"jinjina kai yayi yace"anan kuma ina zata zauna?already fah anyi mata jeren ta agidan da ahwaz ya yi mata"gyada kai tayi tace"ni gaskiya nafison mu zauna gida daya"murmushi yayi yace"ai dama gida daya zamu zauna"..tayi murmushi kana tace"jekuyi magana da ahwaz din "kallonta yayi yace"naga tamkar kina korata"tayi wata yar dariya tace"wani irin kora kuma?"murmushi yayi yafita yana jinta har cikin ransa,fitar shi yayi daidai dawani irin matsanancin kuka data saki,Saurin dakatar da kukan tayi kamar yadda zuciyarta ta umarceta dayin hakan,karatun Qur'an takunna tachigaba da bi tana jin wani sanyi na ratsata.Koda elmoudan suka hadu da ahwaz ya shaidama elmoudan cewar dama already ya siya mai wani gida a alu avenue wanda zayayi containing din inteesar da Jidderh,anan yake fada masa cewar agidan  aka zuba kayan jidderh sauran na inteesar,murmushi elmoudan yayi yace"how can I ever repay you ahwaz?"shiru yayi yana kallon ahwaz din kafin yace"nawa kasiya gidan?"ahwaz yace"not up to 50million"gyada kai yayi yace"gobe insha Allah zan maka transfer "murmushi ahwaz yayi yace"alright".elmoudan yace"amma daka fada ma abbansu jidderh adakata dakai jidderh gidan zuwa jibi ko?"in comfirmation ya gyad'a kai sannan yanufi gidansu Jidderh.Afalo yaga hajiya nazaune tana murmushi,zama yayi akusa da ita yace"hajiya kinga abin arzikin da ahwaz da Inteesar sukayi min?"murmushi tayi ta gyada kai tace"babu abinda zan ce saidai inyi musu addua,Allah yamuku albarka baki daya".."amin"yace sannan yachigaba dacewa"kinga kuma yasiya mana gida a alu avenue wanda zai yi containing dinmu,gobe Insha Allah zan masa transfer din kudinshi,gobe zamu koma jibi kuma akai amarya"dariya tayi tace"angon Jidderh Allah yasanya alheri yabaku hakurin zama da juna"."amin"yace alokacin  inteesar tashigo falon,Aneesah,sumayyah,Jidderh da Jasmine ne ke zaune afalon abbansu kowacce nannad'e da laffaya,kansu na akasa banda kuka ba abinda sukeyi,tagumi Mami tayi domin gabadaya jikinta yagama mutuwa kuma takasa cewa kowa komai,gyaran murya yayi yace"Alhamdulillah da Allah yakawo mu wannan rana mai tarin albarka,ranace dabazamu taba iya mantawa da ba cikin tarihin rayuwar mu,Jasmine,Jidderh,anisah da sumayyah ina mai muku fatan alheri ayayinda zaku shiga sabuwar rayuwa,rayuwa mai cikeda kalubale masu tarin yawa,rayuwace mai hanya mai daukeda gargada,hakuri shine kawai nasihar dazan muku akai,haqurin shine gishirin zaman duniya,kuyi haquri aduk halin dakuka tsinci kanku aciki,kuyi ma mazajenku biyayya,yi nayi bari na bari shine naku,banason inji koda wasa wata ta taka dokar mijinta matukar bata ketare sharia ba,mahaifiyarsu tamkar Mami take awurinku  sabida haka treat her with respect,love,and tolerance likewise your father-in-laws.inason abinda zaya kawoku cikin gidan nan shine ziyara,Allah yayi muku albarka amin,kuji tsoron Allah kusaka aranku cewar ibada kuka tafi yi ba jin dadi ba,Aure isn't bed of roses,sai kun jajirce tareda yin aiki tukuru kafin ku cimma nasara,Allah yayi muku albarka yabaku zuri'a dayyiba"anan ya dasa aya sannan yakalli Mami yace"bismillah "tamkar bazatayi magana ba tace"abinda zan muku nasiha dashi shine hakuri,kuyi hakuri sannan ku bi mazajenku sau da kafa,Allah yayi muku albarka,ubangiji ya albarkaci auren nan  sannan yabada zuri'a mai albarka"ciki ciki sukace 'amin'sunata kuka,motoci daukar amare ne tamkar zasu fasa ciki da wajen bompai,aranar akai Jasmine,Aneesah da Sumy gidajensu banda Jidderh wacce tasoma tunanin koya fasa auren ne basaso su fada mata.Adaren su Inteesar suka soma shirya kayan su,ranar basu runtsa ba har washegari inda motocin dake dibar kaya suka zo suka kwashe,koda elmoudan yaga gidan yasan cewar ba permanently zasu zauna ba dole ya Gina musu wani gidan akan tsarin dayake so.Abin mamaki shine ko su baby basu san da yayansu aka daura Auren Jidderh,sune suka tayata kwana kafin su wuce gidan elmoudan,dakin yadawo shiru domin dama sune ke debe mata kewa,Anty mariya tashigo dakin tasameta azaune tana tunani,zama tayi tace"kidena tunani gobe dai za'a kaiki gidanki"murmushi tayi batareda tace komai ba.suman tsaye  elmoudan yayi sanda yashiga part din Jidderh,wato kayan da aka zuba mata ya wuce tunanin mai tunani,anan yakuma tabbatar da Alhaji Suleiman mai kudi ne,Falo biyu, d'akuna uku toilets hudu sai kitchen,part din Inteesar ma falo biyu ne saidai nata four bedrooms ne da four toilets sai kitchen guda daya,babu laifi gidan yayi kyau saidai ace Masha Allah.karfe tara saura inteesar tashiga gidansu Jidderh,zaune taga Mami afalo suna hira dasu Anty Mariya,sallamar Inteesar ce ta katse su yayinda Mami taji tamkar kasa ta bude tashige sabida tsananin kunyah,bedroom dinta takaita sede tasha mamakin ganin inteesar cikin farin ciki da walwala,to ko batasan abinda yafaru ba?.gyaran murya inteesar tayi tasoma fadin"kada kidamu Mami,hasalima na bada gudunmawa ta wurin hada auren Ahmed da Jidderh,zan kular miki da Jidderh Insha Allah domin tamkar yar uwata ta jini ce,nazo in miki sallama domin mun tashi daga wannan gidan kinsan da kunyah Ahmed ya zauna da Jidderh a katanga d'aya daku."murmushi Mami tayi sukayi sallama inteesar tafita,kiran anty Bebi ne yashigo wayarta,dagawa tayi suka gaisa zuciyar inteesar ta raya mata cewar ta shaidama anty bebin komai tunda yanzu itace amadadin mummy,inteesar tace"namanta ban fada miki yau aka daura auren Ahmed da jidderhn nan neighbours dinmu"gaban Anty Bebi ne yafadi,arikice tasoma cewa"sakayyar da Ahmed zaya miki kenan?irin wulakancin daya shirya miki kenan?kwata kwata yaushe Halima tarasu har dazai miki kishiya?maza ba yan goyo bane".murmushi inteesar tayi tace"Ahmed yayi abinda daya dace sannan nima na bada gudunmawa ta wurin hada auren,koda yake bazaki ganeba "anty Bebi tace"sallamammiya mara hankali,sekinyi dana sanin hada wannan shegen auren"tana kaiwa nan ta katse kiran. Kallon wayar tayi tana jinjina kai sannan ta karasa wurinsu elmoudan dake jiranta acikin mota suka tafi sabon gida,inda zasu fara sabuwar rayuwa.WashegariMisalin karfe shida na yamma aka kai Jidderh gidanta bayan tasha nasihohi masu ratsa zuciya,babu wasu mutane dayawa dubaga duk an watse shiyasa mutanen basu sha wuyar ganin alatun da aka zuba acikin gidan ba,mamaki sukeyi ganin gidan four sister's din iri daya babu wani banbanci sena gini,aransu suke cewa Allah sarki karamar itace ginin gidanta baika na sauran ba,sunyi yan gulmace gulmace da tsegumi kamin su kama hanyar komawa gidansu abbansu Jidderh aka barta ita daya tamkar wata mayya,daga mayafin ta tayi bayan sun fita tana karema dakin kallo,sosai ya burgeta takasa yarda natane halak Malak,toilet din dakin tashiga taga shima tamkar aljannar duniya,daga bisani tafita falo inda taga irin kudin da Abbansu ya kashe,sosai gidan yayi mata kyau tana ta murnar cewar kayan gidan mallakinta ne.Anan tayi maghrib da isha amma babu alamar shigowar mutum,tsoro ne ya soma kamata ta qudundune acikin duvet tana kiran sunayen Allah,Jitayi an bude kofa sanadiyyar haka gabanta ya shiga faduwa,knocking aka somayi akofar shiyasa saurin gyara zamanta tace"come in"wani murmushi yayi dayaji voice dinta,shiga yayi ya zauna akan kujerar madubi yana kallonta,baiyi magana ba shiyasa bata gane cewar elmoudan bane,mikewa yayi yakarasa inda take yana kokarin jaye mayafin data rufe fuskarta dashi,murya na rawa tace"ahwaz bari mana"wani dan murmushi yayi batareda yace komai ba ya fizge mayafin,tana daga ido sukayi two eye's da elmoudan,atsorace ta mike tana addu'o'i domin tasan ba gaskiya bane,taya elmoudan zai shigo har cikin dakin aurenta,ganin tana addua bai b'ace ba  atunaninta yasa tasoma kwalla ihu,saurin rufe mata baki yayi yace"dalla can yima mutane shiru,nine ahwaz din da'aka daura miki aure dashi"dan waro ido tayi she can't believe it,murya na rawa tace"no way,bazai yiwu ba"sakinta yayi yace"shikenan zaki yarda with time"yana kaiwa nan ya fice daga bedroom din.yana fita zuciyarta ta aminta da cewar shine mijin nata inba haka ba taya zai shigo mata daki a irin wannan lokacin,wani tsalle tayi ta dira akan gadon tana murna tamkar wata karamar yarinya,she can't believe elmoudan ta aura tama manta ta dawata Inteesar tashiga toilet ta dauro alwala tasoma jera nafilfilun godiya ga Allah..shima yana fita alwala yayi yasoma nafilfilu har dare yaraba,tunani inteesar yafarayi yasan tana can cikin kunci da bakin ciki,wani tausayin matarshine yasoma ratsashi,mikewa yayi yashiga bedroom din ya tarar da tayi bacci,bai tasheta ba yakoma falo yazauna yama rasa ta ina zaya fara,ga Jidderh Allah yabashi amma yakasa yin komai,yazama wani wawa ,dolo,kazar ma da Ahwaz yasiya musu bai bata ba harta kwanta,tsaki yayi yadauko yaci wanda zai ci yasaka ragowar a fridge,afalon yayi bacci tareda tarin mafarkai masu yawa.Kwanan bakin ciki inteesar tayi tamkar kowacce mata aranar da aka kawo mata abokiyar zama sede tayi kokarin dannewa,breakfast mai rai da lafiya tahada musu sannan tasa ashnoor takai site dinsu,anan ne take tsokanar elmoudan akan Jidderh,murmushi kawai yayi tashige bedroom din daya nuna mata Jidderh naciki,azaune ta sameta tana kallon hanyar kofa,shigowar ashnoor yasata saurin kawar da kanta,murmushi ashnoor tayi ta zauna tana fadin"amarsu ta ango"dariya Jidderh tayi batareda tace komai ba,ashnoor takuma cewa"zo muje muyi breakfast"kin tashi tayi hakan yasanya ashnoor fadin"ayyah ko bazaki iya tashin bane,barin in kawo miki nan"wata harara Jidderh ta wurga mata sannan ta mike tace"ashnoor bakida dama yanzu idan yajiki fa?bayan yasan shi baiyi komai ba mezaiyi tunani?"d'an waro tayi tace"hakane Allah baiji ba"dariya Jidderh suka tafi falon,fafur ta hana Ashnoor ta tafi seda sukayi breakfast dan ma elmoudan yayi fitarshi site din inteesar,bayan mintuna biyar baby ta shigo ta tana fadin"amaren daren jiya"murmushi kawai Jidderh tayi tace"kin tashi lafiya?".. baby tace"lafiya kalau,kefa?ya kwanan sabon wuri?"..tace"Alhamdulillah "nan suka bude sabuwar chapter din labari.Bayan awa biyu elmoudan yashigo yace"Jidderh zo muje,ashnoor da baby ku jirata tana zuwa.Bin bayan shi tayi dama dogon hijab ne sanye ajikinta,tana shiga falon gabanta yafadi ganin hajiya da Inteesar sede from their expressions yanuna mata cewar she's welcome to their family,ajiyar zuciya tasauke sannan ta gaida da inteesar,sosai hajiya tayi musu nasiha shima tayi mishi akan kwatanta aldaci,nasihohi masu ratsa zuciya tayi musu kana suka chigaba da fira banda Jidderh data sunkuyar da kanta kawai,mikewa inteesar tayi tajata zuwa bedroom dinta inda suka chigaba da fahimtar juna,duk wasu abu dabata so da wanda takeso saida ta shaidama Jidderh haka itama Jidderh tafada mata akan dole.Tamkar sister's suke zaune abedroom sunata hira,sosai elmoudan yaji dadin ganin su tare,bai karasa shigowa ba jin yadda inteesar ke shaidawa Jidderh yadda akayi aurenta da elmoudan,hira sukayi sosai kafin Jidderh ta mike zata fita sukaci karo da elmoudan saurin fita tayi yayinda yasaki wani murmushi yashiga bedroom din.Washegari su hajiya suka kama hanyar kaduna,sosai Jidderh taji tafiyar tasu babu dadi,girkin rana inteesar tayi tasa elmoudan yakira Jidderh suci abinci,babu laifi tasaki jikinta taci abinci sedai fira ce bata fiye saka baki ba,anan suka wuni har suka kai dare,karfe goma sha daya Jidderh tamike tace"zan kwanta anty seda safe"bata jira cewar inteesar ba tafice daga site din tamkar iska.murmushi inteesar tayi tace"da alamu har yanzu baka kashe arnen ba,wannan iri abu datakeyi yayi yawa"murmushi kawai yayi sukayi sallama yabi bayan Jidderh,a bedroom yasa meta tana kokarin kwanciya yace"ina son kisan cewar inashan tea kafin na kwanta"tashi tayi tace"okay"sannan tafita zuwa kitchen dinta ta tafasa masa ruwan ta hada masa ,afalo ta tarar dashi yace"zauna kijira ni"yana sha yana kallonta har tayi bacci bai gama Shan shayin ba,sai sha biyu da minti ishirin sannan yakashe kayan wuta ya dauke ta tamkar wata yar baby ya kwantar da ita akan gado shima ya kwanta yayinda ya dorata ajikinshi yanajin wani dumi na ratsashi.hakika yayi baccin dabe taba yiba cikin rayuwarshi.da asuba suka tashi kunya kamar ta kashe Jidderh ganin ta ajikin elmoudan....dakyar ta mike tashiga toilet sukayi sallar asuba,juyowa yayi yakalleta sannan tace"ina kwana?"."lafiya kalau"..yace yana murmushi,saukar da kanta tayi kasa tana murmushi yace"kin yarda yanzu ina sonki?"shiru tayi mishi tana blushing yakuma cewa"Alahmduliilah gamu de amatsayin ma'aurata "nan ma shiru tayi hakan yasanyashi jawota zuwa jikinshi ya manna mata kiss a goshi,saurin runtse ido tayi tana jin dadi na ratsata,hannunshi yasa ya zare hijab din dake kanta yana shafa sumar dake  kanta,murya can kasa yace"ina sonki jidderh"wani hawayen farin cikine yasoma zubo mata,hakika bata taba tsammanin wannan ranar zata zo mata ba."kiyi magana mana"tace"kunya nakeji"murya can kasa kasa hakan yasanyashi fashewa da dariya yace"kamata dai ayi puting end to this your shyness."qudundunewa tayi ajikinshi cikeda kunyah yayinda yake mata murmuring sweet endearment that makes her shed tears.

LABARIN JIDDERH Where stories live. Discover now