page 04

1.5K 84 1
                                    


Bazata iya tuna lokacin daya mata magana hankalinshi na kanta ba,bazata iya tuna sanda sukayi magana ta mata da miji mai cikeda kulawa da kauna kamar yadda suka Saba abaya ba?,bazata iya tuna sanda yashigo apartment dinsu ba se yau,toh duk meya jawo hakan?meyasa Alhajin ke aikata haka?meyasa ya tattara su yazuba akwandon shara ita da yayanta?meyasa ya dena musu dukkan wani abu da ada yake musu?meyasa ya canza saboda kawai yayi sabon aure?Duk Mami ce ke wadannan tunanin cikin ranta,Ta dade tana tunanin canzuwar halayen Alhajin kafin ta kwanta tana me fatan Allah ya rangwanta musu,Jidderh kam kwata kwata baccin yaki zuwa mata bare tasamu saukin radadin da zuciyarta ke mata,bazata iya tuna sanda sukayi dariya cikin farin ciki ba sede vice versa,why is life so unfair to them?after years of hardships and dedication?shin meke shirin faruwa dasu ne?hawayen dake bin kuncinta ta share da bayan hannunta,Tabbas sunga rayuwa,rayuwar da bazata rubutu cikin littafi ba,yaushe zasu samu farin cikin rayuwa?yaushe zasu samun dawwamamman farin ciki?at this time all they do is they laugh in pain. Ita meze kaita auran me mata?meze sa ta zauna da kishiya?upon all what has been happening in their house .Nan tausayin Maminsu ya kamata,Tabbas samun mai tsantsar hakuri kamar Mami se an tona,ta zauna da mahaifiyar miji in so much pain,bata taba appreciating abinda tayi ba sede zagi da cin mutunci,banza wofi yafi mami mutunci da daraja a idon grandma,komai tayi bata iya ba,komai tayi ba dede ba,what kind life is this?meyasa iyayen miji ke yi haka?shin su ba d'an wata suka aura ba?ba d'an wata bane ya rikesu har suka kawo yanzu?shin basa tunanin sunada 'ya'ya mata wanda definitely gidan wani zaa kaita,basa tunanin rashin kwanciyar hankalinta suma rashin nutsuwarsu ne?zasu so su ganta acikin bakin ciki da damuwa?toh meyasa suke takura 'yar wasu,ko ita ba uwa bace ta haifeta?ko kuma daga sama ta fado?(iyayen miji especially mata mu kula wallahi we reap what we sow the very hard way,kina tunanin zaki cuci yar wani ne Allah yabarki?)Dare ya ratsa gari yyi tsit,mafi daukacin mutane sun kwanta domin hutawa dubaga kujuba kujubar dasukayi da rana,mafi karancin mutane ne zaka samu idanuwansu biyu adede wannan lokacin,Elmoudan ne bisa sallaya yana rokon Allah yabiya masa daukacin bakatunshi na alheri,bacci yamasa kaura sabida dinbin tunanin daya sha kanshi matuka,kallon gefenshi yyi inda Inteesaar ke bacci peacefully murmushi yasakar sannan itama ya roka mata Allah ya rangwanta mata azabar kishinta. Yana nan zaune yana tunani ya yanke shawarar samun malamin daze rinqa zuwa yana tunatar dasu akan dokokin musulunci sannan yarinqama Inteesaar wa'azi akan kishiya da zaman duniya.
Washegari.Da Asuba suka tashi kamar yadda suka saba dubaga office da Elmoudan zeje,Tea kawai ya sha bayan yagama shiryawa cikin black suit dinshi datayi fitting dinshi ta fito da tsantsar kyawunsa fiyeda tunanin me karatu,dayake dogo ne amma ba irin tsayin nan ba sosai,Fari ne sol kamar tsada sannan yana da doguwar fuska wacce ta qawatu da zarkadeden dogon hancinsa daya dace da cute pout mouth dinshi,yanada dara daran idanuwa wanda suka kasance fari tass kamar na jarirai dubaga zam zam dayake digawa,Shiba siriri ba sannan Shiba mai kauri ba but fallen in the middle,he has a sweet aura about him,ga kwarjini da sanin yakamata,Elmoudan nada hankalin daba kowa kedashi ba Shiyasa yyi fice ba'a agidansu kadai ba har danginsu,Saukowa yake daga saman staircase sannu ahankali Hannunshi rike da waya,rurin data farayine yasa yakai dubansa gareta,dasauri yyi picking tareda karawa akunnenshi,kamar yana gabanta ya duka "ina kwana Hajiya?hope kun tashi lafiya?"...murmushi naga yyi kafin yace"ehh lfy klau Alhamdulillah "..jim yyi nawasu yan dakiku "ehh hajiya inshallah zanzo amma se weekend"...dubansa yakai ga Inteesaar data tsaya tana kallonsa,murmushi ya sakar mata sannan yace"toh hajiya ayimin afuwa wallahi ayyuka ne suka min yawo,yanzu ban fiye zama ba shiyasa"..kome tace bansaniba senaji yace"yawwa Hajiya cikin wannan satin zanzo"...Kallan wayar yakeyi da murmushi kafin ya maida ta cikin aljihu,Inteesaar da tun faruwar wayar tahade rai,gabadaya ta tsani wani ya rab'u mijinta inba ita ba,shikuma mamakin yadda taji yana waya da mahaifiyarshi batace agaidata yake ba sannan baze iya tuna randa ta kirata ba don su gaisa ,he's really trying his best akan auransu but Inteesaar is not helping matters,bayason sama kanshi damuwa shiyasa yacire tunanin daga cikin ranshi. "Har ka gama wayar?ai nazata..."katseta yyi tahanyar daga mata hannu "banson jin komai"yana kaiwa nan yafice daga gidan yabarta cikeda tsananin mamaki wannan alamari.wannan wani irin mutum ne?mena mishi yadauki fushi?ganin batada amsar tambayarta yasa ta koma ta zauna,haka ta yini sukuku,ganin azahar tayi yasa ta dafa indomie taci bayan ta shirya cikin wata atamfa yar holland pink and ash wacce ta amshe jikinta fiyeda tunanin mai,mayafi ash tayafa tafita bayan ta kullle kofarta,gidan Alhaji Suleiman ta shiga,afalo ta tarar da mai aiki tana en share share,bayan sun gaisa take tambayarta ina Mami?,jiki bbu kwari Laminde wacce takasance yar aikin tashiga ta kira mata Mamin,gaisuwar mutunci sukayi sannan suka chigaba da hira gwanin ban sha'awa kai kace age mates ne.Adede lokacin Aneesah,Jasmine da Sumy suka shigo gidan daga makaranta,dayake yau dukkaninsu basuda lectures din yamma,agajiye suka shiga falon tareda samun wuri su zauna,Da kulawa suka gaishe da Inteesaar wacce fuska asake ta amsa babu yabo babu fallasa,Duk da zuciyarta na gargadinta da cewar daya daga cikin yan mata ka iya auran mata miji,gabantane yyi mugun faduwa wanda atake tafita daga cikin hayyacinta tana rokar Allah kada ya nuna mata wannan rana yakasheta kafin ranar,tuno maganar lallashin da Elmoudan yamata yasa hankalinta dawowa jikinta. Dakallo gabadaya suka bita sannan suka mike suka wuce bedroom dinsu cikeda mamaki,Mami ma mamakine yacikata har ya kaiga tace"hope de something isn't wrong"sassanyar ajiyar zuciya ta sauke sannan tace "babu komai"tayi kokarin danne damuwarta dan kada mafi girman makiyiyarta wato Mami ta fuskanci halin datake ciki,shiru ne yabiyo bayan haka,seda suka danyi jimm nawasu seconds kafin Mamin tace "ya labarin su mamanku kuwa?"..."lafiya kalau"kawai tace agajarce wanda hakan yyi dede da Shigowar Jidderh daga Makaranta,ahankali take tafiyarta dubaga tunanin daya sha kanta,har kasa ta duka tagaida Mami da Inteesaar sannan tawuce dakinsu,jim kadan takuma fitowa "Mami me aka girka?"..."ban saniba tunda bakida kafa da idon zuwa ki duba"fadar Mamin,"yi haquri"Jidderh tace sannan tamike tashiga kitchen din tana me jin haushin yadda Mami tayi responding dinta agaban inteesaar.koda ta duba Taliya da miyar bushashhen kifi aka dafa,kallon abinci Inteesaar tayi ta hadiyi miyau domin koda Mami tamata bismillah kin ci tayi sabida wasu dalilai nata.Bayan kimanin mintuna ashirin Inteeesaar ta mike ta wuce gida,alokacin gabadayansu suna zaune afalon Mami kecewa"Allah sarki Inteeesaar yarinya mai hankali da sanin yakamata "jinjina kai sukayi in comfirmation banda Jidderh da wani zubin bata kaunar a ambacin sunan matar agabanta.summy ce takuma cewa"Ai Inteesaar nada kirkin daba kowa kedashi ba,tsiyata da ita daya akan mijinta ba abinda bazata aikatama mutum ba"..."ke kuwa miji ai abin kulawa ne na sosai da sosai,banga lefin taba"cewar Jasmine,"amma de bekamata tariqa kishi damu ba kasancewar tanada tabbacin babu wata alaka tsakaninmu da mijinta"...Aneesah tafadi"ai koda akwai bedace ba,mijinta yakamata tama duk abinda zatayi ba yan matan unguwa ba."cewar Jiddeh..."rufe min baki shashasha kawai,bansan me Inteesaar tamiki ba kika tsaneta"acewar Mamin,"niba tsanarta nayiba gaskiya kawai nafada"..."ke har wata gaskiya gareki?banza kawai sakarya tashi kibani Guri mara hankali kawai"..mamakine yacika Jidderh jin kalaman Mamin,bakaramin haushi tajiba tamike tashige dakin.nan Mamin tadasa masifar cin mutuncin da abbansu ke mata,complains iri iri tarinqa fada musu abinda ke wakana atsakaninsu wanda na ce Allah shi kyauta.Elmoudan dake office bayan ya idar da sallar la'asar ya dauki wayarshi yana dan latsawa,wata number yagani tamasa magana ta whatsapp,shiga yyi yaga an rubuta"Hi Ahmed,it's been quite so long,how have you been??"...da mamaki yyi reply "fine but who?"..harze kashe data yaji message yakuma shigowa"it's Raliya"gabanshine yafadi amma yadake "ohhh raliya yh kke?"..be gama fita ba takuma masa message "lafiya,love you"...shima atake yamayar mata da"you still do?"atake ta sauka shiyasa bega reply din ta ba ya kashe wayarshi tareda komawa bakin aikinshi. Karfe 6 dede tamasa acikin gidansu,shiga ciki yyi cikin takunsa me sa mara jin magana nutsuwa. Afalo ya tarar da Inteeesaar tana zaune,shigowarsa batasa ta motsa ba,karasawa yyi inda take ya rungume bayan ya ajiye wasu ledoji kan console kafin yace"ya ba magana?"shiru tamishi ita adole tafishi yin fushi gameda abinda yafaru da safe,ganin haka yasa be tsaya bi takanta ba ya shige bedroom dinsu,wayarshi tayi saurin picking tayi unlocking zuciyarta na tsananin bugawa,Inbox tafara shiga ganin ba wani message yasa tashiga whatsapp,da sauri tashiga recent chat din dayayi da Raliya,tana karantawa tana zubarda hawaye,sanda tazo wurin da Raliya tasa love you dinnan tayi wurgi da wayar ta fashe instantly.

LABARIN JIDDERH Where stories live. Discover now