11-15

5.4K 261 1
                                    

Da dare ranar taje take roqon umman ta amince jiyad yaxo kafin baffanta yafito meeting

cikin nuna halin rashin amincewa ta juya tana kallon t.v
ta durqusa qasa tana roqonta
tace pls ummana,idan baki taimakamin ba waxai taimakamin,idan bn sami farin cikinki ba nawa xn samu,

umma jiyad yana da mutunci bafa irin samarin dakike tsammani bane yana da kirki yana sona, umma kisoshi ki amince da shi wlhy ina sonsa.....

umma tayi shiru tana naxari kafin
tace rayuwar duniya fari'ah ba'a mata agargaje, samari da kike gani duk mayaudara ne basu ajiye komai ba sai qarya,inaso intuna maki mgnr mahaifinki kada rudin jiyad ya mantardake matuqar kika bari wannan semester kika fadi course daya xai maki aure da duk wanda ya samu....

jikinta a sanyaye take kallon ummanta dan bata manta rabonta da karanta handout ko kuma yin lecture cikin nutsuwa tun sanda ta hadu da jiyad komai ya fita ranta, hawayen datake maqalewa suka xubo ta maida kanta jikin cinyoyinta tana kuka tana fadin ban mantaba umma,amma bansan yanda xnyi da xuciyataba umma, shi nakeso shina fara so,umma ki gayamin ya xanyi....ta fada bayan ta dago idanunta jawur tana kallonta
[11:25PM, 4/5/2016] pherty: umman ta kalleta cike da tausayawa ta dafe kanta tana fadin

mafita dayace fari'ah kitashi da addua dan nemawa kanki sauqi akan abinda yafi xama alheri agareki,xn tayaki da addu'a amma kicire sonsa sosai a xuciyarki kisoshi kadan namiji bafa abin yarda bane....

tace i trust him umma, jiyad baxai cutar dani ba,baxai cutar da rayuwata ba kiyarda shi mai kirkine

murmushi kawai umman tayi ta girgixa kanta ta tashi ta nufi sashenta

tace umma kin amince yaxo kafin su baffa sugama meeting

ta gyada kanta batare data juyoba,

tayi tsalle cike da murna ta tashi ta nufi dakinta......

Baafi minti talatin ba da kiran nasa yaxo, da sauri ta shigar dashi falon ummanta kafin taje ta kirata su gaisa da jiyad din...

a yanda umma ta lura,jiyad mutum ne mai kawaici sosai tundaga lokacin daya durqusa ya gaida,ya kasa hada ido da ita, yana da kirki kamar yanda fari'ah ta fada amma bata sani ba ko hr axuciyarsa yana ji da yarta sosai.....

ta tashi ta fice tabasu wuri, ta matso da murmushinta tana kallonsa
yau kaga ummana kagayamin me ka fahimta a yanayinta

shima fuskarsa da murmushi yake kallonta
yace umma nada kirki batada kyara da alama xata soni....
tace ai tana sonka saura baffa kawai, ta fada tana yatsina fuskarta.. ya kauda xancen ta hanyar fadin

baby(sunanda yake kiranta) exam x approaching, yaka mata mutsaida duk wata wasa dake gabanmu mu fuskanci karatun mu kinji....

ta bata fuska tana fadin ban fahimceka ba
ya tsaida idanunsa akanta
yace xamu rage haduwa skul saboda muriqa attending lectures,ina so kuma kiriqa karatu pls baby.

tayi shiru kamar ranta baisoba
yace pls baby,ina sonki amma kinsan komai baxai yiwu ba sai da ilimi ko?
ta gyada kai tana kallonsa a sanyaye
yace karki damu ai ga waya ko,kuma dole xamu dan hadu a skul koda baxamu dade ba amma baxamu sake rasa lecture ba kinji....da hakan ya shawo kanta ta amince xata riqa karatu, sunyi hira sosai kowane xuciyarsa cike da farinciki kamar kada su rabu......

MATAR WAYE?Where stories live. Discover now