Haka rayuwa tacigaba da gudana tsanakin ita da iyayen andy ba dadi da dadi,
duk suna cikin jimami da rashinsa, ba kamar fari'a ba databi ta xame ta rame tayi wani irin fari ga tunanin rashin andy ga wahalar laulayin ciki shike sanya iyayen tausayinta ta kowane hali,
a ynxu batada aiki ko abokin hira kamar qur'aninta koda yaushe tana cikin karatu ba kamar da ba,
shirunta da rashin mgnrta kesanya iyayenta damuwa, rarrashin duniya ba wnda iyayen basuyimata ba kuma ba irin nasifar dabasa mata, ganin taqi sauyawa daga halin datake ciki yasa baffa ya yanke hukuncin maidata makaranta meyiwuwa hayaniyar makarnta xata mantar da ita komai,
cikin saa akasami admission tafara xuwa badan tasoba sai da taga bacin ran mahaifinta kana ta fita, ranar da kuka tabar gidan hr abin kebawa baffa mamaki.
Ganin ba sarki sai Allah kuma wanda ya riga ya mutu ya mutu shiyasanya ta soma sakin ranta ga sabbin qawayenta datayi, sai dai wannan karon ta killace kanta da wasa karatunta tasanya agaba tare da renon cikinta hr lokacin haihuwarsa.
Alhmdllh ta sauka lfy bayan doguwar naqudar da tasha tasami yaranta twins duka mata,
iyayen sunyi matuqar murna abba hrda kuka inama andy na raye yaga kyautar daya samu daga mai komai.....
a duk hirar da xasuyi idan yace andy kaqi kayi aure rayuwar duniya bata din din bace babu abinda yafi kyau ga musulmi kamar ya mutu yabar baya, yabar abinda mutane xasu dauwama suna gani sunayima addu'a, sai yayi murmushi yana kallonsa
yace abba kaqi ka fahimci rayuwatane ni ban taba soyayyaba bansan yanda ake neman mace ba, bnsan irin maccen danakeso ba, bnda plan akan kowacce mace Shiyasa nake neman xabin Allah,
abba yace Allah yabaka macce tagari andy, yace amin yana kallonsa kafin
yace abba kasan inason yara da yawa, qananan yara suna birgeni,inaso su xagayeni ina masu wasa, abba har dreaming nakeyi akan yara,abba ya kyalkyace da dariya yace gashi kataso inda babu yara,qaninka dayane tal jiyad nima inaso kutaramin jikoki kaida jiyad,
cikin murmushi yace insha Allah abba,jikoki hr sai kace masha Allah.
suka sa dariya pokaci daya tamkar wasu abokai, nan take abba ya fashe da wani irin kuka mai tsuma xuciya,
ga burin andy yacika.amma biganiba, baiga ya'yan dayake matuqar soba ashe duk tunaninsa da hashensa baxasu cikaba, hajiya tace kayi haquri Alhaji, duk mai rai mamacine muma xamu samesa acan addua yakamata ayimasa.
[7:24PM, 4/19/2016] pherty: Ranar suna yaran sunci sunan Hayfah da Hayrah, masu kyau dasu kamar ubansu sunada shiga rai shiyasa koda yaushe jiyad na gunsu wnda hakan ba qaramin takura fari'ah yakeba shima jiyad baya damuwa da ita bayan gaisuwa ba abinda ke hadasu sai kawai yamaida hankalinsa ga yaran.gata da kulawa yaran kesamu sosai,abba yaturo nanny hr biyu saboda yaran, fariah ba wani damuwa tayi dasu sosaiba amma tana sonsu kamarme sai dai tana nuna kawaici ga iyayenta kamar bata damu da yaranba.
karatu take haiqan, bayan shekara biyu tana shekarar qare skul din,lokacin yaran sun taso suna gudunsu ko ina gwani bn sha'awa basuda banbanci illah kalar fata hayfah ce fara sai hayrah kalar choco bayan wannan basuda wani banbanci tundaga idanunsu bakinsu hancinsu da gashin kansu,
akai akai ake kaisu inda abba wnda jiyad ne mai qoqarin haka sunyi matuqar sabawa da kakanin nasu sosai fiyeda mamansu.....
Sunada shekara biyar lokacin girma ya taso.masu kuma alokacin fariah ta kammala karatunta sai aiki datake xuwa,
suna xaune a falo tare dasu tana gyarawa hayrah gashinta yayinda hayfah k jikin umma tana fitinar uncle jiyad baixo sunfita yau ba..., dai dai lokacin baffa ya shigo ya xauna a kusa da umma tana yimasa sannu da xuwa,
hayfah ta sauko da gudu ta fada jikinsa tana oyoyo,ya dauketa yana dariya sosai yayinda hayrah k qoqarin xillewa taje garesa
fari'ah tace komai nacinki baxaki tashiba sai nagama gyara kan,tunda kinga baffa shine xaki nuna halinku na butulce.... aikuwa ta fashe da kuka tana qoqarin xillewa, baffa ya tashi ya karbeta yana fadin haba autah meyasa kike takura yarinyar,
fari'ah ta tashi tana tunxure bakinta ni baxan qarasamata taje umma ta gyara mata kan, ta juya xata fice
yace xo nan fari'ah, ta dawo ta xauna a kusa dashi, kudi ya ciro ya bata yana kallonta itama tana juya kudin tana kallonsa da mamaki alamar na menene?yace kudin aurenkine fari'ah, nariga na bada ke a karo nabiyu, na auradda ke yau a massalaci.......
xumbur ta miqe tana kallonsa kudin suka fadi suka xube hayfah da hayrah suka sauko da gudu suna rigengen dauka,
tace ni baffa?
yace eh, kiyi haquri oi yafemin ba ina niyar cuta maki ba illah son farincikinki da kwanciyar hankalinki, nasanki da haquri da biyayya shiyasa na yanke wannan.hukunci,idanunta sharkaf da hawaye tace baffa kodai baka sonane kake kyautardani ga duk wnda kaga dama, kake hanamin auren wnda nakeso, bayan aure na biyu nice ya dace na xabawa kaina miji, baffa meyasa xakamin haka bayan duk biyayyar danayima abaya,
ya taso hade da dafata itama umma wannan karon ranta.abace take kallonsa sai dai batayi magana ba amma axata yarda da wannan ba baxata yarda a qara cutar mata yarinya ba saboda son xuciya
yace ina sonki fari'ah shiyasa nake nemamiki irin maxan danakeso maxan danasan baxasu cutardake.ba kigayamin ko akwai wata cutarwa da andy ya maki axamanki dashi,
ta fashe da kuka batare da tayi magana ba
yace kiyi haquri idan nayi maki laifi ki yafemin xabina alherine agareki, ya juya ya haura sama,a fusacce ta dago tana kallonsa yana taka step
tace Baffa!
ya juyo yana kallonta da mamakin yanda takira sunansa cikin tsawa idanunta sun kada sunyi jawur saboda bacin rai,idanunta kyam akansa
tace inason wannan karon kasake gayamin ni MATAR WAYE?