101-134

3.6K 188 1
                                    

A hankali ya sauko daga saman bene ya qaraso xuwa gareta

yace autah meya cnza ki haka, meyasa kika dawo mai tsananin fushi a yanxu?

saboda kana tauye haqqinta amatsayinta na yar'ka kana nuna mata fifiko kuma dole tanada haqqi akanka....acewar umma ranta a bace

yace saboda nasan tanada haqqi akaina yasanya nake nema mata maxan da suka dace da rayuwarta maxan danasan baxasu cutar da ita ba kigayamin Asmau laifine dan mahaifi yakai yar'sa gidan mutunci?

tace kada kaso kanka da yawa alhaji,kada ka manta fari'a nada ikon xabawa kanta miji a halin yanxu,idan da farko ta karbi tayinka tayima biyayya bai kamata a yanxuma kayi mata dole ba,

ka maida fari'ah kamar wata caca duk namijin dakaga dama shi kakebamawa, ka maidata tamkar wata almajira,baiwa ko wata marar gata da baa neman ixinin aurenta ko shawararta sai dai kawai a daura mata aure kamar wata kaxa,

kamanta auren dole a yanxu ba tasiri yakeyiba bai xama lallai dole suso junansuba,idan kana tunanin anyi dace a auren farko sai akace wannan ma yaxama dole ya sota ko kuma ita taso shine?

ta girgixa kanta hade da jan hannun fariah tana fadin babu adalci baxan lamuntaba wannan karon idan kadaina sontane ni ina son ya'ta inason farin cikin fari'ah, ta jata cikin kuka ta juyo tana kallon sa gab da xasu shiga daki

tace baffa dan Allah kagayamin ni MATAR WAYE?

Cikin kakkausar murya yace ke matar JIYAD ce.

lokaci daya suka juyo suna kallonsa bakijsu a hade sukace
wane jiyad?
yace jiyad qanin marigayi andy,

banayi haka dan cutar da ita ko kuma cusgunawa rayuwartaba illah nema mata sauqi itada yaranta,
jiyad ya nemi aurenta bayan ya bamu lbrn soyayyar da kukayi a baya, ya amince da aurenkine a karo na biyu saboda bayason twins su taraigaita bayason suyi agolanci a wani gida bayan gashi,

kuma bayan haka jiyad yana sonki hr ynxu kuma kema na tabbata kina sonsa shiyasa hrna amince aka daura maku aure,

a ynxu ba abinda xnce maki gameda rayuwar aure,kinsan komai idan kinyi da kyau xakiga da kyau ina qara jadada maki kiyi haquri kibi mijinki kiyi masa biyayya shine aljannarki, ya juya ya fice, nan ta durqushe cikin wani irin tashin hankali tana kuka sosai.
[2:08PM, 4/23/2016] pherty: *

A daren ranar aka kaita badan tasoba, iya rarrashi ba wanda umma batayi mata ba harta haqura,

bayan baffanta ya fice kamar yanda ya kawota da farko bai bari an rakota ba, ta tashi ta rufe qofar dakin kafin ta kwanta a luntsumemen gadonta cike da kewar twins dinta,

a hankali take tunano rayuwarta da andy yanda ya wahala da ita da farko da soyayyar da sukayi ta miskina tana qara tunano rayuwarta da jiyad,

batajin xata maimaita rayuwar datayi da andy a farko da jiyad, jiyad yanada muhimmanci a xuciyarta shine tafaraso dalilinsa ta soma fuskantar matsalar so da damuwa, amma batajin xata iya yimasa sonda takewa a andy a ynxu domin andy ya riga yaxama wani bangare na jikinta, andy mutum ne da mace ta xauna dashi baxataso rabuwa dashiba, yanada sauqin kai da shiga xuciya,yana da haquri da nutsuwa bayada saurin fushi kamar jiyad shiyasa abu kadan yake amusing dinsa, ta rumtse idanuwanta cike da tunani iri iri......

         106 to 110

A bangaren jiyad kuwa a kasalance ya nufi nasa sashen kai tsaye toilet ya nufa ya dauro arwallah yaxo ya tada sallah,

ya dade a sujada yana roqon alherin wannan auren garesa yana qara roqon Allah ya kawo masu alheri ya kauda duk wani sharri acikinsa.....

bayan ya idar ne ya kwanta rub da ciki idanunsa a rufe yasani hr axuciyarsa yana son fariah bai taba daina sonta ba illah yafison farincikin yayansa shiyasa yayi qoqarin cusguna mata ta hanyar dauko fidoo dan cin xarafinta amma sam ba budurwarsa bace yayi hakanne dan fariah ta gyara rayuwar aurenta yayansa shima yaji dadin aure kamar kowane namiji amma yau babu shi....

MATAR WAYE?Where stories live. Discover now