36-45

3.3K 196 3
                                    

Al'amura sai cigaba suke tsakanin gidan baffa da abba, sai shirye shiryen biki ake yayinda soyayya da shaquwa k Dada shiga  tsakanin jiyad da fari'ah...

Tym dinda aka kawo kayan aure umma tayi matuqar mamaki hrta kasa boyewa lokacin da iyayen mata suka five

Tace bangane ba Alhaji kayan auren waye haka?
Yace Na fari,ah  ne akwai wata budurwa a gidanne bayan ita?

Tace hr ynxu bn fahimcekaba Alhaji,
Ya dauke kansa yana fadin aure xn mata tunda batason karatu

Tace haba Alhaji y......ya katseta yana kallonta

Aure ne xaayishi a satin sama idan kuma kikasa ta bijire ranki xaiyi matuqar baci ya tashi ya fice......tabisa da idanu xuciyarta Na matuqar bugawa Dan batasan yanda fari,ah xata kasanceba idan taji xaa aura mata wani ba jiyad ba dai dai lokacin fari,ah ta shigo

Cak ta tsaya tana kallon manyan trolleys dake xube agun ta kalli ummanta bayan ta xubar da kayan hannunta ta qarasa gareta da Sauri

Umma kayan waye wadannan?
A sanyaye tace kayan aurenki wai......

Tayi murmushi ta haura sama tana fadin umma Ni banason wannan wasar kayan auren xaynab ne kike cewa nawane,inbnda abinsu baxaa kai gidan iyayentaba sai anan...ta qarasa shigewa dakin tana dialing number jiyad

Ta xauna akan stool tana fadin baby albishir dinka
Yace goro
Tace ankawowa xaynab kayan aure?
Da gske baby..waxata aura ne?
Tace oho mata
[6:09PM, 4/8/2016] pherty: Yace toh fa,kinsan Yaya Andy shima Yau ankai kayan aurensa
Lah shima aure xaiyi Ashe munada biki
Yace sosai ma sai bayan bikinsa xnma Abba magana ayi mgnr aurenmu
Tayi dariya sosai cikin jin dadi
Tace Allah ya kaimu
Yace amin kigaida xaynab ina mata murna kafin nakirata...
Tace olryt tor shikenan ta tsinke wayar...ya ajiye wayar yana kallonsa
Yace baby ce ta kirani ankaiwa cousin dinta kayan aure
Andy ya gyada kansa yana gyara agogon hannunsa
Yace hakan Nada kyau saura kai
Yayi dariya ya xauna yana fadin inason baby sosai dole Na aureta baxan yarda wani ya rigani akanta ba....
Andy ya xauna yana fadin
Allah ne yasan gaibu jiyad,shikadai yasan ko ita MATAR WAYE?
jiyad yace matatace Yaya idan ban aureta my life will be useless Kuma kowaye ta aura sai na kashe.....Andy ya rufe masa baki da hannuwansa
Yace kadinga sa Allah a xuciyarka wannan furucin Sam bai dace dakai ba jiyad,tunda kanason baby nima ina tayaka sonta.

Yayi dariya yana fadin nabari Yaya duk abinda bakaso banaso, ynxuma kashe wayana xnyi hr bayan bikinka cos banason damuwa yan mata na damuna Yaya Dan kawai sun ganni beauty ga kudi da qatuwar mota

Andy yayi dariya sosai kafin
Yace tor qila baby ma kudin tagani

Yasaki baki Yaya babanta mai kudine fa soyayyar gsky mukewa juna Dan Allah kaxo muje kaganta pls Yaya

Yace tor shikenan......

       41 to 45

Bayan isha'i suka shirya sukaje gidan,nesa da gidan sukayi parking sanin baffanta baya bari,da wayar Andy ya kirata tunda ya kashe tasa wayar, bata jima ba kuwa ta fito.....yana ganinta ya fito da sauri yana murmushi Andy Na xaune a mota yana qare mata kallo Ashe ma a hotonta baiga komai ba tafi kyau a fili, wani Abu yakeji tunda ga kansa hr yatsansa ......Yaya kafito ga baby ya katsesa masa tunani

Ya fito,baby ta qaraso tana kallonsa
Nyc to meet you our bros
Yace tnk u sis
Tana murmushi take kallon jiyad
Baby yayanka yafika kyau sosai...
Yayi dariya yana fadin ba kyau ba aji da kudi duk yafini inasonsa kisoshi baby
Ta gyada kai tana murmushi
Tace ina tayaka murnar aurenka Allah ya nuna mana ranar musha biki
Yayi dariya yana fadin amin tare da naku

Duk sukasa dariya ta rufe fuskarta da hannayenta abinda nayi matuqar birge Andy yanason mace mai kunya karo Na farko da Andy yasoma planning akan irin maccen dayakeso.......
[6:09PM, 4/8/2016] pherty: *

Daren ranar daxaa daura masu aure baffa ya kira fari,ah ya gaya mata komai akan auren ta

Ta fashe da kuka hade da riqo hannayensa
Tace pls baffa ba danni ba Na amince da auren amma ka auramin jiyad, shi nakeso pls baffa

Yace dama kina da Wanda kikeso
Ta gyada kai tana kallo sa
Yace ko shine ke hanamiki karatu auta
Tayi Saurin girgixa kanta tana fiddo idanu waje...
Ya riqo hannunta
Yace kiyi haquri fari,ah nayi maki miji yaron aminina kamar ynda nagaya miki daga farko ina roqonki daki haqura ki karbi xabina kimin biyayya kiso abinda nakeso,sanin kanki baxan cutar dakeba baxan aura naki Wanda bn yarda da tarbiyarsa ba....

Ta qara tsananta kukanta hade da sanya kanta a cinyoyinta tana kuka sosai
Hakan yasa jikinsa yayi sanyi, a tausashe umma  tasoma yi mata nasiha kadan daga  aure

1. na farko shine kiji tsoron Allah duk abinda
xakiyi ga xaman takewar aurenki to kiji tsoron
Allah
2.ki xama kamar baiwa ga mijinki sai shima
yaxama kamar bawa agareki
3.kada ki nisance shi domin nisanta dashi xai
iyasa ya mantaki yaxamo baya damuwa dake
4.ki kiyaye masa lokacin cin abincinsa da
barcinsa domin yunwa tana hassala mutum kuma
gurbata masa barci xaisa ya fussata
5. kikiyaye masa gidansa dukiyarsa da danginsa
domin sunada muhimmanci agaresa
6.ki girmamashi matuqa shima xai girmamaki
fiyeda yadda kowa xai girmamaki
7.kada ki juya masa baya yayinda ya kusantoki
8.kada ki fiye naci da fushi alokutan da kike
neman wani abu daga garesa tor lallai xai qosa
dake
9.daga qarshe dan girman Allah kiyi haquri ki
xamo shimfida ga mijinki xai xamo rumfa agareki
har qarshen rayuwarki
Allah yayi maki albarka

Baffa yace amin

Sai abin ya qara tunxurata ta dago a fusace tana kallonsa sai daya tsorata ganin yanayin datake ciki

Tace kagayamin Ni MATAR WAYE?
Yace ke matar Muhammad ce fari,ah.....ta juya tana kallonta idanunta jawur taf da hawaye
Tace umma kigayamin Ni MATAR WAYE?
A sanyaye ummar tace ke matar jiyad ce

Cikin kuka tace kece mai sona umma,kece kika damu dani,kece keson abinda nakeso.....umma kigayawa baffa matsayin jiyad a xuciyata,umma kigayamasa bana sonsa baxan iya haqurin xama da wani bayan jiyad...ta tashi tafice cikin matsinancin kuka sosai, ta janyo wayarta duka layin jiyad akashe suke ta xube nan qasa tana kuka sosai.

MATAR WAYE?Where stories live. Discover now