66-75

2.8K 197 1
                                    

Tun daga lokacin jiyad ya rage xama a gidan idan ma yaxo gidan yakan xauna a falo tare da ita ya janyo wayarsa yana hira da wata budurwa acewar shima ya.manta da ita itama ta mantashi ta rungumi yayansa yanason yayansa ya samu kulawa da soyayyar aure shiyasa yake.mata.haka,

ya lura gabaki daya andy yaxama sukuku a gidan bashida wani aiki sai ja qoqarin kula da fari'ah dan ganin kawai ya faranta mata, shine kuku shike mata girki tana kwance shike gyara dakinsa yaxo ya gyara nata dakin, xai bata lokacinsa yabar aikinsa na office yaxo ya xauna da ita dantayata fira, duk maaikatan gidan ta hanasu aikin komai acewar andy xai mata, abinda k qarawa jiyad haushi sai ranar dayaxo yasami yayan nasa a toilet yana mata wankin undis, a fusacce yaje ya sameta baqaqen maganganu ba wanda bai gayamata ba saboda ransa danayi matuqar baci

ta tashi tana fadin nace bana sonsa banasonsa kai nakeso dole ne konasashi dole n.......ya dauke fuskarta da mari dai dai lokacin andy ya fito baiyi wata wata ba ya dauke jiyad da mari ransa a bace....

yace matar tawa,ashe bakada hankali ban sani ba, miye ruwanka da xaman mu ko miye naka dan ina mata aiki.

yace ba ruwana yaya amma inaso tasani ta kuma qara sani bana sonta,ni jiyad nace bana sonta tabarni tabarmin xuciya i hate herrrrrrr ya fada cikin tsawa kafin ya juya yabar falon ransa a bace.

Sadteeyesh

Hausa novel
[11:41am, 10/3/2016] Fatyma Zahra Too Nv: [2:14PM, 4/23/2016] pherty: [10:56AM, 4/17/2016] pherty: MATAR WAYE?

fertymerh xarah

       71 to 75

Haka rayuwa tacigaba da gudana tsakanin Andy da ba dadi, bayasamun kulawa kamar kowane mijin aure,

Tsakanin shi da ita sai gaisuwa shima idan yayi matane take amsawa a daqile kamar bataso

Ganin abubuwa xasuyi masa yawa ga yanayin aikinsa yasa ya nemo masu aikin girki duk da akwai maaikata a gidan.

Cikin lokaci qanqani Andy ya xama wani iri baya da nutsuwa koda yaushe cikin tunani gida da office bashida lokacin kansa sai nata burinsa kawai ya faranta mata,

Akwai wani lokaci yana tare da hjy take kallonsa da mamaki

Tace mohd duk ka canxa kaxama wani iri kadawo wani sukuku ba walwala kagayamin meke damunka....

Jiyad ya juyo yana kallonsa dai dai lokacin daya sunkuyarda kansa qasa
Yace ba komai hajiya,
Tace kowane mutum inyayi sabon aure ana ganin canji a garesa banda kai,kodai kanada matsala da matar kane,

Ya dago da sauri yana kallonta kafin
Yace hjy muna xaune lfy da ita...
Tace tor shikenan Allah ya kyauta ya yayema damuwar dake damunka,
Yace amin bayan ya kwanta a qafafunta ya lumshe idanuwansa cike da tunani iri iri.

Duk da halin sa ido ba halin jiyad bane amma wannan dai confrontation ne like a chase game da yakeson ganin ynda xai qare,

Dan haka yake ganin bai kamata ya kira sa idon nasa da sunan sa ido ba sai dai ya kirashi curiosity Wanda haline na kowane dan Adam akan abinda ya bashi mamaki tunda yasan matsalar yayan nasa.

Sai ya qara jin ya tsani fari'ah badan komai ba sai yanda takewa yayansa sai ya qudiri aniyar itama sai ya sauyata kamar ynda ta sauya yayanshi.

MATAR WAYE?Where stories live. Discover now