TAFIYA MAI NISA ✈
© Mamu
(Gajeren labari)
1⃣
Murna nake tayi "Ni" Mamu da zumud'i jin cewar an kira jirginmu, dai saurina na fada bayi na sakarwa kaina shower, jikina har b'ari yake yi na fito, na shirya.Na kinkime trolley dina zuwa boot, na dawo nace "maza-maza masu rakiya zuwa airport su fito."
Ai kuwa sai sisters dina suka fara min dariya, big Anty tace "A'ah su Mamu ko damuwa ba'ayi da rabuwa damu?"
Cikin shagwaba nace " Hajiya ku taso mu tafi kar jirgi ya barni, tun d'azu matar L/G R.O dinmu tace suna hajj camp."
Haba nan take Hajiya ta zanzamo sauran yan uwana muka fito compound din gidanmu, mota biyu muka yi COROLLA da BENZ.
Baki na har kunne yau gani za'ayi min rakiya zan tafi kasa mai tsarki."Hanya muka d'auka daga Arkilla har hajj camp, ban taba ganin nisan tafiyar ba irin ranar, cikin mota sai wayoyi nake k'arba ana yi min Allah ya tsare jin an kira jirginmu.
Babban Yayanmu yace "Mamu ke ko damuw ba kya yi ke kadai kika samu visa, duk cikin wadanda zaku tafi tare."
Na turo baki alamar shagwaba, nace "Ni ba ruwana ai na san mutane sosai wadanda zamu je tare dasu."
Hajiya tana dariya tace "karku takurawa Autata ku barta Allah ya nuna min, itama Allah ya nuna mata zata sauke farali."
Gaba daya aka sa dariya ana cewa "su Auta manya."
Nan take kaina ya fara fasuwa ganin mun shigo hajj camp, muka yi parking, muka firfito cikin motoci.
Babangida driver ya janyo trolley dina, muka zo wurin wata 'yar k'ofa, Yayanah yace "ki shiga ki karbo visarki da guzurinki, kuma daga nan ba zaki k'ara ganinmu ba."
Ai kuwa idanuna suka kawo ruwa amma na goge ban bari sun gani ba, don kar su yi min dariya, haka naja trolley dina na shiga.
Shiga ta wurin keda wuya, na fara zare ido ina kalle-kalle, don ni dai ban tab'a shigowa wurin ba, ina rako yan gidanmu amma ba'a bari mu shigo nan, ina nan tsaye naji ana kwalan kira a speaker "MARYAM ALKALI" da sauri naje wurin, naga an mik'o min passport dina tare da visata, akace naje na zauna.
Na zo na zauna kenan naga Mum Sultan ce matar R.O dinmu, muka zauna muna gaisawa, nan fa oga ya kirani a waya na koma gefe muna soyewa ( dayake baya gari).
Bayan na gama waya na dawo lokaci zuwa lokaci ina k'arba kiran yan uwa da abokan arziki, kowa da sak'on addu'arsa.
Muna can wurin siyan kwagiri (Lalita) Mum Sultan ce zata siya, don ni kam wata yar jaka gareni ta yan gayu mai zip masu yawa, aka fara raba guzuri, da gudu muka zo muka bi layi.
Bayan an bamu guzurinmu ne aka samu a layi, bus suka fara daukarmu sai airport.
A airport aka saukemu muka fara dirkowa daga cikin bus, da kyar na fito saboda k'afafuna sunyi tsami sakamakon trolley dina dana d'aura samansu, anan na k'ara ganin su Hajiyata da sauran yan uwana muka yi sallama ina hawaye, sai gargadi suke min irin yadda zan tafiyar da rayuwata a k'asa mai tsarki.
Layi aka samu aka fara mana screening, ana duba masu shiga kasa mai tsarki da kiyagun kwayoyi da sauransu. Ina kawowa a layi aka ce kawai na wuce ni matar oga ce, (kaji k'asarmu).
Wani faffadan fili aka kaimu, bamu yi minti talatin ba aka zo aka raba mana boarding pass dinmu, ina dubawa na kai zaune, ina salati, Mum Sultan tace " lafiya Mermue?"
Nace "Mum Sultan ki duba kiga tym din tashinmu sai 9:am na saf, yanzu fa sha biyu na dare, ina zamu kwana?"
Nan da nan idanuwanmu sun raina fata, na zaro wayata na kira Yayana nace masa "don Allah su tsayani mu koma gida sai 9 na safe jirginmu zai tashi."
Dariya yayi ta yi min, har raina ya fara b'aci " yace "Yarinya ai baki ga komai ba, ke da zaki je makka yanzu wannan abin zai tada miki hankali."
Hajiyata ce ta karb'i wayan tace "nayi hakuri, ai yanzu bani da wurin fitowa."
Nace "Toh" raina a jagule muka yi sallama na kashe wayar.
Na yiwa Mum Sultan bayani, wani wuri aka nuna mana a matsayin departure amma duk sauro ya cika sa fam, (abinka da airport din Nigeria) haka muka zauna akan kujeru na karfe, aka zo ana k'ara fadakar damu, yadda ake aikin hajji.
Daga baya aka bamu take away, wai! Tuni masu bacci sun wartsake aka fara brushi da cinyar kaza.Bayan wuri ya tsana da ciye-ciye aka fara sharar bacci, ni kam sai zare ido nake yi na kasa kwanciya saman k'arfen kujerar nan kamar yadda naga wasu sunyi, sai hango lallausan gadona nake yi wanda yasha shimfidu da filulluka, can Mum Sultan ta jamu muka yi masallaci, kowaccenmu janye da trolly dinta.
Sallama muka rafka muka cire slipers dinmu muka shige masallaci, tabarmi ne shimfide a ko'ina cikin masallacin, an zagayesa da yar gajeruwar gina, zubewa muka yi daya daga cikin tabarmin, Mum Sultan sai minsharinta naji, bayan na gama zare-zaren idona nima na dan kishingida, nan take bacci yayi gaba dani lokacin karfe 3 na dare.
Jin nayi ana tab'ani na mik'e da sauri, ina jin ana kiraye-kirayen sallah, brush dina na zara nayi bakin famfo da naga anata alwala, bayan nayi brush naje toilet amma duk ya b'aci haka na fito waje na dan sakaya, na rage mara.
Mun gama sallah can bacci ya dan fisgemu, can muka ji hayaniya a kanmu, muka farka, ni da Mum Sultan muna kalle-kalle, tsofaffi da yara gasu nan kala-kala, sai cima kake gani kala-kala, tuwo ne, shinkafa ce, koko ne wasu tea ko waina.
Can wata yar yarinya kamarmu ta matso kusa damu, dama Yar kaunyensu su Mum sultan ce, nan da nan muka saba, muka dinke.
An kiramu mun bi layi bus zasu daukemu zuwa cikin filin da zamu hau jirgi, sai ga mijin Mum Sultan ya kawo mana abin kari, tea da bread da waina, a tsaye muka karya cikin layi.
Fara lodamu aka yi cikin bus zuwa inda jirgi zai d'aukemu, bayan mun fito ni dai duk jikina bana jin dadinsa, saboda rashin wanka, sai body spray nake fesawa.
Can mun dad'e tsaye a layi, muka ji jiniyar jirginmu, misalin kafe 9:05, mutanen wurin muka hau sowa, bayan jirginmu ya huta muka fara shiga cikinsa.
Nan fa wasu tsoffi suka rude sai kuka suke yi, sai da aka rirrik'esu zuwa cikin jirgi, bayan mun zauna, jirgi ya gama lodi, hankalin Mum Sultan duk ya tashi wai bata tab'a shiga jirgi ba sai yau, ni kam dariya kawai nake masu ita da Hamida yar kauye.
Aka fara sanarwar kashe waya, bayan mun kashe wayoyinmu, aka fara nuna mana hanyoyin da idan jirgi zai fadi (crash) yadda zaka tsira da ranka, dama Ashe kusa da Exit door muke zaune, hohoho Mum Sultan har ta fara hawaye, ni kam ba aikin da nake yi sai dariya.
Jirginmu yana fara barin k'asa tsoffi suka fara ihu, suna cewa "Shehu Usmanu ka taimakemu."
Sai lissafo sunan 'ya'yansu suke yi suna cewa sun yafe masu cikin kuka.
Wani tangadi da jirgi yayi sai da Mum Sultan ta saki fitsari, kawai sai ruwa naga suna bi akan carpet din cikin jirgi. na zaro ido nace
"Mum Sultan lafiya? tace "tsoro." nace "ikon Allah."
Ina juyawa bayana naga wata Inna tayi jagwab da fitsari, nace "Inna akwai toilet fa a jirgi." tace "yo ni ba iska zai busar dashi ba, tunda gamu akansa."
Dariya kamar cikina zai fashe muke yi nida Hamida har da kwallarmu.
Masu karatu ku biyoni yanzu labari ya fara.
Mrs jabo