KAUYANCINMU

310 28 1
                                    

TAFIYA MAI NISA ✈

©Mamu

(Gajeran labari)

2⃣

Tafiyar awa d'aya muka yi a iska bacci ya kwashemu, shirkaf.
Bayan awa d'aya masu kawo abinci suka fara badawa, nan da nan sai motsin bakuna kake ji, anata brushi da naman kaza da shinkafa yar gwamnati taji wata miya baka k'irin.

Ni dai Mamu ruwan shayi na roki waiter ya kawo min, dama da biscuit da madara a cikin dan kwalin makolashi da aka bawa kowa, bayan am natsa da ciye-ciye kafin rabin sa'a, aka fara duruwa toilet, masu zawo da masu fitsari.
Ko kafin ajima toilet din jirgi duk sun baci.

Bayan wasu sa'o'i sun shud'e Allah ya saukemu lafiya a babban birnin Jidda. Lokacin 6 na yamma na birnin Jidda.

Zo kuga murna gani muke kamar gamu ga ka'aba.
Ashe bamu san da sauran tafiya a gabanmu ba.

Bayan mun gama shan wuyar bin dogon layin screening muka kai ga layi, Hamida yar lukuta wannan lokaci tsayuwar kirki kafafunta basa daukarta, sai wani dafani take nima ina Allah kamani.

Cikin wani daki na wasu mata duk wacce ta fito sai kaji tana Allah ya isa, checking akeyi ashe har cikin brezia, haka akayi mana muna ja masu tsinuwa a zuci.

Wani kayataccen balcony muka fito, ga masallaci ga toilet na maza da mata, ga wajen cin abinci. Bayan munyi salloli muka bi layin nuna ticket a baka abinci.

Shinkafar ba dadi salaf, kamar ansa Laila yin girkin dole. Haka muka zuba yaji akai muka kora da drink da ruwan yan kwalba.

Zaman jiran bus muka yi wacce zata kaimu Madinatul munawarra, da kyar muka ganta wajen goma na dare, kafin su gama karbar passport din kuwa muyi boarding to 12.

Tafia ake yi sai sharar bacci muke yi, titi san6al ga mota Ac, can muka ji dirin mota ta tsaya.
Kowa ya farka, bude idon tsoffin cikin motarmu sun ga haske fal ko'ina, kamar har yayi yawa ma, wuta masu kawowa da daukewa, gasu nan.
Kamar hadin baki naji suna jan tasbihi har wasu na rudewa.
"La'ila ha illaLLah, wa'ina ilaihir raji'un."
Allah ya kawo mu garin manzo, nan me masallacinsa?

Murza ido nayi na kara budesu, na gane gidan mai ne, zaa karawa motarmu gas, nan da nan ma fada masu.

Kamar zasu cinyeni danya suka karyatani, na ja bakina nayi shiru, ina daria kasa-kasa.

Jin driver ya cigaba da tuki yasa wadanda suka fara mikewa tsayi suka zauna dole, suna cewa "Ashe da gaskiyarki yar nan."

Tafiya tayi tafia, akazo wajen tsayawa a huta idan da mai cin abinci ya ci, kofar wani hadadden restaurant ne, driver ya shiga muna take masa baya.

Table ya ja ya zauna ya bada order, aka kawo mashi nan take, yan motanmu sai zuba ido suke yaushe zaa kawo masu nasu plates irin nashi, suka ji shiru.

Duk larabawan da suka rage abinci a plate sai ajiye masu a gabansu, gasu fa sun haye table d'ale2.
Can suka juyo suka ce Mmn sultan mu ba zaa bamu abincin ba, driver shi kadai ne zai ci, bayan an biyashi kuddin komai da komai.

Daria tasha kafin ta basu amsa daga inda muke a kwance saman wani lallausan carpet, tace masu " kowa shi zai siyawa kanshi plate, kuma 300 Riyals ne.
Nan take suka yi gum kuwa.

Wata balarabiya suka ga tayi alwala a toilet din restaurant ta tada sallah a masallaci, nan da nan suma suka hau yin sallah, wannan Karon Hamida tayi masu magana, tace "karfe sha biyu na dare yanzu, asuba bata yi ba."

K'asa suka buga wai haske ya gauraye gari har zasu yi lattin sallah.

Ido kawai muka zuba masu, daga baya muka yi mota, suma suka biyomu, driver yana dawowa aka cigaba da tafia, sai 4am muka shiga birnin Madina.

Wajen rabon daki muka ce ba zamu zauna da tsoffi ba, haka kuwa akayi, mu hudu duk yara aka bamu key, muka shige muka rufe muka fara bin layin wanka.

Mrs Jabo

TAFIYA MAI NISAWhere stories live. Discover now