TAFIYA MAI NISA ✈
© Mamu
(Gajeran labari)
7⃣
**
*makaranta* *wannan* *novel* *kuyi* *hakuri* *for* *the* *late* *update* *abubuwa* *ne* *suka* *min* *yawa.*
*thanks.***
Zaman dirshan muka yi ba shiri bayan mun mike daga faduwar da muka rafka, Allah ya tsaremu bakinmu bai fashe ba.
Hamida ce ta rike baki tana cewa "wai Allah na gode maka hakurin makkana bai fita ba."
Muna zaune a kasan mota ga wani zafi da take busowa amma sai da muka dara.
Bayan mun isa muzdalifa muka sha tafiya kafin mu samu space din zama, muna cikin tafiyar ne tsoffin gidanmu duk suka kulle hijabansu wuri daya don kar su rabu, wato mutane a wurin kamar filin kiyama.
Gashi kowa yasha fararen kaya.
Gani kawai muka yi Laila an wullata cikin wasu larabawa da suka yi group da dan kofin shayinsu suna kishingide, sai ga Laila a tsakiyarsu tana zare ido.
Mikewa tayi a guje larabawan suna Yalla-yalla ta zura da gudu, muka bi bayanta muna kiranta.
Zubewa muka yi wani dan wuri da muka samu da dan fili, wurin bai wuce cin mutum biyar ba, amma haka muka kwanta mun fi mu goma.
Kwance muke sai juye-juye muke yi, hakarkari duk sunyi ciwo, wurin tudu da gangare ne, gamu da tabarma a jaka amma ba wurin shinfidawa isasshe, mutane ne ko'ina kwance, wasu zaune.
Daga kan da zanyi naga ashe kanmu cikin kafafun maza yake, suna daga samanmu. Mu kuma muna daga kasa.
Ga mazan cikin haraminsu, iya kugu sai lullubi a kafada.Juyowa nayi nace "Hamida Allah yasa kar muyi gane-gane, kar fa mazan nan suyi bacci su bude kafafu su manta basu da wando."
Dariyar da muka saka ita ta saka Bizzy juyowa, wacce gata kwance ga wani namiji, suna facing din juna, kamar mata da miji, amma kowa al'amarin gabanshi kawai yake yi.
Karfe biyar na asuba muka yi jam'in sallah, bayan mun bi dogon layin toilet munyo al'wala.
Muna gama sallah muka hau kwashe yan tabarmi da suka samu wurin shinfidawa a daren jia, muka rataya jakunkunanmu bayan mun karya, muka dauki hanya sai zuwa wajen jifa.
Tafiya muke yi babu kama hannun yaro, duk wanda yaji wuya ya yarda yar jakarshi ta tarkace da tabarma, muna kai wajen hawa wasu steps aka fara cire takalmi ana watsarwa don wahala.
Tafiya muke yi ko'ina mutane ne, ko iska baka samu wadatacce, ga zafin rana, don ta fara budewa, ga tafiya, kafafuna ranar kamar ayi min na roba.
Duk inda muka ga masu watsa ruwa ko fanfon ruwan sanyi sai mun tsaya, muna isa kofar wurin jifa Mmn sultan ta zube.
Ganinta kawai muka yi idanunta na juyawa kamar carton an kwada masa fry pan, sai gata a kasa.
Ruwa aka dinga watsa mata wasu na mata firfita, da kyar ta dawo hayyacinta muka rikata muka karasa ciki.
Bayan mun gama jifa mun bi ta kofar baya, zamu fita sai ga tsohuwar nan data bace ta rasa hemarsu, tasha jalabiyar maza fara, a dole harami ta saka, tana ta wani irin wari saboda duk ta bata jallabiyar da zawo yellow shar.
Mrs jabo.