BACEWARMU

228 24 0
                                    

TAFIYA MAI NISA

© Mamu

(Gajeran labari)

3⃣

Kwana biyu muna zuwa masallacin Manzo (S.A.W) gwanin sha'awa, ana uku ne tsohuwar gidanmu d'aya ta bata cikin masallaci, akayi ta nemanta, da kyar aka sameta bayan tayi kwana biyu ciki.

Yau mun dawo masallaci bayan an gama sallar isha'i, bamu tsaya shagona ba wurin siyayya, ashe rabon muga abun daria, dama hawa na BIYU muke, elavator ta cika saboda kowa ya dawo masallaci, sai muka bi ta step, ai kuwa sai ga yan tsoffin gidanmu suna cire takalmi ana sakawa a hannu, suna rarrafe akan step.

Mmn sultan kamar zata kife don daria, nida Hamida har da hawaye,  Ummyn yusra kamar zata shide don daria.

Kamar nayi masu video naji.

Haka muka wucesu muka shige d'aki.

Wayewar gari muna ta sauri zamu je masallaci, Mmn sultan a hanya muna tafiya ta fara tumbling saman express, ga kiba mashaa Allah, sai mulmula take a titi, kamar bula a tire.

Bayan mun  tada ita da kyar, muna matse daria,  muka karasa masallaci.

Da yamma muka dawo yau bamu jira sallar isha ba, zamu zo gida muyi wanki, ashe rabon mu bace ne, muka bi wani get dabam, sai gamu a gidajen yan Côte divore , ranar mun sha bakar wuya.

Sai da muka kara komawa masallaci tukunna muka tuna ashe get dinda muke fita muyi siyayya duk yamma muka bi, bana zuwa gida ba.
Dole muka dubo number get din fitarmu  muka kara so gida muna jin kafa, don ni a hanya har zama nake yi yashe a kasa, idan na huta mu cigaba da tafia, a haka har muka karaso.

Bayan mun gama ziyarce-ziyarcen wurare masu albarka, muka kara kwana biyu muka sha siyayya, don ance kayan Madina sun fi kyau, muka daure kaya sai garin Makkah.

A mota wata ta kusa damu mai suna jam33lerty zawo ya kamata, daga mazan motar har matan ba wanda ya san me zai cewa balaraben driver ya tsaya zaa yi zawo da larabci.

Matar nan sai safa da marwa take a mota, hannu saman kai, tana zazzage-zazzagen jiki, alamar tana matse zawon ne.

Karshe mazan motar suka yanke shawara tazo sit dinmu dama mune a karshe wai tayi zawon a leda, muka ce sam ba zata cikamu da wari ba.

Mrs jabo

TAFIYA MAI NISAWhere stories live. Discover now