[9/26, 8:26 AM] Mamu:
TAFIYA MAI NISA
© Mamu
(Gajeran labari)
6⃣
"Yasar kashi Inna?" Nace cikin mamaki!
Amsa min tayi da "Zo muje ki ga."
Bin bayanta nayi har zuwa toilet.Tun kafin mu isa kofar toilet wari yayi min sallama, na toshe hancina muka shiga ciki.
Kashi ne dankam kamar ya fito waje yayi gudu.
Na juyo kamar zanyi amai nace "inna ba kwa yin flushing ne?"
Tace min "meye gloshi? Mu kam kowa zuwa kawai yake yi yayi bukatarshi, sai yanzu naga abun ya cika sai an yashe."
Kamar zanyi kuka nace "Inna wannan masan kana gama abinda kake yi sai ka danna nan, ruwa zasu zubo su wuce da kazantar."
Na k'arashe ina nuna mata doguwar igiyar da zasu ja kawai ruwa ya zubo.
Cikin rike baki tace "wai duk a makarantar bokon da kika yi aka koya maku?"
Dariya kawai nayi nace tayi flushing din na fito, don ji nake kamar yan hanjin cikina zasu fito waje idan na fara amai, amma bana son ta gane.
Da sauri ta biyoni bayan tayi flushing ya kai sau biyar sannan yayi, tace min "mu tafi dakinmu kin ji Mairo yar boko ki koyawa yan uwana yadda zasu yi, don ni ko na fada masu ba yadda zasu yi ba.
Ba don raina yaso ba nabi bayanta zuwa dakinsu, tun kafin mu karasa kofar dakin wani wari ke bugowa, da alama daga cikin dakinsu ne.
Haka na hakura muka shiga, Wai! Wari kala-kala, na naman kajin da suke shanyawa, wani ya bushe wani bai karasa bushewa ba, wai zasu zo dashi gida, gashi nan kowa da nashi shanya.
Ko da na ware idona a dakin su goma a ciki, gado biyar katifa 5 yashe a k'asa.
Bayan mun gama gaisawa cikin mamaki nace " ya haka? Dama ku goma aka bawa daki? Ai yayi maku kadan."
Amsa min suka yi da wai yan daki biyu ne suka hade daki daya, don zumunci.
Bayani nayi masu sunyi yawa ai, ko dan samun iska mai kyau, sannan nayi masu maganar flushing na fito a 360.
Hmmmm ranar nayi amai kamar ne, kai kazanta bata yi ba a rayuwa.
Ko abinci nake ci daga na tuna zan fara kwara amai.
Yau kam rigima ake tayi da tsoffin nan, anzo amsar kuddin hadaya, suka buga kafa a kasa suka ce kuddi zasu hada su saye rakumi suyi layya dashi, wai su nan wayo zasu yi kada mutum daya ta saye rago.
Sun dauka rakumi saukin kuddi ne dashi, suna lissafin iyakaci su bada riyal goma-goma.
Ko da suka ji kuddin rakumi akan dole suka bada kuddin ragona.Mun fara aiki cikin ikon Ubangiji, gamu a Minna cikin hemomi, muna kwankwance.
Wata tsohuwa sai bin hemomi take yi ta rasa nasu, daga zuwa toilet, da yar butarta a hannu.
Abinka da duk hemomin iri daya ne, farare.Haka ta hakura ta dawo ta kwanta a namu hema.
Tsohuwa ta cigaba da binmu, cikin dare motaci suka kwashemu sai cikin arfa, muka samu wata yar rumfa mai carpet muka baje.
Har mun fara bacci akazo aka tashemu, wai ashe rumfar matan manya ce, karshe sai wata yamutsatsiya muka kwanta.
Da safe bayan motoci sun kawo mana abun kari anata karba, muka karya muka yi wanka da ruwan banza kawai.
Muna nan zaune muna ta addu'o'i sai ga Hamida zata tsinke ganyen cikin arfa, da sauri muka hanata.
Wai zata yi sakacen baki tunda tayi brushi da kaza, nace da kin gane sakace kuwa, don sai kinyi azumi 3 ko kiyi yanka.
Muna gama sallar azahar da la'asar muka fara tsayuwar Arfa, kowannenmu ya rarrabu wannan karon ba wasa, addu'a sai wacce ka manta a ranar.
Bayan rana ta fadi muka ga tsoffin gidanmu suna ta shirga gudu, don bus-bus sun fara zuwa, muka tsaidasu da kyar, muna tambayarsu lafiya? wai ance da an masu magriba a cikin filin arfa to babu hajjinsu.
Sai da muka yi dariya tukunna muka masu bayani, ana so dai ka kwana musdalifa, ba'a son kowa ya kwana nan filin arfa.
Sannan fa hankalinsu ya kwanta, muka bi layi tare dasu.
Bayan motocinmu sun zo muka shiga, da ni dasu Mmn sultan ko wajen zama bamu samu ba a kujerun motar, haka muka yi tsaye a cikinta, driver yana jan mota sai gamu zube a kasa yashe kamar kayan wanki.