LARABCINMU

210 25 0
                                    

[9/21, 5:02 PM] Mamu:

TAFIYA MAI NISA

(Gajeran labari)

© Mamu

4⃣

Wurinmu tayo da yar ledarta,  tana kada jiki, ture-ture muka hau yi, muna rantsuwa bamu yadda ba.

Kallona tayi ganin kamar nafi fuskar tausayi tana cewa "wani tuwo naci da miyar taushe kadan, inaga shine ya bata min ciki."

Bata rai nayi na fuske, na daina kallonta, cikin murya kasa-kasa  nace "ina ganin yadda suke siyan kaza soyayya wurin takari suna razga, baa saba ci a gida ba, ba dole ciki ya lalace ba."

Hamida ta shike da dariya tace "Babu a house."

Ganin da gaske zata saki zawon nan a mota har ta fara tusa, hakan yasa wani cikin mazan motar yayi karfin halin ca6a larabci yadda balaraben nan zai gane ana so ya tsaya, ai kuwa nan take ya faka mota a gefen titi.

Da gudu jam33larh ta fita ta rabe gefe muna hangota ta zuba abunta ta dawo, sai kauce fuska muka yi, tana gamawa ko cikin dustbin bata zuba ledar ba, ta bar ta nan yashe a titi zawon ya zube akan kwalta, ta dawo mota, muka cigaba da tafia.

Bayan mun tsaya inda zamu yi wankan shiga Makka mu dauki niyya, muka fara sabuwar daria, irin yadda maza suka daura harami, gefe daya  matan labarawa sai kallonmu suke basu ga mun tsane gashin kanmu ba da hand dryer, basu san anty gwuidus muke ba.

Shigarmu Makka ke da wuya aka bamu masauki, hura da tuwo aka yi mana lale dasu, bayan mun ajiye kayanmu mun ci abinci muka kama hanyar masallaci.

Tafiya muke ta sha, muna hango agogon nan na kusa da masallaci, yau muke jira mu ganmu masallaci gobe ne shiru.
Da kyar muka isa misalin 1 na dare, gamu ga ka'aba.

Allah Akbar nan take ni da Mmn sultan muka fashe da kuka, Hamida ma sai matsar kwalla take yi.
Muna kuka muna yiwa Allah kirari, hade da gode masa, da ya bamu ikon ziyartar dakinsa mai girma.

Lalila muka jiyo a bayanmu tana fadin Allah na gode maka daka nuna min dakinka, banyi irin na wata dana ji ance tazo ka'aba amma bata ganta ba.

Sai da ta bamu daria, muka dara kuwa.

Bayan mun gama Umra muka dawo cikin masallaci muka yi sallar asuba, muka fara neman hanyar fita, amma muka rasa.

Da kyar muka gane ga ciwon kafafun Safa da Marwa, da kyar muka isa gida, sai wanka muka fadi sai bacci.

Haka muka dinga zuwa masallaci kullum acan muke wuni, sau biyu muke d'awafi safe da yamma, yau da yamma muna tsakiya da d'awafi mun kawo dai-dai kofar nan ta ka'aba inda ake daga hannu ayi kabbara, wani basamuden balarabi yana mayar da hannunsa sai gani cikin hammatarsa ya matse, gashi cunkus ga zufa, da kyar na samu na fito idona duk a waje, na kusa mutuwa.

Ranar ba bakin daria, sai su Mmn sultan ne suka yi min, suma kasa-kasa suka yi, don kar inji, basu san na ganso ba.

Yau kam mun tashi da shiryen-shiryen fara aikin hajji, anata sanarwa abubuwan daya kamata mahajjaci yayi, ciki kuwa har da shaving da yanke farce, saboda duk zaa yi hadaya (layya).

Wasu yan kusa da dakinmu muka sha dariyarsu, wai tun lokacin da gashi ya fara fito masu a hammata basu taba yin aski ba.

Mrs Jabo

TAFIYA MAI NISAحيث تعيش القصص. اكتشف الآن