[Sat, September 29, 2018]
TAFIYA MAI NISA✈
© Mamu
(Gajeran labari)
8⃣
"Inna lafiya?" Queen Mimi ta fada tana karasawa kusa ga tsohuwar, mu kam kara sauri ma muka yi don mu ragewa kanmu wari, gefe kadan muka tsaya.
Sauri kawai take yi tana tafiya tsohuwar nan, ba takalmi a kafarta, bakinta yayi fari fat, alamar kishirwa, ga zawon nan da tayi a riga.
Queen mika mata robar ruwa tayi tace tasha, aikuwa tsohuwa nan take ta shanye tas tana sauke ajiyar zuciya.
Sai sannan bakinta ya bude, muma muka dan matso kusa da ita muna toshe hanci, tace mana "ina tsakiyar tafiya zawon nan ya kamani, ba bayi ba wajen zagayawa har ya fito ya bata min jiki."
Tausayi ta bamu sosai, muna kaiwa wajen wani famfo muka ta watsa mata ruwa, zawon ya fita amma wari yana nan, sannan muka yi gaba bayan mun hadata da wasu tsofaffi yan uwanta.
Tafiya muke tayi mun gaji likis, ni dai sai jan kafa nake yi, dama na taba jin ciwo a kafar yau kam ya tashi ya dawo sabo.
Hamida mai duwawu kamar an saka mata pillows a baya sai kara turosu take yi ta baya, ni har gani nayi kamar sun kara hurowa yau.
Gashi mun bace, duk inda muka hango masu symbol mai state din Nigeria sai mu bisu, amma sai muga ba hanyarmu bane, mu kara dawowa.
Sai larabawa ke ta duba mana map wajen da hemarmu take amma mun kasa ganewa, da kyar wajejen 3 na yamma muka ga wata mota na raba abinci, haka muka samu muka ci a hanya muka sha ruwa a famfo masu sanyi muka ci gaba da tafiya.
Ranar kam kafafunmu ko wukake ne sun yi kaifi haka, tun 5 na asuba muna tafia har 4 na yamma, da kyar muka kawo gida, kowa yana jan kafa.
Laila a gwale take tafiya, cinyoyinta sun goge.Muna shigowa kitchen din hemarmu suna raba abinci, kallo ban iya masu ba, na wuce na zube a katifata, ba wanka ba cin abinci ba sallah sai bacci.
Mmn sultan da bata hakurin yunwa itace taje ta amso mana abinci, suka tasheni muka ci, muka dan watsa ruwa muka yi sallar azahar da la'asar.
Hamida ta kalleni tace "Kinga wai su Bizzy sun wuce makka suyi dawafil ifada sannan su kara dawowa kasa."
Ido na zaro nace "me? Mu kam sai dai idan mun koma tunda anyi mana rangwame zaka iya bari."
Kara komawa nayi na lafe ina kallon yadda kafana ya kumbura, na juyo nace "Hamida ya duwawun da suka kumbura, sun sace?"
Jakarta ta wurgo min, na kauce ina daria, tare dasu Mmn sultan suna nuna yadda take tafiya.
Bayan mun gama jifa ta kwana uku, wacce ta karshe ni sai yi min akayi, don ta biyu ma naje ciwon kirji ya sarkeni kamar zan fadi a hanya, da akwai wheel chair ciki za'a daurani.
Muka dawo cikin garin makka.
Bayan mun huta muka je masallaci muka yi dawafi.Washe gari muna zaune a daki, sai ga Mmn sultan tayo uban kunshi ta shigo dashi na gumama, ita dama kullum cikin siyan gumama take, gaba daya kayanta sune, yaranta kawai ta siyawa sabbin kaya, wato su Sultan.
Amma ko mijinta da yan uwa da sauran kawayen arziki duk gumama ce tsarabarsu, kallonta kawai muke yi, yadda ta tara tulin kayan, jakarta da wuya idan zata dauka.
Kwanakin nan ba abinda ya rage mana sai dawafin ban kwana, aikinmu yanzu zuwa shagona da mall-mall, idan mun dawo masallaci, wani mall da muka je mun dauka mai motar guduwa ma zaiyi damu, saboda nisanshi, har masu saurin kuka a motar sun fara, Laila itace zaune a gaban mota, Ni da Hamida Maman Sultan da Mimi muna zaune a baya, tunawa nayi ana yawan yiwa yan Nigeria fyade nan take nima na fashe da kuka.
Mai mota ina tambayarshi a ina muke cikin harshen turanci, shi kuma sai fada min sunanshi yake a cikin harshen larabci.
Tsayuwarshi a kofar wani hadadden Mall yasa hankalinmu ya kwanta, muka fice aguje, har muna ture juna.
*Bayan* *kwana* *biyu*
Muna zaune Hamida tace zamu je Jidda siyayya, muna nan zaune muna tsara yadda za'a yi, sai ga Mrs zayyan ta shigo cikin dakinmu tana kuka, mikewa muka yi da sauri muna tambayarta dalili.
Cikin kuka tace mota ta hau zata je harami ganin rana ta bude, zafi yayi yawa, sai ta tari taxi ta hau.
Mai taxi bai tsaya ko'ina da ita ba sai cikin duwatsu bakin wata gada, ya kwace mata duk guzurinta yayi wulli da ita bakin titi.
*mu* *hadu* *a* *last* *page* in shaa Allah.