YAR BOKO

187 17 0
                                    

[9/24, 10:31 AM] Mamu: TAFIYA MAI NISA

(Gajeran labari)

© Mamu

5⃣

Matsawa nayi kusa gareta nace, "Baiwar Allah shin da gaske kike ko wasa, baki taba aski ba?"
Cikin washe baki tace "Eh ban san anayi ba."

Nace "meye sunanki?"

Tace "Bizzy." Tana ta daria, cikin raina nace kaico!

Bayan mun gama abinda zamu yi muka fita waje don samun abinda zamu ci, bayan mun siyu mun dawo mun ci, muka yi shirin zuwa masallaci.

Yau kam masallaci ya cika damkam, duk yan garuruwan kusa sun zo, tunda an kusa fara aiki, yan Indonesia muka hadu dasu cikin d'awafi, sun daura wani kyalle gaba dayansu basa rabuwa da juna, haka muka dinga kaure-kaure dasu, saura round daya mu gama d'awafi, Mrs zayyan tace kashi take ji.

Riketa muka yi muka hanata fita, sai zarin fita take wai ya kusa fitowa.
Da kyar muka karasa muka fito tare da ita, tana ta gudu tana tusa, haka muka bi bayanta muna dariya.

Gashi bata iya hawa step mai tafiya wai tsoronshi take yi, tunda taga wata katuwar mata ta hau jere ya kwasheta ta fada min ta tausheni, duk ya yankeni a kafa, Allah yasa ma da safa a kafafuna.

Tun daga lokacin take tsoron hawa, sai  dai tabi step, yau kam super kawai muka ga tayi ta dale step yana tafiya da ita zii zuwa kasa (underground) inda toilet suke.

Bayan mun dawo gida da dare, ina shiga toilet na samesa gashi ne ko'ina kace-kace, yau mutanen gidanmu sunyi aski kenan.
Na fada a raina.

Bayan mun natsa muka fita shagona sayayyar tsaraba, wani shagon balarabe muka je muna cinikin wata jalabiya ta mata mai kyau, balaraben yana ganin Mmn sultan yace ita zai saidawa itace matar Alhaji tunda tana da kiba.

Ni kuma Mamu wai bani da kuddi saboda ni ba shirgegiya bace, ranar naga ikon God.
Daga karshe ma kasa siya tayi nice na siya, aikuwa ya dinga bani hakuri.

Muna dawowa daki muka samu Queen Mimi Hajajju sai mulmula take a gado, tana wani gantsare-gantsare, na karasa gabanta nace

"kawata lafiya kike yau?"

Bata kula mu ba sai wayarta take dannawa, alamar wani take kira a waya.

Tsaki ta ja ta ajiye wayar, wuri na samu na zauna muna kallonta ni dasu Mmn sultan.

Ganin ta zaro dan kanfai dinta (pant) tayi wulli dashi tana fashewa da kuka muka rafka salati.

Hamida ta matsa gaban gadonta tana cewa "fitsari kika yi a pant?"

Cikin jin haushi tace ba oga bane (da yake tare da mijinta suka je) yace min na shirya yana zuwa amma wai ya fita bana kuma samun shi a waya.

Wayyo ranar munyi daria kamar zamu yi hauka, don tsonaka ranar tasha daga ita har mijinta.

Karshe Mimi kunyar kanta ta dawo tana ji.

Wata tsohuwa ce tazo tana kwankwasa mana kofar daki, da yake rufewa muke yi, har key muke murdawa.

Nice na bude mata, tace "Maryam yar boko (sunan da suke kirana dashi kenan. lol) zo ki duba mana bayinmu ya cika kashi baya wucewa, inaga sai kin turance mana ma'aikatan otel dinnan sun nemo masu yasar kashi."

Mrs Jabo🤪

TAFIYA MAI NISAWhere stories live. Discover now