Babi na goma sha biyar

11.9K 911 62
                                    

*Bismillahir rahmanir rahim*

*wama tadri nafsun maza taksibu gada*

           Kwanaki biyun da yayi a dakin sumayyan shi kamsa ji yake ya zama tamkar ango,zuciyoyin su fes,duk wani buduri da fa'izan keyi basu san da shi ba,soyayyarsu kawai ta ishesu rayuwa.

            Cikin kwanakin da suka biyo baya damina ta shigo,wanda hakan shi yayi sanadiyyar zubewar ginin maqotan yaya yahanasu ya fadowa gidansu har ya janyo rushewar wani bangare na gidan,hakan ya sanya mukhtar yace su baro gidansh su dawo gidansa don a samu sararin gyaran gidan nasu,ko bayan rasuwar mai gidan anty yahanasu kusan shine jigo dake d'awainiya wa su yaya yahanasun.

           Qarfe biyu na azahar suka iso gidan tare da yaranta biyu jamila da sayyada,sumayya na tsakar gida a lokacin tana wankin kayanta,da fara'arta ta taso tana musu sannu da zuwa tare da qoqarin karbar jakar hannun yaya yahansun bayan yara sun gama shigewa da sauran kayayyakin nasu d'akin fa'iza,kaucewa tayi gami da jifanta sa wani kallo tana fadin
"Kada ki kuskura ki taba min jaka,matsa da Allah ki bawa mutane guri" ta fada tana wuceta sauran yaran suka mara mata baya,a salube ta koma kan wankinta taci gaba da yi har ta kammala tana jiyo shewarsu cikin dakin fa'izan kai kace yaya yahanasun sa'arta ce,ya tabbatar cewa da ita ke shewa haka da yaya yahanasun sai ace bata da mutunci bata da kunya,amma ga fa'iza na faman shewa da qyaqyatawa gabanta,matar da ko sau daya sumayyan bata iya hada idanu da ita,biyayya take mata tamkar uwar mijinta haka ta dauketa sakamakon ganin irin girman matsayin da take da shi gun mukhtar.

          Tana kammala shanya kayan ta shige wanka saboda tana so taje kitso sakamakon ita ke da girki gobe,har ta fito ta gama shiryawa ko alamun dora abinci babu gun fa'iza,itama bata damu ba sai ta hada shayi kawai ta sha tayi ficewarta ta barsu.

             Qarfe biyar ta dawo gidan saboda layi da ta taras a gidan kitson,tun daga qofar gida ta soma jin muryar fa'iza cikin balbalin bala'i,ta kutsa kai cikin gidan cikin mamakin ita da wa,dai dai lokacin da fa'izar ke fadin
"Yo da kika damen da zancan ciki laifin uban waye mayun 'ya'ya?,qanin naki yayi min cikin mana ya gani idan ban dauka ba,wata uwar yake yimin idan kwana na ne banda kwanciya da zaki uzzura min,to wallahi babu ma mai kwanarmin cikin daki balle ya sanya min ido,dama daki ba daki ba ya zuciyar talaka,sai ku nemi gun kwana" ta fada tana komawa cikin dakin tare da banko labulenta.

           Idanu sumayya tabi tsakar gidan nasu da shi,ko ina kaya ne na yaya yahanasun a barbaje a qasa,gaban sumayyan ya fadi,jikinta yayi sanyi,ta qarasa tsakar gidan,hannu ta sanya tana tattare kayan nasu waje daya,tsawa yaya yahanasun ta daka mata
"Kada ki sake taba mana kaya shegiya munafuka 'yar gidan malamai,to wallahi bari na gaya miki idan ma shiga tsakaninmu kikayi da fa'iza kinyi kadan,hakan da takeyi bazai tunzura zuciyata tunda nasan ba cikin hayyacinta take ba,ke sayyada maza ku hade mana kayan gefe guda mu jira shi muntarin ya dawo" sororo tayi tana dubanta
"Daina kallo na mayya,li'ilafi quraishi,ni baki isa ki cinyeni ba" sai ta kauda kai ta wuce kai tsaye dakinta ta bude ta shige.

            Bata sake fitowa yayi zamanta cikin dakin,sai ta qirqiro wasu 'yan qananun ayyaukan ma cikin dakin nata don kawar da duk wani tunani da zai dameta,tana aikin tana ambatar hasbunallahu wa ni'imal wakil,allahumk finihim bima shi'ita,hakan ba qaramin taimaka mata yayi ba,sai ya tafiyar da lokacinta cikin sauqi har aka kira sallar magariba,ta miqe ta fito domin daura alwala,suna zaune gefe daya na tsakar gidan da qullin kayansu,sosai har cikin zuciyarta taji babu dadi,bai kamata mukhyar yazo ya taras da su haka ba,ko babu komai 'yan uwansa ne jininsa ne,kuma tayi imami cewa idan wani nata ne shima mukhtar din ba zaya wofantar da su haka ba,ta danne zuciyarta ta qarasa gurinsu,cikim sanyin murya tace
"Don Allah yaya ki shigi dakina,ko da ba zaki zauna din ba ki shigo idan yaso idan ya mukhtar din ya dawo sai asan yadda za'ayi din" wani kallon banza ta bita da shi
"Ke wallahi ki fita a idona,wai ke wacce iriyar mayatacciya ce ne,nace bazan shiga ba dole ne,to bari kiji,idan ma wani laqani aka baki na sai na shiga sannan zaki samu galaba a kaina to wallahi ki gayawa malaminki kunyi qarya kun kwana da yunwa" jikinta sai yayi sanyi ta kasa tafiya,zuciyarta na gaya mata basu zama masu kyautawa mukhtar ba indai yazo ya tadda jininsa a wulaqance,duk da tarin izgilu cin fuska da cin mutunci da ita yaya yahanasun ke jifanta da shi,ba ita take dubawa karamcin mukhtar take dubawa.

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now