Babi na casa'in da shida

18.8K 1.5K 305
                                    

*Bismillahir rahmanir rahim*

*wata rana annabi S A W yazo wucewa ta wasu qaburbura guda biyu,sai yace da sahabbansa
"haqiqa(mutanen dake cikin kabarin) ana musu azaba,ba kuma wani babban abu bane yasa ake musu azaba saidai(ma'abocin kabari daya)ya kasance baya suturtuwa daga fitsari,amma dayan SHI KUMA YA KASANCE YANA YADA ANNAMIMANCI"*

*sadaqa rasulul karim*

*qalubale ga munafukai,qalubale ga masu daukan zantukan wancan bangare su kaiwa wancan,su dauki naka su kai wa wani bangare,qalubale ga masu haddasa husuma,masu qiren qarya don su haddasa husuma da rigima tsakanin mutane,qalubale a garesu baki daya,GA MAKOMARKU NAN,RUWANKU KU GYARA RUWANKU KUCI GABA*

*FITINA AKWANCE TAKE ALLAH YA LA'ANCI MAI TADA TA*

*FADA CE TA MA'AIKI*

*ABINDA KUKA SHIRYA BAI YIWU BA,SAIKU SAKE SABON SHIRI,MAIMAKON SHARRI DA KUKA SO QULLAWA SAI ALLAH YA JUYA ABIN YA ZAME MANA ALKHAIRI,GODIYA TA TABBATA GA ALLAH*

*ubangiji na cewa*

*YAKU WADANDA KUKA BADA GASKIYA DA ALLAH,IDAN FASIQI YAZO MUKU DA LABARI,TO KUYI BINCIKE KADA KU AFKAWA WASU MUTANE CIKIN JAHILCI/RASHIN SANI,SAI KU WAYI GARI KUNA MASU NADAMA AKAN ABINDA KUKA AIKATA*

*HAQIQA DUK WANDA YAYI AIKI DA UMARNIN UBANGIJI BA ZAIYI DANA SANI BA,MUN GODEWA ALLAH DAYA SA MUKA KASANCE CIKIN MASU IMANI*

*ALLAH KA SHIGA TSAKANINMU DA SU,KA FI KOWA SANIN BAMA NUFIN KOWA DA SHARRI,TSARKAKE ZUCIYARKA SAI ALLAH YA KUBUTAR DA KAI*

*muna muku fata Allah ya shiryeku,don wannan mummunan ciwo ne kuke dauke da shi,ciwon dake iya dawwamar da bawa cikin azabar kabari*

*ALHAMDULILLAH*
_______________________________________

           Shiru ne ya ratsa dakin,bata sake cewa komai ba,kamar yadda shima bai sake cewa komai ba har ya gama mata gyaran ya hade mata shi waje guda,tana kwance lamo tunani kala kala cikin zuciyarta,har ga Allah bata marmarin binsa,ba don komai ba saboda ta horu cikin abdallah,tana tsoron sake faruwar wani abun,su da zasu tafi can wata qasa wata uwa duniya,wazai tallafeta idan wani abu ya sameta wanda bata fatanshi?,shi da ba zama yake ba,ko yaushe aiki aiki?.

         Washegari ya sake birkice mata,sanda suka je gaida su baba da ummee,ya sanar musu komawarsu ranar lahadi kwanaki uku masu zuwa,ita dinma ummen so take ya barta nan cikin ya sake qwari tukunna,baya ga haka tana tunanin haukar su'adah kada ta yiwa sumayya saukarsa,tun sanda ta yanki almustaphan take jinjina batun,dannan daga bisani itama tazo raiwa kanta illa,to wayr ba zata iya yiwa ba kuma?,hakan ya sanya kamar tasan zaizo da zancan tafiya ta gayawa baba shawararta,yayi na'am da hakan,don shi kansa tsarin yayi masa,ya wuce da su'ad din ya bar sumayyan bayan wata biyu yazo ua dauketa.

       Sanda ummee ke rattabo masa bayanin kanshi na wasa,kusan tare suka daga kansu gaban sumayya na faduwa,kada fa yayi zaton qararshi ta kawo kan ba zata bishi ba?,da hanzari ya daga kanshi yana duban ummee,a hankali ya motsa bakinshi
"Amma ummee nan da can din duka daya ne ai,zata samu dukkan kulawar data dace"
"Ba daya bane almustapha,ka barta nan ta sake koyon yadda zata kula da kanta,a can fa kada ka manta bata da kowa..."
"Amma ummee tana da ni" ya amsa ummin bako kunyar nan fuskarshi,hankalinshi a tashe yake,kawai yadda zai tafi ya barta yake kwatantawa,ji yake sam ba mai yiwuwa bane
"Munsan da kai din ai,awa nawa kake zama a can din....kaga...magana ta wuce tashi ka tafi,kada ayi visa da ita" a hankali ya miqe bai ko dubi sashen da take ba,duba daya zaka yiwa fuskanshi kasan yana cin fushi,ya juya a nutse ya ficea binshi,binshi tayi da idanuwa kamar zata sanya kuka,bacin ran data gani kawai saman fuskarshi ya daga hankalinta
"Amirah" taji ummi na kiran sunanta,da sauri ta maida hankalita wajen tana amsawa
"Kada ki damu kinji,rabu da shi,ciwon 'ya mace na 'ya maca ne,kina wannan halin na yau lafiya gobe babu ta yaya zaki tafi inda baki da mataimaki sai Allah,qyaleshi ko yayi fushi zaya sauko,ni nasan bazai iya fushi dake ba" maganan ummin ta qarshe ta bawa sumayya kunya,sai tayi qas da kanta tana amsawa da to,duk da haka zuciyarta bata nutsu ba.

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now