Babi na tamanin da takwas

21.6K 1.6K 729
                                    

*Bismillahir rahmanir rahim*
______________________________________

        Sallar asuba ce ta farkar da iya,sai data kammala sallar sannan ta sauko qasa ta dawo wajensu humaida,tsokanarta suka dinga yi kan ina ta gudu?,bayan sunsan oga baya nan,murmushi kawai tayi tana tuna abinda ya faru daren jiyan,mamakin kanta ta dinga yi,batasan me ya sameta haka ba.

        Bata damu tayi wanka tunda wuri ba,zani ta daura saman kayan baccinta ta zura hijabi suka fice tare da su humaida ta gaida mutanen gidan,hada hada tayi yawa a gidan kasancewar gobe daurin aure,babu abinda zasuyi cikin gidan kasancewar komai na gidan da za'a gabatar akwai ma'aikata wadanda zasuyi,qarfe goma ta koma bangaren nata,ta kintsa ko ina,saiga sallamar mai kitso da anty dije ta gaya mata zata turo mata ita,babu bata lokaci ta fara mata,'yar maiduguri ce,ba qaramin iya kitso Allah ya hore mata ba,ga sauri a wajenta,cikin awa biyu ta gaka yarfa mata shi wanda ya zauna a kanta kamar an saqa shi,baki daya jelar ta kwanta gadon bayanta,rabon da tayi kitso irin haka har ta manta,sannan kai tsaye ta wuce kitchen dinta,samun kanta tayi da tunanin me zata tana dar masa wanda zaya burgeshi,murmushi ta saki sanda ta gama wassafa mai zata dafa sannan ta hau aiki.

       A wanni biyu kacal ta kammala,abinci iri biyu tayi,daya na baba ne daya na almustapha,tuwon alkama ta yiwa baban miyar karkashi wanda ya tuqo sosai yana santsi,dakinta ta koma ta sheqa wanka sannan ta fito tayi sallar azahar,tana shirin fara shiryawa ta jiyo shigowarsu amira,saukowa tayi jin amiran ma qwala mata kira
"Wallahi tunda na shigi nake jin qanshi iri daban daban,me kika girka ne haka?"
"Zaki ci?"
"Na waye?"
"Yayanki mana" ta fada tana juya ido,baki amiran ta rufe
"Wallahi duk maitata na haqura,wannan sanwa tafi qarfina" dariya sumayyan ta saka ta haura sama tana fadin ina zuwa,komawa tayi ta shirya cikin kwalliyar atamfa peach ce da adon yellow,fitted riga da skert wanda aka yi masa wata iriyar wrapper,ta zauna ta tsara daurin dankwali tamkar head din amare ya zauna dam a kanta,cas cas kayan suka mata kamar a jikinta aka dinka,ta bi jikinta da turate ta feshe shi sannan ta sauko,babu wanda bai tanka adon nata ba,har suka sanyata dariya.

        Har misalin hudu da rabi na rana hira sosai suke wadda ta dauki dadi matuqa,ta sake a cikinsu ana kwasar cafta,turo qofar falon da akayi shi ya maida hankalinsu wajen,almustapha ne,sanye da straight leg da longsleeve shirt,qafanshi snickers ne baqi,idanunshi saye da glass mai haske wanda kana hango qwayan idanunshi,hannunshi soke a aljihunsa kafadarsa rataye da jaka,tuni shiru ya ratsa falon kowa ya kama bakinsa,wadanda suka cire mayafi suka fara lalubarsa suna yafawa,tunda ya shigo idanunshi na bisa kanta,cikin izza yake takowa har zuwa tsakiyan falon,baki daya suka hau gaidashi,amsawa daya kacal yayi musu baki daya ya haye saman,tsam ta miqe tana fadin
"Ina zuwa"
"A'ah madam saidai mun ganki" inji humaida tana qyaqyata dariya,harararta sumayya tayi saboda shirin bata kunya da takeyi ta juya ta haye saman.

        Bakin qofar ta tsaya gabanta na duka,wani farinciki taji na mamayarta,cikin zumudi da son basarwa ta tura qofar dakin ta shiga,yana tsaye ya baiwa qofa baya,ko takalminsa bai cire ba bare a kai ga zama,waiwayowa yayi baki dayansa ya motsa bakinsa yana amsa sallamarta,idanunsa duka suna kanta,wani abu yaji na ratsashi,kyawun da yaga tayi masa ba mai misaltuwa bane tun daga qafafunta da yasha lalle ja da baqi ya qawata qafar ya bita da kallo ya dire a kafadarta wanda jelar kitsonta ta sauka,takowa yayi a hankali kamar mai sanda ya tsaya gan da ita,wanda tsaiwar baida maraba da runguma,tana niyyar bude baki ya rigata
"Kinsan zan dawo kika tara min wadancan?,sauka ki sallame su idan baso kike ayi abun kunya a gabansu,ke zaki ji ba dadi don na fuskanci kunyarki tayi yawa ni ko a jikina" daga kai tayi ta dubeshi,sai ya kashe mata ido daya,da sauri ta dauke kan ta ta juya da hanzarinta,a iya zamansu kadai ta soma fuskantar sa,ta soma gane sauyawar yanayiyyika tattare da shi,fargabarta daya me zata gaya musu?,zata ce su fita su bata waje?,riqota taji yayi,ta sake juyowa suka hada idanu
"Kada ki jima,kizo ki shiryani kayan jikina sun dameni" ya fada a wami shagwabe,wata bahaguwar kunya ta mamayeta,saita qara wuta zata fice kamar zata hantsila,haka ta dinga sauka har ta kai qasan.

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now