*wa tawakkal alal hayyul lazi la yamutu wasabbih bi hamdih*
_kayi tawakkali ka dogara da rayyayyen(Allah S W T)da baya mutuwa,kayi tasbihi/ka tsarkakeshi ka kuma gode masa_
Goguwar dawowarta sumayyan da taji ya sanyata daga kai ta bita da ido har ta shige dakinta.
Cikin mintinan da basu wuce biyu sumayyan ta fara jiyo qauri wanda gake da alama da wani abu aka sanya cikim garwashi,data luta sosai sai ta fuskanci daga bangaren zainab ke fitowa,mai da kanta tayi taci gaba da kallonta,cikin sakanmi qaurin ya buwayeta,hakan ya sanya ta koma dakinta ta dauko burner da turaren wuta ta fito falon wanda hakan yayi dai dai da sake ficewar fa'izan zuwa harabar gidan,jikin socket din dake daura da kayan kallon ta jona ta cikata da turaren wuta,mintina qalilan ya danne qaurin ya koma qamshi.
Tana zaune taji bude get din gidan da qarar motar mukhtar din,wanda hakan ke alamta dawowarsa,sai ta miqe ta koma daki ta sake feshe jikinta da turare sanna ta nufo harabar gidan.
Turus tayi ganin zainab gefan mukhtar tamkar zata shige jikinsa tana dubansa,hannunsa riqe da cup wanda ta cika masa da zobo wanda tuni ya fara kwankwada,yi tayi kamar ta juya saboda takaici sai kuna taga sam hakan baiyi tsari ba,zai kuma faranta ran zainab har taci karenta babu babbaka tunda ta riga da taga tsaiwarta.
Fuskarta ta fadada da fara'a,sannu a hankai ta soma takowa gun wanda takalmin qafarta duj da plate ne ya dinga bada sauti,hakan shi ya janye hankalin mukhtar ya zuba mata ido,ta masa kyau sosai,ji yake kamar ya tafi ya sureta ya daga sama yadfa suka saba,yau ta sauya masa sosai sumayyan,da wannan tunanin ta qaraso inda suke ta tsaya gabansa tana jifansa da murmushi,so yake take sumayyata kinyi kyau,so yake ya yaba mata,amma wani dunqulallen abun ya danne zuciyarsa,ya sake duban qwayar idanunta sai yaji wani bacin rai ya kamashi,murmushin da yakeson maida mata sai ya musanyashi da hade fusjarsa tsaf wanda hakan ya baiwa sumayyan mamaki,saidai duk da haka bata karaya ba ta miqa hannu ta amshi jakarsa tana masa sannu da zuwa.
Bai amsa ba don ji yayi ya gaza amsawar
"Wash" zainab ta fada wanda shi ya sanya su duja suka dubeta,baikai ga tambaya ba ta dora da nata jawabin
"Ka gani ko mukhtar,kaga abinda nake gaya maka ko?,yanzu fisabilillahi duk fadin gurin nan bai isheta ba sai ta takani saboda tsabar raini?" Mamaki fal zuciyar sumayya take dubanta,ya Allahu,nata salon kenan?matar da tazarar dake tsakaninsu ya isa tiqa tiqan mata biyu su tsaya shibe zata ce har ta taka ta?,tamkar dama neman abun fadan yake ya sake tunzura yana ji ana azqlzalar zuciyarsa,juyawa yayi yana jifan sumayyan da wani irin kallo
"Halayyar banzan da kike son koya kenan ko sumayya?,halayyar da ban sanki da ita ba?,to bari kiji ni bazan lamunta ba,bana son tashin hankali kin sani,har sau yaushe zan huta daga dawowata ko iskar gidan ban gama shaqa ba daga shigowarki zaki tada mana fitina?,to ki shiga hankalinki da ni idan ba haka ba zanyi mugun saba miki", bata data cewa,to me zata fada ma tunda ya riga ya yarda ya hau kai kuma ya zauna?,bata baki ne kawai tsayawa kare kai,saboda haka aladabce tace
" bansan na taka ta ba in sha Allah hakan bazai sake faruwa ba kayi haquri ya mukhtar"sai da yaja fasali sannan yace
"Shikenan ta wuce"
"Au ni ba zaka ce ma ta ban haquri ba shikenan na gane matsayina wallahi" ta fada a zafafe tana fashewa da kukan kirsa sannan ta kwasa tayi cikin gidan da sauri,don sosai ta shaqa ba haka taso ya kasance ba,so tayi cikin biyu ayi daya,imma yace sumayyan ta durqusa ta bata haquri,ko kuma tayi qoqarin kare kanta ko ta masa turjiya ya jibgi banza a gabanta taci dariya ta more.Da idanu sumayyan tabi mukhtar din ganin yadda ya diba shima ya bita cikin wani tashin hankali da yaji ya rikito masa sanda ya fara jiyo sautin kukanta,wanda babu qwalla ko daya sai tsabar ihu da iya manaqisa,kai sumayya ta kada zuciyarta ta karye,lallai babu shakka wani sabon SHAFIN QADDARAR TA NE YA SAKE BUDEWA CIKIN KUNDIN QADDARARTA,sau ta lallashi kanta kawai ta shige ciki da jakar tasa ta ratsa ta cikin falon nasu ta wuce sashen sa.
YOU ARE READING
KUNDIN QADDARATA
Mystery / ThrillerKalmar QADDARA kalma ce dake rataye bisa wuyan kowanne bawa,haka rayuwa ta gada,tafe take da QADDARORI kala kala,masu zaqi da akasin haka............. SUMAYYA na kallon yadda KUNDIN QADDARARTA ke ta bude mata shafi bayan shafi na TATA QADDARAR kowan...