*Bismillahir rahmanir rahim*
*LA HAULA WALA QUWWATA ILLA BILLAHIL ALIYYUL AZIM*
___________________________________Zuba masa ido kawai tayi tana jin wani zallar bacin rai na ratsata,hawaye na bin kuncinta,ji take a duniya ya gama tozar tata,ya gama wulaqantata,a dacan ba haka ai ta sanshi ba,ta ina zata fara debo irin rayuwar da yake da muradi,sam ko daya ita ba zata iya ba
"Yanzu na sake tabbatarwa cewa baka qaunata almustapha,kanka tsaye kake gayan wadan nan maganganun?" Ta furta tana nuna qirjinta da yatsa,a nutse ya daga idanunshi ya zuba mata su,wato wanda yayi nisa baijin kira,barin hali sai mutuwa?,duk yadda ya kai ga dorata a hanya kenan qaryarshi ta sha qarya,bazata taba fahimta ba,ya fuskanci duk abinda yake gaya mata ashe bata bakinsa yake,kwanaki biyun da yayi dakinta ya bata lokuta sosai yana nusasheshe da ita abubuwa da dama,ta kuma kwantar da kai ta nuna tana dauka,ashe duka busa yake mata cikin kunnuwanta ba magana ba.Tsam kawai ya miqe ya ci gaba da rage kayan jikinshin,ya daura towel ya shiga toilet,yana tsaye riqe da qugunshi yana tarawa kanshi ruwan wanka ta turo qofat,hankalinshi kaf bai wajen,ya kasu gida biyu,wani na wajen sumayya yana tunanin tayi bacci kuwa?,yayin da daya ke kai kawo kan halaye da dabi'un su'ad
"Kana nufin kai maisheni banza da baka da lokacinta kenan?,amma ita waccar ai kana da nata lokacin ko?,har kana iya kamata bayan qazantar data futar,wanda iyakar sanina da kai kana da qyanqyamin da bansan lokacin daka zama haka ba" shiru yayi mata baice mata kanzil ba,iya tsahin rayuwarshi mutum ne da baya son hayaniya,tubewa yayi ya shige bathtube abinshi ya barta tsaye,sai ta fashe da kukan baqinciki ta juya ta fice zuwa uwar dakin.A nutse yayi wankanshi,ranshi na sake fari da haske a duk sanda ya tuna cewa nan da wasu watanni shima zai zama baba,nan da wasu watanni zai dinga gajin gilmawar yaro ko yarinua cikin gidanshi,yaron da za'a kirashi da d'anshi,mallakinshi,jininshi,murmushin farinciki ne ya subuce masa sannan ya miqe ya fito.
Kwance rub da ciki ya tadda ta tana rusgar kuka,ya bude ma'ajiyar kayanshi ya fitar da shirt da trouser ya sanya,ya shirya tsaf abinshi ya fice ya sauka qasa,dining ya wuce yayi serving kanshi yaci abinci ya qoshi sannan ya wuce zuwa sashen ummee.
A kwance ya taddata tana kallon news a al-akhbar,sallamarshi ta sanyata miqewa ta zauna tana amsawa,suna ranta shi da sunayyan tun jiya da bataji motsim daya daga cikinsu ba,ya qaraso wajenta fuskarshi dauke da murmushi ya zauna gefanta suka soma gaisawa
"Ya sumayyan take?"ummin ta tambayeshi ba tare data tambayi su'ad ba,rabonta data shigo ta gaidasu tun shekaran jiya da suka shigo tare da shi,amma ita hakan ba damuwarta bace tunda dama ba zamansu take ba zaman mijinta take,indai kuma suna zaune lafiya lau to da sauqi
"Lafiya.....na barota tana bacci"
"To masha Allah" hira suka shiga yi irin ta da da uwa,cikin daqiqu kadan ta fuskanci yaron nata na cikin farinciki da annashuwa qwarai,sai ta danganta hakan da cewa tsantsar farinciki kulawa da walwalar da yake samu ne daga wajen abokiyar zamanshi,ya jima gurin ummeen sosai sunyi hirar da suka jima basuyi irinta ba,bai bar wajen har bayan sallar magariba,sai da aka kirashi a waya ya qarasa baqin get wajen masu gadi da kanshi ya amshi saqon da ya bayar ayi masa order.Sanda ta farka taji dadin jikinta sosai,hakan ya sanya ta shiga toileta ta hada ruwan wanka mai dumi ta wanke jikinta,ta dawo gaban madubi daure da towel ta janyo kujera ta zauna kai,don kasala take ji ba zata tsaiyawa ba,haka kawai take jin wani farinciki da annashuwa tana ratsata,ta dinga kallon kanta a madubi tana sakin murmushi,lokaci lokaci tana shafa cikin nata wanda yake a dame da hannunta,itakam ciki na zuwa mata a bazata,tun yanzun Allah ya dasa mata so da qaunar abinda take so tamkar yadda taso abdallah tun kafin ta haifeshi,gababta ya yanke ya fadi sanda ta tuna irin gwagwarmayar da tasha hannun zainab,tsantsar makirci zalla da kuma wuyar da tasha kafin abdallah ua kai labari,ambaton sunan Allah ta dinga yi tana nemawa kanta da abinda ke cikinta tsari tun daga lokacin,bata fatan makamancin abinda ya faru da ita wancan karon ya sake maimaituwa da ita, akasalance ta dinga shafa man gabanta na faduwa ta wani bangaren.
YOU ARE READING
KUNDIN QADDARATA
Mistério / SuspenseKalmar QADDARA kalma ce dake rataye bisa wuyan kowanne bawa,haka rayuwa ta gada,tafe take da QADDARORI kala kala,masu zaqi da akasin haka............. SUMAYYA na kallon yadda KUNDIN QADDARARTA ke ta bude mata shafi bayan shafi na TATA QADDARAR kowan...