Babi na goma sha biyu

9.2K 869 109
                                    

*Bismillahir rahmanir rahim*

*qul innal amra kullahu lillah*



          Sallamar fadima ce ta ratsa dodon kunnenta,tana daga kitchen din ta amsa mata,kai tsaye ta nufo kitchen din ta leqo,murmushi sumayya tayi qoqarin sannan tace
"Au fadima ce?" Yatsina fuska tayi ta karkace baki tace
"Eh.....nice,ana ta kitchen ne anata fama?" Cikin jin dadin jin fitowar kyakkyawan furuci yau daga bakin wanda ya jibanci mukhtar zuwa gareta tace
"Wallahi kuwa,kin ganmu muna ta fama da sanwa" bisa ga sabanin tunaninta sai taji tace
"A'aha,anan dama aka fi kauri ai,aci a cika mana gida da kashi,sockaway nan da nan ta tumbatsa" sosai maganar ta bata ranta,cin fuskar tana ganin kullum dada gaba yake,me yayi zafi ne haka?,ba aure bane kuma ta bar dan uwansu yayi,tunda a yanzu suna da wadda suke tunanin zata cika muradinsu ai yaci ace sun sakar mata mara tayu fitsari yadda ya kamata,sai ta sake yin wani murmushin idanunta cikin na fatiman
"Ayyah,ai kayi auren ma kayi kashi cikin gidan mijinka ma rahama ce,wasu har yau an rasa wanda zai daukesu ya kaisu gidansa ko kashin ne ma suyi" sarai ta fahimci magana ta yaba mata,a fusace ta qarasa shigowa kitchen din tana tunkarar sumayya kamar zata kai mata shaqa
"Da uban wa kike?"
"Da wanda ya tsargu" ta fada tana bude tukunyar miyarta tana juyawa,wuyanta ta ruqo ta baya,a nutse ta juyo ta sanya hannunta ta zare shi daga wuyan nata tana nunata da yatsa
"Kada ki kuskura fati" sumayyan ta fada kana ta ja tsaki ta juya taci gaba da abinda takeyi.

        Baki ta saki galala tana dubanta,iya tsawon zamanta da su ko kallon banza babu wanda sumayyar ta taba yiwa duk irin budurin da sukeyi tsakiyar kanta,kafin ta kai ga cewa komai fa'iza ta sanyo kai cikin kitchen din tana cewa
"To malama,da kika zo nan kika tsaya kina kalen magana nan aka aikoki?" Ta bude baki tayi da niyyar yin magana fa'izan ta tarbeta
"Kinga miqon saqona sai ki dawo kuyita yinta 'yar ayi jikar na saba" waiwayowa fatiman tayi cikin mamakin kalaman fa'izar
"Wace 'yar ayi jikar na saba din?,babata da ta haifeni ta haifi mijinki muntari ko innar babarmu?"
"Kinga duk wanda kika zaba cikinsu,zaki bani saqon ko kuwa?" Ba yadda ta iya saboda yaya yaha ta jadda da mata saqon,amma ta sake yarda fa'iza ba mutunci gareta ba,tsaf zata iya zagesu su dukan,haka tayi haushin kaza juye kan dami ta zabgawa sumayya harara tare da jan doguwar qwafa
"Yar malamai ba'a haifa ba an shanye mana dan uwa" ta fadi tana shirin ficewa tabi bayan fa'iza,dariya tayi
"Au ashe na isa ma" tana jin maganar kuma ta bata haushi tare da mamakin budewar bakin sumayya amma haka ta haqura tabi bayan fa'izar.

          Qeme me fa'izan ta hanata kudin motar komawar bayan ta bata saqon,juyin duniya tace bata da ai dan uwansu bai bada ba,haka nan ba don taso ba ta shiga wajen sumayyan,a lokacin ta gama aikinta tana kan kujera tana gyaran qumbarta(farce)
"Kudin mota nazo ki bani zan koma gida"a nutse ta daga kai ta dubeta
" da na aikeki ina?"fuska ta hade don kada ta rasa
"Ai na sancewa akwai kudi gurinki"
"Wadanda kika bani ajiya kenan dazu" sosai take shan mamakin yadda sumayyan ta zama,amma babu komai komai ya kusa zuwa qarshe saboda haka ta dan sassauto
"Ba halinki bane sumayya ba fa,ko dari ce ki bani zata kaini gida" shiru ta danyi sannan ta ajjiye rezar hannunta ta shiga uwar dakanta ta dauko dari biyu ta miqa mata,babu godi bare na gode ta amsa ta juya ta fice,da kallo ta bita sannan ta girgiza kai,ashe guri suka samu suketa shanya yadda suka so?,wato sam wani mutumin baisan alkunya ba kenan,sai ka sauya launi kuke iya zama dai dai da shi?,idan banda sun sayawa kai raini ina ita ina fadiman ina ita?wadda a qalla ta bata shekara kusan shekara hudu ko biyar
"Allah ya kyauta ya rufa asiri" ta fada a fili tana ci gaba da abinda take.

          Lafiya lau yau tayi barcinta har ta kammala ranakun girkinta ta miqa mukhtar din ga fa'iza.

         Kasancewar da safe suje miqa girki ga wadda zata karba ya sanya tana kammala komai ta wanke kanta ta wuce gidan kitso nam qarshen layinsu,sai data fara shiga gidan maman nana ta dauki saboda tana son zuwa gida sannan suka wuce.

           Zuwa sha daya na rana aka gama mata kitson ta wuce gidansu.

          A kitchen ta tadda innarta ta dora sanwar rana,gidan babu kowa saboda qannen nata duk weekend na zuwa wata islamiya tun tara na safe sai biyar da rabi na yamma suke dawowa.

         "Ina fatan lafiya kuke dai ko?" Innar ta tambayeta bayan sun gama gaisawa,murmushi ta saki ta kada kai
"Lafiya qalau inna"
"To madalla haka akeson ji,aci gaba dai da haquri,zaman aure ko kai kadai ne sai kayi haquri balle kuma da abokiyar zama,Allah yayi miki albarka"cikin jin dadin addu'arta tace
" amin inna na gode"suka dan fada wata hirar kafin tace
"Wai ni kam inna ina ya abbakar?,ko leqoni fa inna baya yi" ta fada cikin shagwabe fuska
"Hmmm,yayanku ai yanzu bai ga ta zama ba,ya dauko aure" cikim zumudi da murna sumayya tace
"Allah innarmu?,wace a ina take"
"A'ah,sai ki jira shi yazo kuma wannan kyaji daga bakinsa" ta fada innar tana miqewa saboda kasancewar abubakar dan fari a gunta.

          Tana nan har abubakar din ya dawo,nan suka sha hirarsu,sai kusan shida saura ya dauketa kan babur dinsa ya kaita har qofar gida,tayi tayi ya shigo yaqi haka ta haqura.

          Muqullinta ta sanya ta bude dakin nata ta sanya kai zata shiga,wani dunqulallen abu ya tokareta,tashi daya taji wani azabbaben bacin rai ya kamata,tsanar dakin ta mamayeta,sai ta koma da baya ta janyo kujera 'yar tsuguno bakin qofar dakin ta zauna,duk da uban tarin gajiyar da ta debo amma sam bata sha'awar shiga dakin.

           Har qarfe goma na dare tana tsakar gudan zaune,a nan tayi magariba tayi isha'i kasancewar mukhtar baya gari yayi tafiya legos sarin kaya.

           Tsakar gidan yayi tsit sai ita daya,fa'iza ta gama kara kainarta ta qule daka tana kyautata zaton ma tayi bacci,gashi babu hasken wutar lantarki don nepa sunyi tsiyar,gidan taje ta rufe sannan ta dawo tsakar gidan,ta jima tsaye a bakin qofar tana nanata addu'a sannan taji salama na saujarwa ruhinta,ta kwashi jakarta ta shiga dakin gabanta na wani irin bugawa,kayanta kawai ta sauya ta haye gado a takure wani tsoro da batasan na meye ba fal ranta.

            Cikin baccinta taji kamar ana tashinta,a firgice ta farka tana ambaton Allah,tamkar ana korota daga dakin haka ta dinga ji,a gaggauce ta fito izuwa tsakar gida jikinta na rawa,sulalewa tayi ta zauna dirshan jikin qofar dakin tana ci gaba da kiran sunan Allah a haka asuba ta risketa,a nan ta daura alwala tayi sallar asubar.

          Qarfe shida da rabi na safiya taji wani irin qwarin gwiwa na shigarta,ta miqe cikin hanzari ta koma cikin dakin,tamkar ana tafasa zuciyarta da tsanar dakin ta nufi uwar dakanta ta dangana da sif dinta,akwatinta ta jawo tamkar ana umartarta ta shiga loda kayanta tsaf sannan ta sauya na jikinta ta rufe akwatin ta janyo shi waje,sakatar gidan ta zare kana ta fice kai tsaye ta nufi bakin titi.

         Ta kusan a qalla awa guda tsaye bakin titin ba tare da ta samu abun hawa ba kasancewar safiya ce babu yawaitar sawaye,sai da ta fara qosawa sa tsaiwar har tana tunanin fara takawa da sawayenta wani mai adaidaita ya nufo inda take,da hanzari ta tsaidashi gudun kada ya wuce ta rasashi,ta gaya masa inda zai kaita shi kuma ya gaya mata abinda zata biya,ba tare da ta tsaya ciniki da shi ba ta hau tare da tura akwatinta ciki shima.

*masu karatu muje zuwa,kada kuce komai kowanne dan adam da irin tasa QADDARAR*

*Mrs muhammad ce*

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now