Babi na hamsin da daya

8.5K 793 38
                                    

*Bismillahir rahmanir rahim*

_______________________________
Innal laha ma'al lazinat taqau wallazina hum muhsinun*

*haqiqa Allah yana tare da masu jin tsoronsa,kuma yana tare da masu kyautatawa*
____________________________

    A hankali jerin gwanon motocin jami'an tsaron suka dinga kutsa kai cikin hanyar don baza'a kirata layi ba,saboda sabuwar unguwa ce wadda ba'a kammala ginin nikan dake cikinta ba balle a samu sukunin gabe layuka,kana iya bi ta ko ina,cikin gonaki ko filayen dake daura da wajen wucewarka,motar dake gaba mutumin dake kusa da mazaunin direba wanda shine shugaban 'yan sanda shi ya dauki wata waya da jami'an tsaro suke magana don bada umarni zuwa sasanni dabaj daban ya kara a bakinsa yana bada sanarwa ga sauran motocin dake biye da su a baya a kan su kashe jiniya,sannan ko wannensu ya shrya don suna gab da qarasawa gidan da na'ura ta musu nuni cewa a wannan gun layin wayar mukhtar ke aiki.

      Sosai suka dinga rage gudu har suka qaraso daura da gidan inda suka faka motocinsu,ogan nasu ya sauka ya bawa kowanne umarni kan inda zai tsaya,kafin wani dan lokaci sun zagaye gidan baki dayansa,daya daga cikinsu wanda ke sanye da kayan gida saidai akwai qaramar bindiga boye a aljihunsa ya nufi qofar gidan kai tsaye,yayi bugu kusan sau goma kafin ya jiyo wata kakkausar murya na tambayar wane,nine yace aka sake maimaitawa da cewa kai wane
"Gun oga nazo,idan na baza'a bude ba ai harkar ba dole bace sai na koma akwai masu jira na"ya fada cikin zafi zafi
" bari na sanar masa"mai maganar yace yana mai juyawa zuwa cikin gidan,a falon gidan ya samesu harda ZAINAB dake zaune tana dakon zuwan mutumin da zata saidawa abdallah da shi,wanda abdallah ke zaune gefe daya a falon cikin kashi da fitsari,kwanukan da yake cin abinci da su suma sun gauraya cikin qazantar,yana sanarmusu baqo yazo oga ya bada umarni a bude masa ga zatonsu mao siyan yaron ne yazo.

      Yana kammala bude qofar yayi caraf ya damqeshi,bindiga ya nuna masa saitin kansa yana cewa
"Duk wani motsi da zaka yi wanda zai alamtawa abokan aikinka akwai matsala dai dai yake da harba alburushi cikin kwanyarka,muje ka nuna mana inda suke" kai ya kada idanuwa a warwaje kamar an shaqe mujiya,alama ya yiwa sauran jami'an tsaron da zasu shiga ciki suka biyo bayansu.

       Kusan su biyar ne a falon,ganin an taso dan uwansu da bindiga ya sanyasu saita tasu
"Ku ajjiye makamanku,idan ba haka ba ku baqunci lahira" cewar wani gabjejen dan sanda cikin kakkausar murya,da fari sun so suyi gardama,amma daga bisani da suka ga yawan jami'an tsaron ya sanya su ajjiye makaman nasu aka tattarasu gu daya sannan aka fara aikin daure musu hannayensu don yin gaba da su.

      Tuni cikin zainab ya duri ruwa,ta tabbatar cewa matuqar batayi wani abu da zata wanke kanta ba tun anan babu shakka tata ta qare,saboda haka tayi hanzari ta faki idanuwansu ta zagaya inda abdallah ke zaune cikim qazanta yana kallon kowa ta kunceshi ta qanqameshi a jikinta duk wari da zarnin da take shaqa ta hadiyeshi,sai ta saki kuka mai gunji tana fadin
"Allah na gode maka da ka kubutar da mu daga hannun wadan nan azzaluman,Allah abin godiya" kukan nata na qarya yaja hankalinsu,wannan kakkauran dan sandan daya gama qullesu ya kalleta yana zare ido,cikin daga tsawa yace
"Kefa?,daga ina?"ance mara gaskiya ko cikin ruwa gumi yake,take jikinta ya kama rawa cikin rawar murya tace
" nice....nice uwar dannan,sato mu sukayi"baki dayansu 'yan sanda suka zuba mata ido,kowa dai yasan case din rasa abdallah,hakanan sunsan uwa da ubanshi,to ita wannan din wace da zata ce uwarsa ce
"Wallahi qarya take yallabai,ita ta bamu kwangilar kashe......." Wanda ya bude musu qofa wanda da alama duk ya fisu tsoro ya fara rattabo bayani cikin rawar jiki
"Qarya ne sharri zai min" zainab ta fada cikin daga murya tare da yunqurin hanashi tona mata asiri,take sai musu yaso ya balle tsakaninta da shi,shi yana son bayyanawa ita tana son hanawa,yayin da ogan nasu haushin zainab ya tsaya masa a wuya,ya tabbatar koma meye wannan kama sun yana da alaqa da aikinta da suka aiwatar mata,ji yake ina ma bai ya da bindigarsa ba,da babu shakka sai ya fasa mata kai da harsashi a take,amma babu komai,idan kere na yawo zabo na yawo zasu hade,tsawa shugan 'yan sandan ya buga musu wadda ta sanyasu yin tsit
"Lawan,dauke abdallah,idris ka sanya mata ankwa itama,ko meye ma ya kawota nan din muje bincike zai nuna" ya fada yana ficewa tare da yi musu umarnin su tafi,zainab na zare ido na komai aka buga mata ankwa aka hadata da tsagerun aka tura cikin mota,sun fara tafiya kenan ogan ya faki idon dan sandan dake tsare da su ya daga kafceceyar qafarsa ya daki ta zainab cike da jin haushinta da ganin ta jaza musu masifa,ji kake qasssssss zainab din ta saki wata razananniyar qara ta sume,shugaban 'yan sanda shi yace aci gaba da tafiya kada a tsaya idan anje station a mata duk taimakon da za'ayi,yayin da yasa suka qara dora kula a kan oga don gudun kada ya subuce musu.

         Tun safe da taga fitar malam alhj farouq da kawu hankalinta ya kasa kwanciya,duk da cikin damuwa take sai damuwar tata ta ninka ta da,jan carbi take wanda shi ya zamo mata abokin hirarta tana share hawaye,har aka yi sallar la'asar babu labarinsu,abunda ta kula da shi shine lokaci lokaci anty dije na daga waya tana kiran mai gidanta,saidai babu wanda ta tambaya kamar yadda babu wanda ya yimata bayani.

      Cikin dakinta tayi sallar magariba tana jiran isha'i,ta zurfafa a cikin tunani anty dije ta shigo
"Kizo inji su malam"
"To" ta fada ba tare da ta iya motsawa ba,gabanta ne ya tsananta faduwa,zuciyarta ta ta cire tsammani ,wala'alla ba'a samu nasara ba,wala'alla ta rasa abdallanta kamar yadda ta rasa mahaifinsa,shikenan haka Allah ya tsarama rayuwarta,sai ta kife kanta jikin gado ta saki kuka
"A'ah,subhanallahi sumayya kuka dai?,ke da nace kije su malam da abban laila(alhj farouq)na jiranki,tashi don Allah ki bar kukan nan haka" anty dije ta fada tana qoqarin dagata,ita ta dafa don ba cin abinci take ba balle ta samu qwarin jikinta a haka har suka isa falon.

     Bata san ta saki anty dije ba,bata san kan qafafunta take tafiya ba sai data isa gaban abdallah ta zube wanda ke kan cinyar ya abbakar,wani sabon kuka ta saki tana yunqurin daukar yaron ganin yadda ya sauya cikin kwanakin da basu wuce goma ba,yayi baqi ya rame goshinsa har da ciwo,a haka ma sai da aka kaishi wajen mama tayi masa wanka ta bashi abinci yaci aka sauya masa sababbin kaya,qanqameshi tayi tana sake sakin kuka mai cin rai,kowa tausaya mata yake tare dayi mata kyakkyawar addu'ar yankewar qaddarorinta haka nan,a hankali alhj farouq ke bayani
"Alhamdulillahi an kama Abdallah tare da wasu wadanda babu shakka su sukayi sanadin mutuwar mukhtar kamar yadda sukayi iqirari da kansu,tunda an kamasu da wadansu abubuwa dake sake bayyanar da hakanne,cikin wadanda aka kama harda wata ZAINAB wadda da fari ta musu iqirarin cewa itace mahaifiyarsa" da sauri sumayya ta dago kai tana maimaita zainab cikin ranta gabanta na ci gaba da faduwa,alhj farouq ya dora
"Amma abinda su yaran suka ce shine ita ta dauki ta basu aikin kashe mukhtar,sannan daga bisani da taga ba zata iya biyansu sauran kudin ba ta sauya shawarar daukar abdallah ta tafi neman kudi da shi,taga gwara su saida abdallah ta biya kudin sauran tayi harkar gabanta" ba sumayya ba wannan karon,baki daya jama'ar dake falon ba qaramin girgiza sukayi ba,wannan waccw iriyar masifa ce,tamkar ba diyar musulmi ba,tamkar babu digon musulunci a jikinta,wannan karon cak kukan sumayya ya tsaya,sunayen Allah ta dinga kira,tsoron zainab na kamata kamar tana wajen,kisa zainab,kisa?,kisan mukhtar?,daga bisani wani hawayen ya sake subuce mata,har ta gaji da kuka haka nan,ko da yaushe idanunta zafi suke mata saboda kuka,har wani lokaci take gani hatsa hatsa,sai ta rufe idonta tana godewa Allah daya QADDARA mata sake rayuwa da d'anta,ya kubutar mata da d'anta cikin aminci da salama,bata san da wanne baki zata godewa uncle mukhtar mijin anty dije ba,ta sake jinjina masa da yadda yayi zumunci irin haka sanda taji yana fadin idan aka kammala bincike cikin 'yan watanni qalilan insha Allah za'a soma shari'a,don dole abi kadin haqqin rai a kuma hukunta duk wanda ke da hannu cikin lamarin,tabbas babu shakka indai har da zainab cikin wadanda suka aikata wannan aiki mutum ya zama abun tsoro,to idan babu sa hannunta shin me ya kaita wajen?,har tana iqirarin abdallah danta ne?,ita ce mamarsa?
"Ya Allah ka yimin gata,ka shigemin gaba,ka yimin jagora cikin al'amuran rayuwa ta" abinda ta dinga fadi kenan tana maimaitawa rungume da abdallah a jikinta,shi kansa yaron kallonta yake tayi yana kiran ammi lokaci zuwa lokaci,haka yayi luf a jikinta jikinsa a sanyaye yana jin dumin mahaifiyarsa.

   ******    ********   ******

*wai ina lukman ne?*

*kuyi haquri da wannan sabgogi sun sha min kai,ku tara gobe in sha Allahu*

*mrs muhammad ce*

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now