*Bismillahir rahmanir rahim*
*innalillahi wa inna ailaihu raji'un*
*Allah subahanahu wata'ala yana cewa cikin qur'aninsa*
*RANAR DA ZAMU CE DA JAHANNAMA SHIN KIN CIKA?,SAI TACE AKWAI QAARI NE?(na mutanen da za'a zuba mata)*
*subhanallah,Allahumma ajirna minan nar*
____________________________________
Ba yadda ummee ta iya wani lokaci haka take biyewa tsiyar su'ad,ta lallabata,takan yiwa mustapha fada idan ya mata tsawa ko ya niyyaci dukanta,sam bai son sangartarta,bai shiga gidansu ma sabida halayyarta data uwarta da bata yi masa ba,ummee bata son yadda yake mata,takan ce yarinya ce fa mustapha su'ad har yanzj,cikin zuciyarta kuma bata ganin laifin kowa sai na uwarta,tunda ance ice tun yana danye.....,haka nan barewa bata gudu danta yayi rarrafe.
Tun yana qaraminsa Allah ya zuba masa miskilanci,halinshi ne,halittarsa ce haka gado yayi,yaro ne shi mai zubin gidan sarauta,yana qaunar doki,kayan sarauta da duk wani abu daya danganci hawa doki,kusan yadda halayyarsa take tamkar babban mutum ya sanya abokansa yaran turawa ke tsokanarshi da sunan MAN,mukhtar baabaa prof shima yakan tsokaneshi lokaci lokaci,daga haka sunan ya bishi,son dokinshi ya sanya baabaa prof tun a lokaci yakan siya masa ticket yaje kallon wasan polo tun a american,yawan kallon wasan polo ya sanya su'ad itama wasan ya soma burgeta,bai da abokin tafiya duk sanda zashi kallon,sai ita ke nacewa zata rakashi,tun yana daka mata tsawa yana korarta yana cewa ba zata rakashi ba har ya fara barinta tana binsa,saidai har suje su dawo bai tanka mata,ita kuwa ta cikashi da surutu,abinda baiso kenan,yanzu kansa zai hau ciwo,don ciwon kai bai masa wuya.
Tsabar qwaqwalwa da Allah ya zuba masa ya sanya aka daukeshi daga nursery zuwa primary,a can din ma suka fuskanci basirarsa ta girmewa gurbin da suka bishi,tilas aka sake turashi ajin da zasu kammala secondry a shekarar,
A shekarar ne baabaa yaga dacewar ajjiye aikinsa ya dawo gida ya tattara kan iyalinshi baki daya,anty maamaa dake abuja da ummee dake tare da shi a america,maida hankalinsa sosai yayi ya tasamma gina katafaren gidanshi a abujan,gini ne dashi kansa yasan cewa ya kashe masa maqudan kudade duk da ba komai bane abinda ya cira wajen ginin cikin irin dukiyar da Allah ya hore masa,a yanzu ya tabbatar baida wasu family na jikinsa sosai baya ga sauran dangi tsiraru da suka rage banda yaransa da ya haifa,wanda a yanzu sun zama su bakwai,ummee na da biyar
ADAM
MUSTAPHA
FARIDA(UMMAN HUSNA)
HUDA sau auta
SUMAYYA(AMIRA)Bilkisu anty maamaa na da yara biyu duka maza
MAHMOUD da
USAMAGini yayi yana mai hasashen gaba,yana son yaransa maza su zauna da shi idan Allah ya hukunta hakan cikin gida daya,hakan ya sanya yayi sassa biyu,ko wane sashi akwai wasu sassan ciki,duk a lokacin ma adam da yake babba a lokacin yake ss two a can american,sanda suka tashu tafiya aka bar adam ya kammala secondry dinsa,yayin da uncle abdus samad mahaifin su'ad ya nemi alfarmar a bar masa mustapha,saboda ya lura da yadda su'ad ke daga hankalinta daga jin labarin tafiyarsu,da fari mustapha yaqi ya murje idanunsa,sabida asalan shi mutum ne da bai boye abinda ke ransa koda ba zai maka dadi ba,gaskiya ce zaya fadeta komai dacinta,saida baabaa prof ya jashi yayi masa fada kaca kaca,ya gaya masa abdus samad babansa ne kamar yadda shima yake babansa,yarone mai biyayya da bin umarnin iyayensa komai tsaurinsa,baison bata musu ko yaya,hakan ya sanya ya sunkuyar da kai,bai sake cewa qala ba har akayi aka gama suka tafi suka barshi hannun abdus samad da matarsa khaulat,murna cikin khaulat kamar tayi me,a take ta dinga hasasowa ranta hada mustapha da su'ad,tabbas ba zata bari 'yarta tayi asarar babban gida irin wannan ba,zata so hada alaqa da gudan professor mukhtar muhammad,tabbas ba qaramin kankaro mutunci bane ku samu relation da attajirai irinsu,shu'umin murmushi ta saki,kusan ita ta qara kitsawa su'ad soyayyar mustapha,tunu yarinya ta hau turba,dama gata cikin turawa,batasan kunya ba ko kadan,a shekarun har tasan wani soyayya da i love you,a haka shekaru suka fara tafiya,adam ya kammala karatunsa yana niyyar komawa naijeria,yana son qasar tayi masa,ba kamar mustapha ba da ya lura tunda aka tafi aka barshi bai kuma zancan qasar ba,fushi ne ko ameriacn tafi yi masa oho?.
YOU ARE READING
KUNDIN QADDARATA
Tajemnica / ThrillerKalmar QADDARA kalma ce dake rataye bisa wuyan kowanne bawa,haka rayuwa ta gada,tafe take da QADDARORI kala kala,masu zaqi da akasin haka............. SUMAYYA na kallon yadda KUNDIN QADDARARTA ke ta bude mata shafi bayan shafi na TATA QADDARAR kowan...