page 1

7.7K 431 32
                                    

*REAL PURE MOMMENT  OF LIFE WRITERS P.M.L*💭💭💭

ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035

    *KUK🅰N KURCIY🅰*🐦🐦🐦

      *Written by*
💅💅 *Sadnaf*💅💅

*Gajeran labarai dake k'unshe da darussa Wanda ya faru a gaske Wanda ba wai labari aka bani ba aa ni ganau ce na Dade  inaso na rubuta amma Allah bai nufa ba sai yanzu Allah yasa sak'on ya isa ya kuma amfani al-umma Bismillahi rahamanir Rahim*

*true life story*

*Page 1*

Amina a zaune take  a tsakiyar kananan yaranta tana duba Home work d'in da suke yi tana gyara musu duk inda suka yi ba dai- dai ba Littafin Sadiq d'anta na Biyar data k'arba take dubawa tana girgiza kai cikin tsananin takaicin irin Zeron da yake ta samu a kwanakin nan  daya sa wasa agabansa Wanda da ba haka yake ba magana tafara yi tana "Sadiq wai me ke damunka ne kwana biyu mai yasa baka maida hankalin ka akan karatu yanzu dubi yanda aka baka 0/6 duk koya maka Dana ringa yi jiya kace min ka gane ko Dan Kaga bana zaneka"

Hafiz kanin Sadiq da sauri yace "Umma Auntynsu ma tace na gaya miki zata fara Zane shi dan bashi da k'ok'ari sai wasa da yake yi da abokansa"

Takaici ne yasa Amina kai mishi rankwashi akai Sadiq yayi sauri ya kai hannunsa ya fara sosawa sabida yanda rankwashin ya shige shi

"Sadiq wlh zan fara zaneka tunda Yanzu duk k'ok'arin danake yi akan ka baka gani ya za'ayi a madadin ace kana cigaba sai ci baya kake kai da littafinka idan aka duba da wuya asamu zero shine Yanzu ko d'aya baka ci sai dai aga zero"

Sadiq matse idonsa kawai yake yana Sosa kansa

Amina littafin ta jefa mishi tana duba littafin Hassana da Usaina 'yan autan ta da suka kasance 'yan biyu ganin sun iya Home work d'in yasa ta duba na Hafiz taga shima dai-dai yake yi.

Tsawa ta dakawa Sadiq da yake wuki wuki da ido tace "zaka  fara Home work d'in  ko sai na zaneka"

Jiki na rawa Sadiq ya d'auki littafinsa yafara Home work d'in.

Ita kuma ta mik'e ta shiga kitchen dan ta duba girkin data d'ora.

Tana dab da shiga kitchen d'in Abban Hadiza yayi Sallama tare da shigowa cikin gidan fuska a d'aure.

Amsa Sallamar Tayi tana mishi sannu da zuwa.

Ya amsa yana mai shigewa cikin gidan.

Sai da ta duba abincin da ta d'ora ta nufi cikin palon ganin baya ciki yasa ta fito ta shiga d'akinsa dake tsakar gidan dan gidan d'akuna biyu ne  ciki da Palo  sai D'aki d'aya a waje d'akin dake wajen tsakar gidan shi ya  kasance na mai gidan.

D'aga labulen Tayi tare da Shiga ciki.

Abban Hadiza kuwa yana kwance akan katifarsa yana kallon ceiling d'in d'akin yana d'an girgiza k'afa.

Amina a gefensa ta Zauna cikin sanyin murya tace "Sannu Abban Hadiza"

Abban Hadiza bai amsa mata ba illa ma cewa da yayi "Amina nifa na fara gajiya da fitar nan danake yi ina shan wahala yau ma yanda na fita haka na dawo babu ko biyar duk k'ok'arin da nayi dan naga na samo wani Abu  wlh ko biyar bansamu ba duk inda  na je sai dai ace min babu wajen danake neman aikin ma danaje yau hakuri suka bani"

Amina ajiyar zuciya ta sauke tace "Karka damu Abban Hadiza insha Allah zaka samu aikin dazu Dana gaya maka zanje wanan makarantar akan su d'aukeni na ringa musu Nanny tunda sunce bazasu d'aukeni koyarwa ba dan   kwallin secondary gareni to na samu sun d'aukeni kuma albashin ba laifi dubu goma sha biyar zasu ringa biya sunce ma daga gobe nazo na fara to shine na rok'esu su bani koda dubu biyar ne sabida ina da bukata sosai shine na samu suka bani a ciki na d'an siyo mana kayan abinci nasan zai mana kwana biyu yanzu ma haka shinkafa na Dora kwanu daya har dare insha Allahu kafin su kare Allah zai kawo yanda za'ayi"

KUKAN KURCIYAWhere stories live. Discover now