page 14

3.3K 369 48
                                    

® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L*💭💭💭

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035

*KUK🅰AN KURCIY🅰🐦🐦🐦*

       *Written by*
*💅💅SADNAF💅💅*

*page 14*
                 Amina ta  Makance ta kurmance  tsabar b'acin rai bata ga  cikin dake jikin Zaituna ba bata ji ihun da Zaituna take zunduma wa ba dukanta kawai take yi tana kuka.

Abubakar kuwa hankali a tashe ya ringa k'ok'arin banb'are Amina daga jikin Zaituna amma ina Wani irin Ture Abubakar Amina kawai take yi  yana   fad'uwa k'asa.

Su Hadiza kuwa hankali a tashe suka tashi daga bacci suka nufi tsakar gidan sukayi cirko cirko suna kallon Mahaifiyarsu cikin Mamaki dan sun san Halinta tunani suka fara yi mai Zaituna tayi mata haka da ta Zuciya.

Abubakar kuwa ganin dagaske Kisan Kai Amina ke shirin yi yasa ya ringa dukan Amina ta baya dan ta d'aga Zaituna da ma ta kasa ihu sabida Azaba duk ta tsitsige mata kitson Rubber attach d'in da tayi.

Amina kuwa a Zuciye ta d'aga Zaituna ta cakume wuyan Abubakar ta had'a shi da  bango ta hau kai mishi duka Dan sosai fa ta Zuciya.

Hadiza ganin ta shak'e musu wuyan uba yana gwalalo ido yasa suka nufi wajenta suna rok'onta akan ta cika shi watsi tayi dasu Hadiza da suka Rik'e mata hannu ta cika Abubakar tare da nufar d'akin Zaituna ta fara watso duk abinda ta gani a d'akin waje su 'yan biyu kuwa sai kuka suke  suna  kankame da  juna dan sun san yau kashinsu ya bushe idan Amina ta damke su.

Abubakar kuwa sai hakki yake Zaituna na juyi a kasa hannunta dafe da cikinta.

Abubakar ganin har katifa Amina ta wurgo shi waje yasa ya tsaya a bakin k'ofar cikin k'arfin Hali  yace "Amina kanki d'aya kuwa ina kikeso muje daddaren nan naga dai gidana ne bakida ikon korar mu  daga gidan nan"

Amina a haukace tace "wlh kungama zaman gidanan kai da matarka ai gida yanzu ba naka bane gidan 'ya'yana ne babu abinda kake tsinana mana acikin gidanan duk abinda kuke yi ban tab'a yi muku Magana ba tunda abin naku ya kai Ku lalata min tarbiyyar yara wlh dole kubar gidanan kuje duk inda zakuje amma zaman gidanan ya kare muku wlh"

Daga haka ta cigaba da watso kayansu dake cikin drawer waje Abubakar kasa Magana kawai yayi ya cigaba da Kallon ta duk abin nan da akeyi k'arfe uku da rabi na dare sai da Amina ta fitar da komai dake d'akin banda gado da wardrobe sabida bazata iya  fita dasu ba ta fito daga d'akin ta kulle da kwadon dake kan window jikinta rawa kawai yake tana sharce Hawaye.

Tunda take bata tab'a tsintar kanta a cikin irin wanan tashin hankalin ba ace yaran data Dade tana yiwa tarbiyya Mahaifinsu ya jawo suna neman lalacewa tashin hankalin ta bai wuce batasan iya tsawon lokacin da yaran suka fara irin wanan halin ba Hakane yasa ta nufi wajen Hassana da Husaina da ke Zunduma ihu tunda ta nufo inda suke kamar had'in baki suka saki fitsari a wando dan Aminar tana da sauki amma fa idan ta damke ka bazaka ji da dadi ba.

Cakumo su tayi a zuciye ta nufi d'akin ta dasu inda suka ringa ihu suna bata hakuri akan sun daina bazasu kara ba.

Su Hadiza kuwa kuka suka fara yi tsoron Mahaifiyarsu na shigarsu .

Inda tana zuwa bakin k'ofar palon ta juyo tare da daka musu tsawa akan su shigo su kulle mata k'ofa tun kafin ta rufe baki suka shige da sauri suka rufe k'ofar palon tare da sa sakata inda suka bar Abubakar kawai da Zaituna a tsakar gidan.

KUKAN KURCIYAWhere stories live. Discover now