page 7

3.3K 315 21
                                    

® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L*💭💭💭

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035

*KUK🅰AN KURCIY🅰🐦🐦🐦*

       *Written by*
*💅💅SADNAF💅💅*

*Thanks oll for d prayers Alhamdulillah am getting better*

*page 7*

Abun ka da Wanda ke da hakuri bai iya Zuciya ba da Wanda aka kai shi bango  Amina wani irin fincike jikinta tayi daga ruk'on da yayi mata  ta daka mishi wani Mummunan tsawa tana "Abubakar juya ka fitar min daga d'aki tun kafin na fitar dakai da k'arfi"

Abubakar tsananin mamaki da tsoron Aminar ne ya hana shi motsawa daga inda yake dan tunda yake da ita ko d'aga mishi Murya bata tab'a yi ba ballantana har akai ga ta daka mishi tsawa.

"Ko bazaka fita bane"?

Amina ta kara ce mishi a tsawace.

"Amina kina da hankali kuwa ni Mijinki kike dakawa tsawa ni mijinki kike kora daga d'akinki"

Abubakar yace yana nuna kansa

"Mijina a da ba amma banda Yanzu ka fitar min daga d'aki nace Abubakar ko kana so dai na fitar dakai da kaina.

Abubakar cikin k'arfin hali yace

" Amina kinyi kad'an ki koreni daga d'akina dan nan gidana ne zan dai fita  Yanzu sabida na san kishi da bak'in ciki ne yake dawaniya dake kar naki fita abun ya miki yawa banza Shashasha"

"Naji atafi dai mai buduruwar Zuciya ko kunya bakaji"

Abubakar bai tanka ta ba ya fice daga d'akin.

Amina kuwa tabishi da uwar harara tare da Jan dogon tsaki.

Abubakar kuwa yana zuwa ya tarar da Zaituna tana wani cije cijen lebb'e.

Zama yayi a gefenta yace "Amarya sai dai kisha shayi da bredin ko kuma kiyi k'ok'ari ki soya dankalin  dan waccar guzumar sai da na had'a mata da duka akan ta soya miki dankalin amma sabida taurin Zuciya wai sai dai na kasheta"

Zaituna mik'ewa tayi cikin tsananin farincikin dukan dayace yayi mata tace "Haba Baby ai da baka daketa ba kishinka ke dawainiya da ita ba komai bari na tafasa mana ruwan shayin"

Daga haka tayi hanyar waje k'afa aware har dasu dinginshi .

Abubakar sai a lokacin ya tuna darensu na jiya can k'asan Zuciyarsa kuwa yana kokwantan bashi ya fara Sanin Zaituna ba.

Sai da suka sha shayin suka k'ara soyewa kafin Abubakar yaci wanka ya saka d'aya daga cikin sababin kayan daya dinka inda yafito a ango sak.

Zaituna kuwa tana wankan ta k'ara kwanciya bacci yayi awon gaba da ita.

Abubakar kuwa yana fitowa bai zame ko'ina ba sai Majalisarsu data cika tayi dinkim ana jiran zuwansa dan Alkawari yayi musu akan zai basu labari bare ma yanda labari ya bazu akan yanda amaryar Abubakar ta cika unguwar da ihu da hirarsa suka tashi Majalisarsu   inda kowa ya matsu gari ya waye su sha labari daga wajensa.

Tun daga Nesa suka fara Mishi kirarin " Ango kasha kamshi sai kyalli kake"

Abubakar murmushi kawai yake yana wani tafiya a dage shi alailai ango.

Yana k'arasawa suka saki ihu harda daga shi sama sai da suka dan nutsu suka saka shi a tsakiyarsu dayake katon tabarma suka  Shimfid'a.

Nan take suka hau tambayarsa wane irin dadi Zaituna ta shayar dashi haka da ya kusa kasheta taringa zunduma ihu har mak'ota.

KUKAN KURCIYAWhere stories live. Discover now