page 5

3.8K 304 23
                                    

® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L*💭💭💭

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035

*KUK🅰AN KURCIY🅰🐦🐦🐦*

       *Written by*
*💅💅SADNAF💅💅*

*WANAN SHAFIN NAKINE KE D'AYA AUNTYNA AUNTY SIS ILVSM WISH U OLL D BEST*

*page 5*

B'angaren zuhura kuwa sai abinda yayi gaba wajen lalaci da san jiki dan babu abinda ta canza a cikin hallayenta in banda ma k'azanta da abubuwa sukayi dan yanzu har band'akinta take sa Babawo ya wanke mata yana yi yana karewa panties d'in ta dake jibge a bokiti da kallo idan ya fito ma sai ya bi ko'ina na d'akin ya chaje ko zai samu abun d'auka.

Su laila kuwa babu laifi ba kamar kwanakin baya da suke zuwa da danyen indomie makaranta ba yanzu duk abinda suke so dashi suke tafiya dan Maman Baby ita ke dawainiyar dafa musu abinci su tafi dashi tunda suka tsadance da Zuhura akan zata ringa biyanta duk wata banda morarta da mamn Baby ke yi albarkacin abincin da take dafawa su Laila suma suke samu suci kayan dadi dan mijinta ba mai k'arfi bane zuwa wanan lokacin har kanwar Maman Baby Safna ita ke shiga gidan tayiwa Zuhura girkin rana Dana dare Zuhura kuwa tayi mata alheri.

Da biyu Mamn Baby tace kanwarta ta ringa zuwa gidan sabida ta gama karantar Zuhura ballaga ce ta bugawa ajarida da bata da rabo da godiyar Allah Dan niimar da take ciki wasu ko kwatanshi basu samu ba take wasa da damarta fatan ta bai wuce wataran Musbahu yaga Safna yace yanaso ba.

A yau wajen k'arfe tara na safe bayan su Laila sun tafi makaranta Zuhura na d'aki ta baje hanci da baki tana baccin asaran da ta saba.

Babawo yazo gidan dan yayi aikinsa kamar yanda ya saba na wanke wanke Sharan Palo da moping.

Sanin  uwar d'akinsa na kaiwa sha d'aya ko biyu tana baccin asara batare da ta ko motsa ba shiyasa yake abunda ransa ke so a gidan kafin ta farka

Yana zuwa bai tsaya b'ata lokaci ba ya Dora indomie super park guda biyu manya ya samu kifin gwangwani guda biyu ya zuba aciki yana gama dafawa.

Ya fasa kwai guda shidda ya soya ya saka a plate daban yaje ya ajiye a tsakiyar carpet din dake palon ya d'auko maltina na gwangwani guda biyu ya ajiye ya cire rigarsa ya ajiye ya rage daga dogon wando sai yagaggen vest d'in daya rage a jikinsa kayan kallo ya k'unna kamar yanda ya saba ya d'an sa volume k'adan yanda Zuhura bazata jiyo shi ba .

Ya zauna yafara cin indomie yana kad'a kai yana bin wakar da ake yi sai sharbana majina yake yi kai idan Kaga Yanda ya zauna ya tankwashe k'afa tunani zakayi dan gidan ne hankalin sa akwance yake cin abincin yana d'aga gwangwanin maltina yana girgiza kai.

Adai-dai lokacin Musbahu ya dawo gida dan ya d'auki kudin daya shigo dasu jiya dan bai san zai yi amfani dasu ba shiyasa bai fita dasu ba.

Dayake a waje yayi parking mai gadi ne kawai yasan da zuwansa.

Sauri yake yi ya isa b'angaren nasu inda yana shiga d'an corridor d'in da zai sada shi da palon ya hango bayan Babawo a zaune a tsakiyar palon nasu yana girgiza kai yana kad'a k'afa.

A d'an mamakince Musbahu yayi slow ya fara tafiya a hankali inda yaci birki a dai dai kan kujerar da Babawo ya bawa baya.

Babawo kuwa ko kad'an bai san da shigowar Musbahu ba loma kawai yake yana girgiza kai hannunsa d'aya d'auke da remote.

KUKAN KURCIYAWhere stories live. Discover now