page 9

3.1K 308 15
                                    

® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L*💭💭💭

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035

*KUK🅰AN KURCIY🅰🐦🐦🐦*

       *Written by*
*💅💅SADNAF💅💅*

*page 9*

Washegari kuwa Amina yunwa  ne yasa ta fitowa wajen k'arfe goma sha d'aya na safe inda ta  tarar da Abubakar da Zaituna a zaune a tsakar gida kan tabarma Abubakar nata ferayar dankali  Daga shi sai gajeran wando sai washe baki yake Zaituna kuwa tayi matashi da cinyarsa dan sosai ta susuta shi Daren jiya inda Abubakar yaringa nan nan da ita dan har salon dai bai sani ba Zaituna ta ringa mishi shiyasa tana cewa dankali zata ci yace ko bai iya ba zai koya.

Kallo d'aya Amina tayi musu ta d'auke kanta cike da takaicin kunyar da Abubakar bayaji tana fata dai ya zamana iya yau zai yi Wanan tab'arar tasa tunda yau yaranta zasu dawo dan Sam bazata lamunci ya gurb'ata mata  tarbiyyar yara ba dan idan ta Zaituna ne ba damuwa zatayi ba amma shi fa dayake Da yara cikin yaran ma har da balagagu haka kawai bazata yarda ya ringa fito  musu da gajeran wando tsakar gida duk abinda zai yi yayi shi a d'aki babu abinda ya shafeta.

Ahaka ta shige Kitchen ta d'ora indomie inda tunda ta fito Zaituna ta fara kissama yanda zata cusa mata bak'inciki.

Tana k'ok'arin d'ora tukunya taji muryar Zaituna na "Mama Amina ina kwana dafatan kintashi Lafiya"

Amina ko d'agowa batayi ta kallesu ba ta cigaba da abinda take yi.

Inda Abubakar kuwa ya tab'e baki ya cigaba da yanke Rabin dankali da sunan ferayewa.

Zaituna ganin ta k'ara maimatawa Amina bata kulata ba yasa tayi rau rau da fuska ta tashi daga kwancen da take ta kalli Abubakar tana "Baby wai nikam mai nayiwa Mama Amina ne idan na gaisheta bata so ta kulani tun jiya fa nake gaisheta bata amsawa mai nayi mata haka me laifi dan na gaisheta ahaka kake ganin za'a samu had'in kai da zaman Lafiya a tsakaninmu"

Abubakar tsaki yayi bayan ya wurgawa Aminar da ko kallonsu batayi da harara yace
"Kema sai kace dolene sai kin gaisheta ki rabu da ita mana Na gaya miki kishi ne yake dawainiya da  ita shiyasa bata kulaki ki rabu da ita taji da bak'in  cikin dayake damunta karki kara gaisheta taje can ta karata mu kuma muyi ta cin amarcinmu".

Murmushi Zaituna tayi cike da jin dadi ta koma ta maida kanta a kan cinyarsa tafara wasa da gashin jikinsa Abubakar kuwa ya fara kyalkyala Dariya yana " Amarya ki bari dan Allah ni wlh yanzu zaki d'aga min hankali'

Zaituna kuwa dan ta cusawa Amina bak'in ciki duk da ba kallonsu take ba had'awa tayi da yi mishi cakulkuli shi kuwa Abubakar yayi ta tsintsira Dariya.

Amina kuwa ko kad'an bata bari b'acin rai ya bayyana a fuskarta ba duk da can k'asan Zuciyarta kamar an zuba mata fetur a k'unna dan Bata tab'a tunanin Abubakar zai iya mata irin Wanan butulcin ba auren da ya k'ara bai b'ata mata rai kamar Yanda yake shuka mata rashin mutunci  yake zubar mata da mutunci agaban Zaituna da bata fi sa'ar 'yarta ba  tabbas duk abinda Zaituna zatayi mata bata da laifi dan Abubakar ne ya bud'e mata k'ofar tayi mata rashin  mutunci dan shi ya nunawa Zaituna bata da wani daraja a idonsa.

Ahaka ta d'aure ta tsaya a kitchen d'in har indomie ya nuna ta juye a plate ta fito ta koma palonta tana dab da shiga palonta taji sun kwashe da mahaukacin Dariya inda ta tsinkayi muryar Abubakar na cewa "wai wayaga kayan wanki buguzum buguzum ji wani tafiya dan Allah"

KUKAN KURCIYAWhere stories live. Discover now