page 10

2.5K 187 17
                                    

® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L*💭💭💭

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035

*KUK🅰AN KURCIY🅰🐦🐦🐦*

       *Written by*
*💅💅SADNAF💅💅*

*page 10*

                Tun kafin ta k'arasa wajen Majalisar ta ringa rusa uban kuka hannu aka kamar wacce ta rasa uwa da uba duk inda ta wuce kallonta kawai akeyi.

Abubakar dake zaune a tsakiyar Tabarma suna buga whot dan sunyi Munafircin sun gaji daga nan suka fara buga whot dan aikin kenan.

Shi ya fara Hango Zaituna daga Nesa hannu aka tana rusa uban kuka inda suma 'yan majallisar suka d'ago suna kallonta sakamakon kukanta daya fara iso musu.

Abubakar Hankali a tashe ya mik'e dan ya tareta inda Garbati yayi saurin rik'e  shi dan suma zasu so ta k'ara so suji dalilin Wanan uban kukan da take yi Adai dai lokacin ta k'araso kusa dasu ta zub'e a kasa tana ta shiga uku  ta lalace.

Tuni 'yan Majalisar suka fara mik'ewa d'aya bayan d'aya suna tambayarta Lafiya.

Inda Abubakar yayi Mutuwar Zaune sabida tsananin takaici dan irin zaman da tayi zaninta rab'ewa yayi gida biyu ana hango gajeran wandon da ta saka.

Cikin ihun Kuka Zaituna tace "Baby Mama Amina da yaranta ne suka had'u suka yi min duka suka cillo ni waje babu abinda nayi musu tunda ka fita ta dawo take zagina ban kulata ba sai da yaranta suka dawo Ta saka Hadiza ta dakeni daga nan sukayi min taron dangi wayyo Allah nashiga uku na lalace ace ina amarya yau kwana na biyu ace har anyi min irin Wanan dukan"

Babu abunda ke tashi sai sallati da sallallami inda Zaituna ta k'ara rushewa da kuka.

Anan kowa ya hau tofa albarkacin bakinsa ana tayi hakuri amma Amina bata kyauta ba.

Abubakar kuwa bak'in ciki da takaicine yasa har lokacin ya kasa bud'e baki yayi magana dan bai tab'a tunanin Zaituna zata iya biyo shi har Majalisa ba.

Sabo ne ya tab'o shi yace "Wai ya kayi shiru ne ka tashi ka rakata gidan kaje kaji mai dalilin daya sa sukayi mata taron dangi haka "

Abubakar mik'ewa yayi yace "Tashi mutafi gidan"

Zaituna mik'ewa tayi har lokacin tana kuka kamar wacce ake cirewa rai tabi bayan Abubakar daya yi gaba kamar zai tashi sama.

Ko nisa basuyi ba 'yan Majalisar suka fara yi dasu.

Suna d'an yi nisa Abubakar ya juyo yace cikin tsananin b'acin rai "Zaituna Wanan wane irin rashin kamun kai ne da rashin hankali da zaki biyoni har Majalisa mai yasa bazaki jira na dawo gidan ba har sai kin biyoni kinsan kuwa kuwa halin 'yan Majalisar mu kuwa ni nasan  yau kuma basu da hirar da ya wuce namu"

Kuka Zaituna ta rushe dashi tana "Haba Abubakar ya bazan biyoka har Majalisa ba matarka da yaranka suna neman sabauta ni har ruwan cikina fa Hadiza ta hau ta ringa zuba min naushi inda mama Amina ita kuma ta cilloni waje to idan banzo na fad'a maka ba gidanmu kake so na tafi fissabillahi ni wlh Dana san haka halin matarka yake da ban soma auranka ba ni danake da samari marasa Mata amma na dage nace kai nakeso na aura tun ba'aje ko'ina ba ka fara gwadamin halinku na maza har kana cemin Mara hankali babu komai muje gidan ka bani takadata ace yau kwana na biyu har na fara cin duka awane dalili".

Abubakar tuni kalmominta suka kashe masa jiki da tace tana da samari ta dage ta aure shi inda Zaituna kuwa ta cigaba da kukan Munafirci tana yarfa Majina.

KUKAN KURCIYAWhere stories live. Discover now