page 2

4.1K 330 17
                                    

® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L*💭💭💭

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035

*KUK🅰AN KURCIY🅰🐦🐦🐦*

*Written by*
*💅💅SADNAF💅💅*

*page 2*


Zuhura mata ce ga Musbahu 'yan uwan juna ne Aka had'asu Auren Zumunci Musbahu wani katon super market gare shi dan har distributing kaya yakewa masu k'aramin shaguna ana wa super market d'insa lak'abi da k'aramin singer Mutum ne shi mai kudin gaske haka zalika abun hannunsa bai rufe mishi ido ba mutum ne shi mai balain saukin kai da hakuri dan Sam bashida hayaniya hakurinsa yasa yake Zaune da Zuhura dan Zuhura ba ita yake so ba dan dai an had'asu ne dama aka had'asu Zuhura bata da hallayen da ake so kowace mace ta kasance tana dashi

Zuhura Sangartaciyar mace ce mai bala'in san jiki dan akaran kanta wanka wahala yake mata ballantana azo akan aikace aikacen gida dasu girki a farkon Aurensu ba k'aramin wahala Musbahu ya sha ba dan bai ma san yanda zai kwatanta san jiki da kaz'antar Zuhura ba babu yanda batayi dashi akan ya samo mata 'yar aiki ba yak'i domin tunda aka had'a baki da 'yar aiki aka cutar dasu yasha alwashin babu shi babu 'yar aiki a gidansa Musbahu idan yafito daga gidansa har wani nishad'i yake ji na shigarsa dan kwanciyar bacci kawai ke kai shi gidansa shima d'akinsa idan ya gyara kullewa yake da mukulli girkinta kuwa ba Kullum yake samu yaci ba dan sai ta kusa awa uku tana dafa abinci inda shi kuwa Idan yaga bazai iya jira ba sai yayi tafiyarsa hakane yasa wani zubin kafin ya dawo gida yake cika cikinsa ahaka suke zaune har Allah ya azurta su da yara uku Laila Mus'ab da jawad inda yake tunanin haihuwa zai iya sakawa ta canja amma ina tana nan ayanda take idan taga aiki ya jagule mata sai ta kira makota su tayata aiki ta basu kud'i Abu d'aya dazai fi baka mamaki shine wani irin dan banzan bacci da take dashi na asara dan idan tana bacci tsaf zaka saceta batare da tasani ba a kullum bata da aikin daya wuce Kallo da bacci chatting kuwa bai dameta ba ahaka su Laila suka taso da rashin kulawar uwa duk da babu abinda suka nema suka rasa dan har sai dai su bawa mak'ota kyauta laila tun tana da shekara biyar ta fara yiwa kanta wanka da kuwa ta cika shidda ta fara had'awa da kanenta tana yi musu Abu d'aya daya taimakesu shine suna da mai musu wanki da guga shi yasa ko da yaushe zaka gansu fes suna kuma da Almajirin da yake musu wanke wanke da shara da mopping duk da ba iya wa yayi sosai ba dan shima yarone ba wani babba ba ga gida iya gida amma rashin gyara yasa ya fita hayyacinsa Musbahu Sam bai san da zaman Almajirin ba dan mai wanki kawai da guga yasani.

Zuhura zamu iya kiranta da ballagaza wacce bata san ciwon kanta ba dan ta sakarwa Almajirinta Babawo fuska fiye da tunanin mai tunani dan babu inda baya shiga a cikin gidan har d'akin baccinta Dana yara b'angaren mai gidan dake sama ne kawai bai tab'a shiga ba dan shima kullewa yake idan zai fita da har can zata iya Aiken shi banda uban Satan da yake mata na kayan abinci da kudi duk abinda ransa ke so shima yi kawai yake a gidan.

Zuhura zata iya kwana biyu da kaya d'aya batare da wanka ba
ba kuma kayan ne bata dashi ba tsabar lalaci da k'azanta ke sata haka idan dai kaga Zuhura Tayi wanka tayi kwalliya to ka tabbata unguwa zata tafi wanan san Jikin nata da San baccin masifa yasa bata iya yiwa yaranta girki idan zasu tafi makaranta ta gwammace ta basu raw indomie ko cornflaskes ko ta bawa kowanensu k'aton bread ya tafi dashi makaranta dama laila ita ke shirya k'anenta dan tun bama ta iya musu wanka su fita ba har sai da tazo ta saba idan Mahaifinsu ya tashe su da asuba basa komawa bacci dukansu Zuhura kuwa d'akinsu take dawowa tayi kwanciyarta sabida kar Musbahu yagane sai sun tafi take fitowa dama ta saba Musbahu da sassafe yake fita dan wani zubin yana Riga su laila fita ta hakane yasa bata da tashin hankalin abinda zata bashi yaci idan zai fita a duk lokacin da ta tashi idan Babawo Almajirinta yazo zai musu wanke wanke sai tace ya d'an dafa mata indomie taci idan kuma bata ra'ayin indomie zata had'a bread da butter taci da shayi mai kauri girkin dare kuma ko ta kai makota ayi mata ko kuma ta kira ayi mata har cikin gidan rayuwar da Zuhura keyi kenan acikin gidanta wanan kenan.

KUKAN KURCIYAWhere stories live. Discover now