page 16

3.9K 412 28
                                    

® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L*💭💭💭

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035

*KUK🅰AN KURCIY🅰🐦🐦🐦*

       *Written by*
*💅💅SADNAF💅💅*


*Wanan shafin sadaukarwa ne ga dubanin masoyana masu karanta kukan kurciya  Masoyana Real Sadnaf Fans Sadnaf true fans Masoyan P.m.l Kundin kaddarata Fans Basmah er lele grp Zauren biebie isa Sadnaf novels Sadnaf Hausa Novels kai da grp dayawa dayawa da idan nace jerosu zanyi Zan  iya kwana ban gama  ba Maman Sadiq ban mantaki ba Biebie d Ummu Muhseen mai kuka idan banyi posting ba da duk grps Admins d'ina Ga page 16 Nan kyauta kuyi yanda kuke so dashi*

*page 16*

B'angaren Zuhura kuwa tashin hankali da take ciki ada Nafila ne akan  Wanda take ciki yanzu Dan k'arfi da Yaji Musbahu ya rabata dasu Mus'ab ta hanyar d'aukesu daga gaban kakarsu tunda  yazo ya ritsata watarana  dataje ganinsu duk da har lokacin Mus'ab gudunta yake Jawad kawai ke Zuwa wajenta shima da k'yar.

Har wajen motarsa tabi shi a guje tana kuka Tana ya yafe mata kar ya rabata da yaranta amma ina Musbahu a Zuciye ya finciketa daga jikin Motarsa ko kad'an bai ji tausayinta ba dan itama bata ji Tausayin Laila ba.

A haka ta ringa bin Motarsa yana tafiya tana k'walla kiran Sunan Mus'ab da Jawad har sai da ta kasa tado motar.

A kasa ta Zub'e ta ringa kuka kamar ranta Zai fita dan sosai take jin kaunar yaran nata har a Zuciya yanda take jin ta zata iya hakura da komai a rayuwa banda yaranta.

A haukace ta kara komawa wajen Fulani Mahaifiyar Musbahu ta zub'e agabanta tare da rik'e mata k'afafuwa akan ta taimaka mata ta kira Musbahu ya dawo mata da yaranta dan su kadai take gani taji dadi.

Tsananin tausayin Zuhura yasa Fulani kiran Musbahu a  waya amma fir ya k'i daga wayar dan yasan abinda yasa take kiransa.

Kuka Zuhura ta ringa yi sosai kamar zata shid'e Wanda har sai da Fulani ta sa driver ya maidata gida dan birkice mata tayi akan babu inda zata je sai Musbahu ya dawo mata da yaranta.

Babu irin ban baki da rarrashin da iyayenta basu yi mata ba akan ta kwantar da hankalinta Musbahu zai dawo mata dasu yanzu fushi ne yayi.

Amma Zuhura Sam tak'i kwantar da hankalinta ta maida kuka sana'arta zuwanta Gidan Musbahu hud'u amma mai gadi ya hanata shiga gidan dan da kakausar murya Musbahu yayi mishi gargadi akan duk ranar da Zuhura ta zo gidan ya barta ta shiga a bakin aikinsa.

Tuni kulawar su Mus'ab ya koma Hannun Musbahu ganin ba a karkashin wani yake ba shine ogan kansa da kansa yake musu wanka ya musu girki dan ba laifi ya iya girki tunda boarding Yayi  da kansa yake kaisu makaranta  kafin ya fita sai ya d'ora musu Na rana sai ya saka a flask  ya kaiwa Maman Baby da Uniform d'insu akan idan sun dawo suci su tafi islamiyya kafin su tashi daga islamiyya zai dawo idan ya dawo sai ya kara musu wanka sai ya tafi dasu shago.

Anan zai kai su restaurant suci abincin dare su yi kallo a shagon idan sunyi bacci sai ya kaisu wani waje a shagonsa da anan yake hutawa idan ya tashi kuma sai ya d'aukesu su tafi gida.

Sosai yake basu kulawar da basu Samu ba awajen Mahaifiyarsu yake kuma  so ya kuma mantar dasu Laila data zame musu uwa duk da yasan abune mayuwaci Mus'ab ya iya manta Laila  dan har yau ba dai dai yake ba yana nan shiru shiru yasha farkawa daddare yaga yabar kan gadon da suke akwance dan tare suke kwana inda hakan kansa ya sauko k'asa anan zai tarar da shi a d'akin Laila ya rungume Teddynta yana bacci hakan kansa ya zubar da hawaye dan tsananin tausayinsa ahaka zai d'auke shi da teddyn ya mayar dashi d'akinsa ya kwantar.

KUKAN KURCIYAWhere stories live. Discover now