page 23

2.8K 373 79
                                    

® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L*💭💭💭

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035

*KUK🅰AN KURCIY🅰🐦🐦🐦*

       *Written by*
*💅💅SADNAF💅💅*

*FOLLOW ME ON WATTPAD@SADNAF*

*page 23*

         "Abubakar ai banida Nonon da zan bata kai ma kasani rabona da shayarwa yanzu wajen shekara bakwai kenan ko da ma ina da Halin da zan shayar ya za'ayi na shayar da jaririyar Alhalin tana da uwa a raye ai babu Wanda ya cancanci ya shayar da ita sama da Mahaifiyarta data tsugunna ta haifeta dan haka aganina kaje ka lallab'a ta  ta shayar da ita".

" Amina ba dole sai kin bata nono ba ko Madara ne dan Allah ki taimaka kirnga bata tunda kika ga  ta kawo min jariryar wlh ko mai zanyi bazata shayar da ita Ba kema kinsan Halinsu da rashin mutuncinsu wlh bakiga cin mutuncin da kakarta tamin ba sai da ta Tara min jama'a a bakin shagona yau Dan girman Allah ki rufamin Asiri badan Halina ba kuma dan Halin Mahaifiyarta ba wlh nayi nadamar abinda nayi miki ina kan nadama ma tunda bawa bai isa ya kaucewa kaddararsa ba."

Abubakar yace kamar zai yi kuka

Kukan da jaririyar ta fara tsallawa ba kakautawa ne yasa Firdausi nufar d'akin da sauri su 'yan Biyu dasu  Mus'ab suka bi bayanta.

Abubakar kuwa ya mik'e a rude cikin tsananin tausayin jaririyar da bata ji ba bata gani ba bai tab'a tunanin Rashin Imanin Zaituna ya kai haka ba sai Yanzu da ta kawo 'yar data tsugunna ta Haifa ko damuwa batayi da Halin da zata shiga ba.

Hannu yasa ya k'arbi Jaririyar yayi hanyar fita daga d'akin dan ya gama fidda rai Akan Amina zata k'arbi Jaririyar dan tunda ya fara magana bata d'ago ta kalleshi ba Jarirya kuwa har muryarta ya dashe tsabar kuka.

Yana dab da ficewa daga d'akin ya juyo muryar Amina tana  "Kawota"

Cikin tsananin farinciki ya dawo da Sauri tare da mik'awa Amina Jaririyar.

Amina ta k'arbi jaririyar da Bismillah.

Abubakar kuwa ya hau jera mata godiya.

Amina bata ko kalleshi ba ta goya yarinyar a bayanta tace ya siyo madara da kayan jarirai madarar ma irin Wanda ake bawa Jarirai.

Abubakar jiki na Rawa ya fita waje yana mata godiya.

Amina kuwa ta fita taje ta d'aura ruwan Zafi kafin kice me Jaririyar tayi luf a bayanta.

Tana cikin yiwa jaririyar wanka Abubakar  ya dawo da kayan Jarirai Niki Niki feeder pampers Madara  da duk wani Abu daya danganci kayan Baby.

Cikin minti Ashirin Amina ta shirya Jaririyar ta had'a mata Madarar sai data sha feeder biyu ta d'auke bakinta.

Amina ta kwantar da ita Abubakar na daga gefe yana ta kallonsu Yana yiwa Amina addua a zuciyarsa dan yasan samun mace irinta a Wanan zamanin sai an tona.

Amina a gefen Jaririyar ta kwanta Abubakar ya mik'e yana "Nagode sosai Amina Allah ya biyaki da aljannatul Firdausi Na sawa  Yarinyar Suna  Aminatu"

"Allah ya rayata"

Kawai Amina tace ta lumshe idonta.

Abubakar kuwa yafita waje.

Tamkar 'yar cikinta haka Amina take kula da Meena 'yan biyu dasu Mus'ab kuwa sai murna sukeyi sunyi kanwa mai kyau dan har lokacin Su Mus'ab basu koma gida ba aranar da Ta cika Sati d'aya Abubakar ya yanka rago Akayi Radin Suna a Massallaci.

KUKAN KURCIYAWhere stories live. Discover now