Part 2

5.3K 303 64
                                    


____TAGWAYE BY BASMA_BASHIR

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

Flashback

Sun taso cikin tsananin talauci da y'unwa...
A garin Maiduguri sukeda zama, dashike Alhaji Isma'il cikekken d'an 'kabilan Shuwa Arab ne, hakan yasa dawuya ka banbantasu da Larabawa. Saminu da Sambo suna da mugun kamanni wanda duk duniya babu mai banbantasu se mahaifinsu Alhaji Isma'il.
Tsana'ar tsa 're iccenda Malam Isma'il keyi yake taimakamusu suna iya ci so biyu a rana wataran so d'aya. Tun kamin rasuwar mahaifiyarsu burinta shine tsakanin Y'an biyun nan nata d'aya daga cikinsu yayi karatun boko kuma yasamu cikekken ilimin boko mai anfani, 'Dayansu kuma yasamu cikekken 'karatun Arabiya mai anfani.

Hakan yasa Malam Isma'il yayi tseyin daka da tsana'o'i iri daban daban sabida yayi kokarin cika burin marigayiya (Matarsa) kuma mahaifiyar y'ayansa.

****
Shakuwar dake tsakanin Saminu da Sambo shakuwa ne wanda ko a tarihi babu wanda yata6ajin y'an uwa irinsu, Saminu ya so d'an uwansa Sambo fiyeda yakeson kansa domin ko'da ya kwan biyu baisa abinci abakinsa ba bazata dameshiba dazaran Sambo yana samun abun ci da sha. Hakama Sambo kwata kwata bai damu da kansaba ako yaushe burinsa shine yaga d'an uwansa Saminu cikin firin ciki da annashuwa.

Shekarunsu goma sha biyu aka rabasu, inda Malam Isma'il yakai Saminu karatun almajiranci achan garin Nijer, Sambo kuwa yacigaba dazama tareda mahaifinsa yana zuwa makaranta.
Tun yana kukan rashin d'an uwansa har yadena da lokaci suka tafi, Akwai shi da 'kokari a makaranta, duk malaminda ya tambayesa dalilin da'gewarda yakeyi kuwa cewa zayyi yana 'kokari ne ya kammala karatunsa yayi kud'i domin yaje garin Nijer yanemi d'an uwansa Saminu.

Ana_nan ana_nan Sambo yakammala karatun sakandari.
Suna shirin tara kud'in zuwa jami'a tsausayi ta riskesu, Malam Isma'il yayi hatsarin Mota acikin gari, nan ta ke bai kara minti d'aya ba yabar duniya.

Alhaji Sambo yayi matukar kukan rashin iyaye da rashin d'an uwansa Saminu domin bayan rasuwar mahaifinsu yatafi kasar Nijer sama da kasa ya nemeshi amma babu alamarsa.

********
Da ga'don mahaifinsa yacigaba da karatu har zuwa karshe, inda yayi nasaran samun scholarship zuwa 'kasar Amurka ta tsakiya, anan yakammala 'karatunsa har zuwa PHD.
Yafara kasuwanci mai zurfi cikin Amurka, Lokaci na tafiya kasuwancinsa na 'kara bunkasa har yafara aika kayansa zuwa kashashe daban daban, yayi suna a duniya babu wanda baisan Alhaji Sambo Isma'il Maidugu ba sabida yawan confanunnukansa dakuma 'kayansa dake shiga dafita cikin 'kasashen duniya.

***
Kasuwanci ce tahad'ashi da Safeenah Y'ar wani balarabe a garin Jiddah dake birnin Saudi Arabia, Soyayar shekara guda sukayi sannan aka d'aura musu aure suka dawo Nigeria (Abuja) dazama. Sun shafa tsahon shekaru Allah bai basu haihuwa ba, likitocin duniya duk sun dubasu amma babu wata mafita. Chan... Wani abokin kasuwancin Alhaji Sambo ya kwatanta masa wani kwararren malami dake 'kauyen Agadas wanda aikinsa yake tamkar hankan wuka, Magani kurun zai basu kuma da yardan Allah daga nan sun rabu da matsalar rashin haihuwa har abada.
Alhaji Sambo ya gamsu da maganar abokinsa, Washe gari suka shirya tareda Safeenah zuwa garin Agadas tareda Abokin nasa Muktar.

Garin agadas tanada nisa matuka, sunsha hany'a kamin su Kai 'kauyenda Muktar ya kwatanta musu. Amma abun mamakin shine wanda sukatarar amasayin malamin.

****
Suna isa sega d'an uwansa Saminu yafito cikin wani d'akin bukka. "Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun Saminu ashe rai kanga rai" Alhaji Sambo ya dafa kai cikin rud'ani, yayinda yake faman share hawayen dake kokarin zubomasa.

Littafin dake hannun Malam Saminu ne yafad'o kasa inda yafara zubar da hawaye Shima
yana kokarin komawa cikin bukkansa. Damke hannunsa Alhaji Sambo yayi, A wannan lokacin ya ka 'sa rike hawayensa zubowa suke tamkar lalataccen fanfo "D'an uwana baka ganeni bane? "

Tagwaye (Identical twins) Where stories live. Discover now