PART 4

4.2K 217 19
                                    

_______TAGWAYE BY BASMA_BASHIR

Bankad'o kofa yayi yashige kamar daga sama yafad'o, da ka 'ga fiskarsa akwai alaman damuwa da 6acin rai. Muryarsa na karkaruwa ayayinda yafara ambatan sunan Matarsa "Safeenah, Safeenah ina kike neh, Safeenah"...

Shigowarsa keda wuya, yayi Kacibus da Safeenah, yayinda take ko'karin bud'e masa kofan d'aki; "Baban Ma'isha Lafiya kashigomin d'aki haka ko sallama babu? Ta fad'a a tsorace.

Ta6e baki Alhaji Sambo yayi ya fiskanci gabas yanacewa "Ya Allah wani irin laifi na'aikata kake sa'kamin da wannan hukuncin, Ya Allah kagafartamin duk laifukan dana aikata maka".
Zuciyarsa ce ke tafasa, idanuwarsa suna kwalla wanda kan nuna tsananin rad'anin dayake damunsa a zuciya.

Tseyawa Safeenah tayi Jugumm tana binsa da kallo da idanuwar tausayi tace: Mijina yau kuma dame kazo da ita? Ko dei matsalar tsakaninka da Yaya Saminu ne? Tafad'a cikin sanyin murya.

"Safeenah, matsalar Y'ar muce Ma'isha, munyi kuskuren tarbiyantar da ita tun afarko gashi yanzu muna samun sakamakon, Imagine Y'ar da muka Haifa ta gagaremu ta fi 'karfin mu kuma ba ta Jin maganar mu. Safeenah wannan wani irin rayuwa neh? Yafad'a cikin sanyin murya da fiskan tausayi.

Matsowa Safeenah tayi har kusa dashi ta rike hannayensa tanacewa; Ma'isha bata gagaremuba kuma ko kad'an bamuyi kuskure wajen bata tarbiya ba, ka tuna Ma'isha jinin mune kuma mun haifeta da larura yakamata mu ringa binta a hankali har zuwa lokacinda zata mallaki hankalin kanta domin ita yarinyace yakamata ka fahimceta.

Mikewa yayi wuf!, yahad'a da ajiyar zuciya yanacewa: Saukowata daga jirgi Gidan Ma'isha nawuce inda na tsameta tareda wani shashashan yaro wai shi saurayinta, suna zaune su kad'ei suna soyyayya na yi kokarin janyota mudawo gida amma Ma'isha ta nunamin fin 'karfi, jefoni tayi awaje tayi cikin gida...

Awannan lokacin Safeenah ta 'kasa rike hawayenta, kai tseye tabarsu suna zuba iya san ransu....

     **********************

Ata 6angaren Ma'isha kuwa a kwance take kan gado tana rusa kuka tareda da'nasanin abubuwanda ta aikatawa Mahaifinta, Sedei babu yedda zatayi hakan shine kawai zai iya taimaka mata gamida zancen komawa Gidan Daddy, duk dacewa tana kewar Momcy sosai an Kwan biyu Momy Bata ziyarcetaba, Kuma har ga Allah tanason ta ziyarcesu Amma babu Hali. Wannan dalilin yasa take dad'a tsanan Ma'inah Wanda a tsanadiyarta ne ta rabu da dukkan Farin ciki a rayuwarta, ta rabu da Daddy dakuma Momcy.

Da wannan tunanin na 6acin Rai da bakin ciki Ta mike Kai tseye tawuce bathroom anan ta wasa ruwa a jikinta tafice zuciyarta na tafasa ta zauna gaban Mirrow.
Fiskar dake fiskantar ta cikin Madubin yasa tasa kafa tarusa ta Pakzzzz... madubin ta watse tsakar d'aki. Inda ta zube 'kasa tana rusa kuka  mai kona zuci "Ma'inah meyasa kike biye da rayuwata? Meyasa kika shiga rayuwata, Why? Na tsaneki Ma'inah why do you have to take everything from me why Ma'inah? Har madubi idon na duba fiakarki nake gani, Ma'inah you are my worsed enemy I hate.

Bata taso inda takeba, tasa hannu ta lalu6o wayarta dake saman drawer, inda takai layin Hamza Scissors. (abokinta) A bugu d'aya ya d'aga wayar "Maisshhhhh Ya akayi toh?

Sanda taja doguwar nunfashi Sannan tace; Scissors kahad'a y'an gidanka da kungiyar su Suratu kuzo gidana na shirya mana party.

"Party Kuma Hajjajo? yau Kuma me yafaru? Na san abokiyar tawa ba ta shirya mana chasu se in ranta ya 6ace. Ma'ishhh waya ta6omin ke neh?" Scissors yayi responding cikin muryar Kulawa.

Kuka Ma'isha tasaka tareda cewa; Scissors it's Ma'inah she is trying to distroy my life Don Allah kuzo I really want to drink shiyasa nashirya mana chasun zamu shakata sosai.

"Calm down Friend I will always be here for you karki damu zamu kawo champagne iya son ranki".... Da wannan magana Scissors ya katse wayarsa, Ma'isha kuwa se yanzu jikinta yayi karfi, inda ta taso tashirya cikin wata Y'ar guntun Riga mai filawowi Sannan ta rangada kwalliya kamar yedda tasaba.

Tagwaye (Identical twins) Where stories live. Discover now