ASSALAMU ALEIKUM🎤📢 FANS📢🎤
😘H*E*L*L*O * F*A*V*O*U*R*I*T*E*😘
❤️❤️❤️❤️❤️👂👂👂👂
👇👇👇
(KU GYARA ZAMA
KU nitsu, ku Karanta
👇11,628 WORDS 👇)SORRY. NOT. EDITED. PLEASE BEAR WITH ME.....
***❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️***
"This house looks empty without our Twins, I wonder where they are right now, I miss them already.
Mummy ce taketa mita, tun tuni Yaranta suka fita basu 'kara dawowaba har izuwa wannan lokacin da magriba takawo kai. "Anya lafiya kuwa? Umma na murmushi tace' Haba Hajiya Safeenah yara da girmansu, bai 'kamata ki dourawa 'kanki damuwa haka ba, zasu dawo mana kwantar da hankalinki, lafiyarsu kalau.Murmushin Mummy ta maidamata" Maganar ki gaskiyane Umma sedei kuma azahirin gaskiya banson yarana suyi nesa dani sabida kamar yedda kikasani mugaye masu ki'shin yarana sunada yawa a gari, kamar Maisha for example, you know we can't trust this brat at all.
Babu Shakka Umma taji zafin wannan maganar sedei kuma ko kad'an ba'tason Mummy ta fahimci hakan, Share hawayenta tai tana murmushin 'karfin Hali, ta gyad'a kai" Hakane'. Har cikin zuciyarta takejin rad'adi idan ta tuno da irin munanan halin 'Yarta Maisha, sedei kuma wataran takan batsar da tunanin sabida idan ta dade tanayi, nan da nan zuciyarta zata iya bugawa ta mutu. Yawan tunanin Maisha da Mijinta ya haifarmata da matsaloli iri iri kamar hawan jini da ciwon zuciya, kullum cikin fa'ma take, tana zirga zirga a hany'an asibiti.
Irin hawayenda suke gangarowa a idanun Umma wanda ita 'kanta batasan dasuba, Yasa Mummy ta fahimci cewa wannan maganar datai ne ya 6atamata rai. Dasauri ta share mata hawaye "Ki ga'fartamin, banyi maganar daniyar 6atamiki ba, wallahi ni kaina kusan kullum nike hawaye sanadiyan Maisha sabida aganina laifina ne, na d'auramata dukkan soyayya ta da kula har idanuwata suka rufe, kunnuwa ta suka toshe, Ban nunamata hany'an kwarai ba. Binta nake a Sannu tamkar jinjira duk abinda takeso shi zata aikata, muna rashin jituwa sosai da Mijina a sanadiyan Maisha har Mijina ya'kusan maidani gidanmu. Kinga kenan ni ce na lalatamiki yariny'a, Ban bata tarbiya ba, shiyasa ta sauya daga Maisha'nki takoma wata daban, Dan Allah ki gafartamin Umma, Wallahi bazan ta6a yafewa 'kaina ba because you owe me a lots, ke ce kika shayarda yarana dukkansu biyu suka samu lafiya kuma suka girma gwanin ban sha'awa, Amma ban sa 'ka miki da komai ba face zunzurutun takaici da bakin ciki.
__Y'ayanmu zakice sabida har abada Ma'inah da Miemah amasayin y'ay'an ciki na na d'aukesu, Musamman ma Miemah zan iya rabuwa da kowa amma banda ita, mun shaku da juna fiyeda tsammaninki.
Ganin irin hawayenda suke sau'ka a idanun Mommy dakuma sananin tausayinda ke bayyane a fiskarta yasa Umma ta mike dasauri ta rungumeta" Ba laifin ki bane Safeenah, Kuma bazan ta6a tuhumar ki da ita ba, Saminu shine sanadiyar lalacewar tarbiyan 'Yata kuma bansamman akwai ranarda zan gafarta masaba. Kamar yedda turawa suka fa'da "Like Father Like Daughter" a jini yake, Maisha tayo halin Mahaifinta sak! Halaiyarsu babu banbanci.Sam hankalin Mummy ba'ya kan maganganun Umma, shiru tai tana tunani, Bata ta6a sammanin cewa karshen Maisha zata zamto babu kyaun irin hakaba, sabida ako da yaushe tunaninta da burinta shine Maisha tayo farin jinin Mahaifinta yakasance kowa na santa, Kuma ta kasance mai tsoron Allah da taimako.
***💓**💓**💓**💓**💓**💓***
Sai yanzu suka 'karaso Dr_Manav Alsiddique_Mansion bayan tafiya mai nisan dasukai. Hajiya Turai takaraima gidan kallo sannan tafashe da kuka, dama chan kukan takeyi sedei ahankali take zubda kwalla sai yanzu tafito a bayyane.