PART 11

2.8K 166 11
                                    


______TAGWAYE BY BASMA_BASHIR

Likita dafatan 'Dan uwana zai war'ke, Doctor kada'ge iya bakin kokarinka domin kaceci ran Sambo shi kad'ei yaragemin ba'nida kowa bayansa. 
Dawannan maganar Saminu ya 'Karaso, nunfashi yake sama sama yana waiwaigawa ko zaiga Safeenah a wajen,. Se yanzu tadawo bayan fitowa datayi kar6an magani gun likita. Agogon hannunta taduba yanzu 'karfe Hudu kenan ta asuba amma babu alamun chanji tattareda mijinta tun fad'owar dare yake cikin yanayin Su'ma har izuwa yanzu, likitoci se aiki suke akansa tun zuwarzu, harma suka dena suna jiran iko gun ubangiji.   Alokacinda aka kawosa asibiti, Safeenah ta'kira Saminu a waya tafad'a masa yalinda suke ciki daganan yabi ya ra'zana ko kad'an bai 6ata lokaciba nan take yai urgent flight yazo Abuja a daren.

Se yanzu likita yatashi jikinsa duk tayi sany'i ya rasa wace irin suma Alhaji yai, duk dabarunsu na likitoci yayi amma babu motsi "Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun'  iya abunda yafurta kenan sannan yami'ke yana tafiya.  "Meye kake nufi Bawan Allah taya zakabarmu a duhu?" Saminu yarike hannayensa dika biyu yasake Kunnuwa, baki harma da ido yana jiran amsarda likita zai basa.

I'm sorry munyi iya Bakin kokarinmu amma har yanzu dei babu wani chanji Sedei mujira nanda awa biyu zuwa uku, idan yatashi toh falillahil hamdu idan Kuma bai tashiba dukkanmu musulmai ne kuma munsan ma'anar Ayan "Kullu nafsin Za'iqatul Maut".    Kallonsa Saminu yake Jugumm har tseda ya kammala maganarsa yatafi sannan yafara zubar da hawaye shima yabud'e kofa yafita.

**
Mutuwar tseye Maisha tayi alokacinda tahango likita yafitce daga d'akin Asibiti cikin damuwa tareda Kawu_Saminu duk alokaci d'aya, 'This can't be, Innalillahi wa Inna ileihi rajiun' kwanon abincin dake hannunta ta6arar, ta'kama Salati tana hawaye masu tsananin zafi 'Lailaha illahu Muhammadu Rasoulul Lahi (SAW) Daddy I'm sorry su6ucewa maganar tayi Allah ma yasan ba'nida niyar 6ata maka rai kawai dei gaskiya nafad'a, Kwata kwata Ka dena kula da Mahaifiyata nikuma Momcy itace komai arayuwata bansan naga ranta ya6ace, I'm so sorry Daddy I love you so much kar'ka tafi kabarni.

Ita kad'ei take magana tamkar mahaukaciya mutanen asibiti se kallonta suke, Bata kula kowa ba se 'kara murya take hawaye suna zuba babu control "Ma'inah " Tafad'a ahankali sannan tashare hawayen dake fiskarta nan ta 'ke tachanza ido inda ta wainasu sama tareda turo Baki gefe, tasau'kar da gira "A tsanadiyar ki mahaifina yashiga wannan halin, yanzu haka rai a hannun Allah, Ma'inah I will not spare you, Wallahi you must pay. Ba'a shigan gonata a kwana lafiya Ni Maisha wuta ce mai balballa wacce ruwan banza ba'ta kashani, Ko da 6angon duniya Daddy ya 6oyeki wallahi Maisha Ra'min kurege ce takan tone ko ina a duniya.

Murmusawa tayi alaman wani tunani ne yazo mata sannan ta gyara gashin 'kanta fiskarta cikeda fara'a yayinda tafara tafiya "Dear Twin Sis zamu had'u a office gobe kuma wallahi se kin gwammace sanina dakikayi a duniya Ma'inah Sambo Maidugu."

Tafiya take ahankali a hankali tana tunani iri iri, se murmushi take tana waina idanu, Hangan Mahaifiyarta datayi yasa tadawo cikin hayacinta dasauri ta'karaso inda take "Momcy lafiya meye yasa kike barin Daddy shi kad'ei Ina kuma Zaki? Tafad'a cikin nunfashi d'aya.   
Ma'isha Daddy ya farfad'o yi maza ki'kira likita zankoma wajensa. Momy takatseta sannan takoma d'aki. Bata 'kara cewa komai ba juyowa tai kurun babu inda ta tseya se  ofishin likita.

      ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

Bayan ta idar da Sallan asuba tareda yin nafiloli, ta 'karanta Al Qurani mai girma Sannan tamike atsorace tabud'e tagar d'akin tana lekowa, Shiru babu kowa awaje se y'an Sanda masu Bakaken 'kaya suna wayon gadi. 
"Gida sekace ta shugaban 'kasa" Ma'inah tasa ke murza ido tana ganin d'akin datake ciki, mamaki take tayi tun shigewarta wai duk wannan makaken d'akin na tane ita kad'ei ai ko d'akin Mai martaba Sarki ba ta 'kai haka.

Tagwaye (Identical twins) Where stories live. Discover now