PART 15

2.8K 159 13
                                    


Assalamu Aleikum Wa Rahmatul Lahi Wa Barakatuhu Dear Sisters and Brothers Thanks you so much 4 voting and commenting in d previous chappy 😍😍😍❤️❤️❤️

**************


____TAGWAYE BY BASMA_BASHIR

ENJOY 👇👇👇

"Hajiya babu wata matsala jikinki ya warware, Sedei akiyaye gaba kada kisa'ke kai kanki ga fad'a ko hayaniya irin haka, Oga ya bamu umarni cewa mu gargadeki mukuma ja miki kunneh sosai da sosai, sabida acewarsa bakya Jin maganarsa ma barre kikar6i shawararsa, Amma gskya in asan samunsa ne kada kisa'ke ziyartar gidan Alhaji Sambo don gudun wata matsala makamanciyar wannan.
Da'idanun mamaki Ma'inah take kallansa har tsanda haushi ya addabeta sannan tadakatar dashi "Sabida kawai sunansa Zaid. Tafad'a abayyane sannan ta'kara ta6e baki tanacewa "Wai meye damuwarsa da lafiyata ma tukunna bayan duk wannan cin zarafin dayaimin cikin bainin jama'a ya6atamin suna wai ni Ma'inah Sambo Maidugu Karuwa Kuma Y'ar Shaye shaye, how dare him, He is the worsed person I've ever known. Cikin hawayen takaici ta'karasar da'kalaman nata "Wallahi kuma duk wannan shirmen dayake faman yi ba zazuyi aiki akaina ba sabida har abada ba'zan yafemasaba, I hate him. Nan ta'kafe muryarta tafara dashi_dashi, inda ta'kara wata sabuwar hawaye tana tuna wulakancinda Zaid yaimata a office wanda ba'zata ta6a manta dashi' ba har zuwa karshen rayuwarta.

Shiruu likitan yake binta da kallo har tai shiru sannan ne yami'ka Mata takardan sallamarta daga asibiti batareda yatan'ka mataba haka yabar d'akin cikin rud'ani dakuma bin umarnin Zaid cewa komenene tafad'a akansa kada suhukuntata.
Zaid na la6e chan ba'kin kofa yana Jin duk abubuwnda take fad'i shima ransa na bala'in 6aci idan ya tuno wannan kuskuren dayai inda yawulakan Tata cikin bainin mutane a wajen aiki cewa ita Y'ar Shaye ce kuma 'karuwa. Abinda ke 'kara 6ata masa rai kuwa idan yatuna musabbabin faruwar hakan duk ba laifin kowa bace fa'ce Maisha Sambo Maidugu domin tun tuni yarigada ya tabbatar dacewa Maisha ce yad'auko abige yakai gidansa inda tai masa 'karya dasunan Y'ar uwarta. Wannan dalilin yasa yake dad'a tsanar Ma'isha aransa.

Doguwar nunfashi yasaukar sannan ya'kara da tsaki "Me yasa nake irin wannan tunanin, Zaid kadawo cikin hayacinka kuma kar'ka manta da alkawarinda kad'auko wakanka cewa bazaka 'kara yin soyayyaba har zuwa karshen rayuwarka, Muna is the only one you have, She is your responsibility Zaid wake up, Bakada hujjan tsanar Ma'isha a ranka sabida ita bakomai bace awajenka haka kuma zuciyarka batada hujjan San Ma'inah sabida ita kanta bakomai bace. Both the twins are good for nothing and useless ka'fi 'karfinsu Zaid.

CEO lafiya kake magana kai kad'ei haka? Maganar Asad ne yadawo masa hayacinsa, Inda Afirgice yagirgiza Kai "Babu komai I just don't care, Muna itace kadei kayamata zuciyata tatuna. Me yasa?Asad ya'kara tambayarsa cikin mamaki "Kodei akwai matsala ce? No babu komai as far as my daughter is safe babu kuma abunda zai dameni bayan wannan.

Dashike Asad ya sa' ba da halin abokin nasa Nan da nan yaga'ne tsarkuguwar dayai akan Ma'inah ce domin tun afarko ya rigada ya ga'ne cewa abokin nasa ya'fara San Ma'inah sabida babu wata macen dayake kula kuma yake yawan tunani bayan ita, Sedei yanada tabbacin cewa wannan shegen d'agin kan nasa dakuma abubuwnda sukafaru abaya ba'zasu ta6a barinsa ya gaskanta zuciyarsa har yafara soyayya ba. Da dukkan alamu kuma Ma'inah keuta ce daga ubangiji kuma itace zatayi tsanadiyar dawowar farin cikin Zaid Insha Allah. Da wannan tunanin Asad yai murmushi sannan ya'kara fad'an Insha Allah. A bayyane. "Asad are u ok kaima naga kana maganar Kai kadei Kodei akwai matsala ce? Dasauri ya girgiza Kai "No Dude go ahead kacigaba da tuna Muna after_all she is all you have.

Jinjina kai Zaid yai shima, jikinsa duk a tsargu yayinda yakecewa "You are right dude. Sannan yai shiru yafara bin abokin nasa da kallo Kuma. Babu abunda Asad ya'kara fad'i bud'e kofar d'akin yai Kai tseye yashige, shima Zaid haka yabiyosa duk dacewa ba'asan ransa yai hakanba. Shigewarsa keda wuya yafara tattara magungunan Ma'inah yanacewa; Miss tashi mutafi gida ya'kamata kisamu hutu....
"Asad tun jiya kake zirga_zirga cikin asibitin nan yanzu ya'kamata kakoma gidanku domin kasamu hutu d'awainiyar tayi yawa zakayi rashin lafiya, Za'muje gida tareda ita kar'ka damu. Zaid yakatseshi cikin nunfashi d'aya.
'Dan guntun murmushi Asad yai babu musu ya jinjina kai "Toh se'mun had'u kenan.
Yana fad'an wannan ya ijiye magungunan dama kamar jira yake akorosa babu sallama yabar musu d'akin kai tseye Yana amsa wayarda akayimasa.

Tagwaye (Identical twins) Where stories live. Discover now