Episode 2

842 35 0
                                    

MEENAL✨
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
EPISODE 2
Kallon Ahmad Hajia Saudat tayi ta dan yi murmushi Wanda da ka gansa kasan na yake neh, ta dan Kara turo daurin ta gaba, Ahmad! Sanin kanka neh irin son da daddynku yake yiwa mysha, baya Jin maganar kowa sae ta ta, yanzu haka zan sa ido Ina ji Ina gani yarinyar nan ta bar kasar nan, don Allah Ahmad kayi wani abu akai Ko legal neh ka nema mata tunda ta kafe ita Arabic take son karanta" ta fada Cikin shesshekar kuka. Zaro idanuwa Ahmad yayi alamar firgici yace "legal fah kika ce mummy, kin fa San halin yar ki Amma ki tuntubeta kiji"

Daddy bai shigo gidan ba sai gurin karfe 9 na dare, abinci kawae ya iya ci shima a gurguje saboda rashin ganin giftawar mysha, Ko ruwa kasa sha yayi ya dubi mummy "wae Hajia Ina mysha take ?" Ya tambaya yana mai kafe ta da idanuwa, "ni na rasa irin son da kake wa yarinyar nan, sai kace ita kadai gareka duk ka bi ka lalata ta yarinya duk ta sangarce....." tsawar da ya daka mata ce ta dakatar da ita daga karasa maganartaa, "banason wannan maganar tun ba yau bah na fada miki, zaki wuce ki je ki Kira min ita Ko kuwa?" Sumi-sumi Hajia ta mike ta nufi dakin mysha, Cikin mintinaaa kalilan suka dawo falon ita da mysha, sanye take da wata blue riga with black mini skirt, kamar yanda ta Saba kan nan nata babu dan kwali, da gudu ta rungume daddyn ta, "daddy tun yaushe ka dawo? Shine baka shiga ka ganni bah?" "Sorry my daughter da yunwa na dawo, albishirinki?" Ya fada yana shafa kanta, dagowa tayi babu shiri tace "what?" Gaban mummy neh ya yanke ya fadi, ta kasa gane dalili, a hankali ta samu guri ta zauna ta cigaba da saurarar hirar mysha da daddynta, abinda taji daddy ya furta neh yasa tayi saurin dafe kirji, ji tayi yace "maganar tafiyarki school, saudia ki shirya gobe by 1am jirgin zae tashi" Ae wani irin Ihu ta saki ta Kara rungume daddynta.

Washe gari tun karfe 1 na rana, aka gama hada mata kayanta, wani irin farin ciki take ciki Wanda bata taba shiga kamar sa bah, ita kuwa mummy fadin irin tashin hankalin da take ciki bata baki neh, kamar wasa time na wuce wa, it's 12:30am, mysha ta shirya tsaf Cikin wata pure plain black abaya, ga wannan farar fatar, in mutum ya ganta zae iya rantse wa balarabiya ce, nikam nace shadaudau! A hankali ta shiga dakin mummy, a zaune ta ganta Tana jan charbi, ta lallaba a hankali ta bi ta bayanta ta rungumeta, "mummy zan tafi" ta furta Cikin muryar kuka, Ni kaina bansan mysha nasan mummy har haka bah, haka sukayi sallama mummy na kuka mysha na kwalla har ta bar gidan, karfe 1:15 jirin su ya tashi sae Saudi Arabia, prince Muhammad bin abdulazeez Airport, medina.

Kwance Ammar yake yana Shan strawberry sae yaji kamar wayar sa na ringing a hankali ya kai lausassan hannunsa zuwa inda wayar take, sunan bestfriend dinsa ya gani yana yawo a screen din wayar, Cikin hanzari ya daga wayar "Assalamu Alayk 'afdal sadiq, kayf haluk" daga chan daya bangaren abokin nasa mai suna Maheer, yace "wa'alayk salam ya Ammar, Ana bi kyar, Alhamdulilah, Abid yana sama in the next 30 minutes zasu sauka, ka dauke sa please ka kaisa masauki and guide him through his registration anan school dinku neh, shukraan jazilaan, smiling Ammar yayi ya furta "Mafy Mishkilah Maheer!" Nikam da nake a gefe nace shadaudau! Bai tsaya wani bata lokaci bah, jallabiyar da ke gefensa ya saka ya dau waya ya fita.

Prince Muhammad bin Abdulazeez Airport, Medina ta cika makil, jiran fitowar Abid Ammar kawae yake, yana tsaye a jikin farar motarsa, ya hango abid yana dan  dube dube da alama shi ya ke nema, kafin ya karasa inda yake ya hangi wata balarabiya sanye da abaya, ta sha gaban abid, da sauri ya karasa gurin, wani sentence da yaji ta fada neh ya dakatar da bakin sa daga fara magana, ji yai tace "who the hell you think you're ? Are you blind?" Sam Abid bai gane avinda take cewa bah, "Assalamu alayk ya uktee, what are you saying please?" Nan ranta ya Kara baci, "I don't know, I said I don't know, before you said a word, look at this trolley, is this yours? Ta tambayesa Tana banka masa harara, murmushi Ammar yayi ya kalletaaa, simply because you mistakenly exchanged trolley with him that's why you're shouting like a mad person ? Don't you have manners? You should have talk politely....there she cuts him in...hold on! Don't dare interfere into my affairs, you said I don't have manners right? I will now prove to you that I am mannerless, kafin ya bude baki ta kifa masa Mari hade da cewa do you think you can mess with mysha? raggabrash! Ta fizge trolley dinta hade da barin gurin.

To be continued
Shadaudau Writers✨✨

Meenal Where stories live. Discover now