MEENAL✨
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
EPISODE 4
Meenal, na isa gida bayan ta gaisa da yan uwa da abokan arziki kai tsaye dakinta ta nufa, wanka ta fara yi daga bisani ta kwanta, juyi kawai take a gado bacci ya gagare ta, hannu ta sa ta dauko wayarta kirar iphone X ta dan fara viewing pictures on Instagram, Tana Cikin kallon pictures kawae sae taga Kiran ya Ammar ta FaceTime, Cikin hanzari ta daga, kwance ta gansa a kan gado yana lumshe ido, Meenal! Ya furta, murmushi tayi, nan yake tambayar ta inda take, yaga kamar dakinta na Egypt, take ta sanar dashi labarin zuwanta, sun dade suna waya, at last suka kashe.A kwana a tashi yau kwanan Meenal 6 a Egypt, shiryeye shiryeyen komawa gida take domin kuwa early in the morning jirginsu zae tashi, da kyar ta iya fitowa daga gidan Tana kuka suna kuka, da ace ta Kara 10 minutes bata fito bah, missing flight zata yi saboda tsananin son da take wa mahaifanta.
Zaune take a business class Tana tunani, meat pie da lappa lappa aka kawo musu, murmushi neh dauke a kyakkyawar fuskarta ganin wasu kyawawan yara suna kai kawo a business class, daga chan gefe wata farar mata sanye da abaya tace Ahmad! Sunan daya daga Cikin yaran kenan, da kaga faces dinsu kasan yaranta ne, Meenal dake kallon su ji tayi gabanta ya fadi, idanuwanta sun disashe, Ahmad neh kawae take tunanin zae iya haskaka mata su, jikinta ya mata lauyi, duk duniya babu avinda take son gani kamar sa, a ena zata gansa? Tambayar da takewa kanta kenan, shikenan ta rasa masoyinta! Bata Kara Ko motsi bah har suka isa Nigeria Kano state.
Tun bayan haduwar Ahmad da wannan kyakkyawar fuskar a Airport ya gaza samun sukuni, burinsa ya sake sa ta a idanunsa, for a week ya kasa gudanar da aikin da ya kai sa chan, cikakken abinci ma baya iya ci, tunani ya fara yi, gashi tare da ita da yaransu kyawawa masu kama da ita har guda biyar suna cin abinci, yana Cikin wannan tunanin neh bacci yayi gaba dashi.
Washe gari da safe, Ahmad ya shirya tsaf ya nufi Airport da niyyar Ko Allah zae sa ya ga Meenal, zuwa yayi daedae gurin da ta basa passport ya samu guri ya zauna har kusan awa 4 bai ga Ko me kama da ita bah, haka ya tashi gwiwa a sanyaye ya nufi gida.
A kwana a tashi yau satin Ahmad 1 yana zuwa airport Ko zae ga Meenal, Amma har yanzu shiru, ba dan yaso bah yau Wednesday ya hada kayansa ya bar kasar da niyyar zae dawo nan da sati daya Ko Allah zae sa ya ganta.
Tunda ya koma gida babu avinda yake iya aikatawa sai tunani, baya iya cin abinci baya iya bacci, kullun Cikin tunanin, tun abin baya damun mummy har ya fara damunta.
Bangaren Meenal kuwa tun da ta dawo, take tunani, ta kasa gane abinda yake damunta, bacci cikakke bata iya wa, da ta kwanta fuskar Ahmad take gani, kwance take tayi nisa Cikin tunani, hawaye neh ke bin kuncinta Wanda yayi daidai da lokacin shigowar Ummi, hankalin Ummi ne ya tashi "Limadha dafaly Yafky?" Ta tambaya Cikin kaduwa, kuka Meenal ta fashe dashi "La'aarif Ya Ummi" abinda ta iya furtawa
Kenan.Bayan sati daya da yin haka, Ahmad ya hada kayansa, shiri yayi sosae na barin kasar zuwa Egypt Ko Allah zae sa yaga Meenal, Ko da kuwa bazata masa magana bah.
To be continued
Shadaudau Writers✨✨
YOU ARE READING
Meenal
RomanceMEENAL✨ ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Meenal yarinya ce mai matukar Kyan gaske, wadda ta taso Cikin gata, samun yarinya mai gatan meenal sae an duba. Ta kasance Tana da shekaru 18. Iyayenta yan asalin Egypt neh, as a result of that she was born and raised in Egypt...