Episode 7

519 29 0
                                    

MEENAL✨
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
EPISODE 7
Juyawa yayi ya kalli bodyguard din da Keh left side dinsa yace ka sa a bi yarinyar nan gida a kawo min address din. Nan suka bar Airport din, mota 2 na bin Meenal ragowar sun tafi kai Ahmad gida.

Da gan-gan Meenal ta dinga yawo Cikin garin Kano for almost 2 hours daga karshe ta yanke shawarar komawa gida, black Prado din na biye da ita har suka isa gida. Shiga tayi tai parking da gudu ta wuce dakinta.

Ahmad na zaune a parlor yana Shan avocado wani security ya shigo, fari ne tass yana da kiba madaidaiciya, Excellency mun bi yarinyar har zuwa gidansu, and here is the address sir! Ya fada yana mika masa wata white paper me dauke da golden rubutu. Murmushi Ahmad yayi, ya masa godiya hade da karbar takardar yayi mota.

Meenal na zuwa gida ta Kira Ya Ammar, Sanar dashi tayi ta hadu da Ahmad har ma yasa a biyota har gida. Tsaki yayi yace "hope he's not a Nigerian?" ""La'aarif Wallah ya Ammar!" Ta fada a takaice. Fada ya shiga yi mata kan kafin ma ta bari ya shiga ranta ta fara tabbatar da asalinsa domin kuwa tasan auren Wanda ba Arab bah is prohibited a culture dinsu. Shiru tayi bayan ta gama wayar, jikinta yana bata cewa Ahmad bai yi kama da balarabe bah, hasali ma Ko larabcin bai iya bah. Wani irin kuka ta fara mai ratsa zuciya. Bata son rabuwa da familyn ta kuma hukuncin da zaa mata kenan in har tace zata auri Ahmad. Cikin sanyin jiki ta mike ta nufi bathroom, alwala tayi tai sallah, ta dade Tana rokan Allah kan ya kawo mata mafita.

The following day, around 8pm Ahmad ya shirya tsaf Cikin wata alkyabba ba karamin kyau yayi bah a matsayin sa na dan hausawa, Cikin nutsuwa ya nufi parking lot, daddy na hangensa ta sama yayi saurin kiransa a waya, "Son Ina zaka fita neh?" Daddy ya tambayesa, " Dad! Yanzu zan dawo bah nisa zanyi bah" tsawa dadddy ya daka masa "don't tell me you're going to drive yourself?" Shiru Ahmad yayi chan after about 5 seconds yace "yes dad, I don't want any security, inda zanje is well secured! "Will you hush up! Ka bari drivers su kai ka!" Daddy ya fada hade da katse Kiran. Baa son ran Ahmad wasu securities suka raka shi zance vah. Daya daga Cikin securities yasa suka shiga Cikin gidansu Meenal don kiranta.

Meenal na zaune a parlor Tana cin gurasa da miyar dabino wadda aka yi garnishing da inibi, mutum ta gani a kanta yana zare idanuwa, "idan kece Meenal kije waje oga na San ganin ki" abinda mutumin ya furta kenan. Shiru tayi Tana kallonsa, ji tayi kamar magana ya ke sai dai kash! ba yaren da take fahimta bane. Amma wani bangaren na jikinta yake fada mata sallama yayi hade da tambayanta in da Aby dinta yake? She smiled hade da nuna masa kujera "Wa Alayk Salam, Abi zahaba ilal masjid" sae yanzu mutumin ya gane gidan larabawa ya shigo "kuttmar ubanchan, Ni da Ko islamia banyi bah" Mikewa yayi ya fita daga parlor, parking lot ya nufa ya shiga Cikin mota, ya kalli Ahmad "excellency yarinyar nan fah Tana ciki Amma wallahi bata Jin Hausa in fact she seems to be Arab".  "No wonder that's why she's extremely gorgeous" Ahmad ya fada under his breath a fili kuwa yace "take me to her"

Mutuwar tsaye Ahmad yayi ganin Meenal a zaune sanye da riga da Wando gashin nan ya rufe mata fuska har ma wuyanta gaba daya, Assalamu Alaykum! Ya furta a hankali. Murmushi tayi hade da amsa masa sallama, bata wani damu da Kayan da suke jikinta bah saboda a culture dinsu its normal ma yarinya ta fita da Wando unlike the Hausas, it's an abomination.

Bayan Ahmad ya zauna ya kalleta, murmushi kawae yake mata ya rasa da yaren da zae fara mata magana, shi bai iya Arabic ba ita bata Jin Hausa, chan zae zuciyarsa ta raya masa wani abu, tunanin gwada yi mata English yayi, How are you?" He asked, luckily for him ta amsa masa a takaice "fine" ajiyar zuciya yayi cike da nishadi, ba karamin dadi ya ji bah Jin Meenal dinsa ta iya English. "My name is Ahmad, I once met you at Cairo international airport few months back, and actually I fell in love with you, I'm 30 years old, born and raised in Kano state Nigeria, I've only one sister named Amysha, she's nice and kind, you'll get to know that after we got married. Ya fada yana murmushi. Kallonta yayi, from all indications bata fahimci abinda yace bah. Murmushi kawae ta sakar masa ta maida kanta ga film din da take kallo,  yake ya mata Wanda ya fi kuka ciwo Cikin sanyin gwiwa ya nufi bakin kofa, ya juyo kallonta ya karayi kamar bata San yana gurin bah. Wayyo Allah! He said under his breath. Ya fita yana murmushin takaici.

Dariya Meenal tayi yayin da ta furta tsantsar son da take masa a fili, hade da janyo pillow din da ke kan royal chair, I enjoy the moment! She whispered.

One week after, Ahmad ya shiga Cikin damuwa, al-amura sun rikice dole yana bukatar dawowar yar uwarsa mysha. Anya zata taimakesa ? He asked himself, he eventually calmed himself and develop some confidence ya shirya don kuma zuwa gurin Meenal gwada sa'arsa.

Mai gadin gidansu bashi da wata matsala, babu tashin hankali ya bar Ahmad ya shiga gidan, wannan karon Tana garden Tana wasa da green leaves ya shigo, murmushi yayi da ya hangeta sanye Cikin wata jar riga da wani gajeren farin Wando, kamar kullun yau ma kanta babu dan kwali Ko ribbon sakinsa tayi yana sheki. Bata Ankara bah sae ji tayi ance Meenal! A Gigice ta juyo Tana dube dube, ganin wannan saurayi yasa ta harde fuska "How are you" ya tambayeta she smiled "fine", ya dan gyara tsayuwarsa, how is mom and dad, studies and life ? Kallonsa tayi ta furta "fine" tun abin na basa Dariya har ya fara bata masa rai, Cikin fushi yace Apart from "fine" which other word do you know in English? He asked, murmushi tayi dai still Tana kallonsa. Within few minutes ta gama wasa da leaves din ta bar gurin Cikin takun Jan hankali, he stood there speechless. Nikam Aunty Maryam nace shadaudau.

Lokaci na ta tafiya Meenal da Ahmad babu wani chanji har yanzu babu wani communication tsakanin su sae dae yaje ya ganta tace masa "fine" ya tafi.

Thursday morning, kwance mysha take Tana tunani, ganin time zae kure yasa tayi saurin tashi zuwa Airport domin kuwa yau zata koma Nigeria tunda ta samu Hutu har na 2 months. Wajen karfe 11 na safe jirginsu ya tashi around 3:30 suka sauka, ta fito Tana Jiran ganin Ya Ahmad wasu irin cars ta gani suka ta jiniya a Airport din, Ahmad taga an budewa mota ya sauko, Ina! da gudu ta fada jikinsa hade da rungume shi ya jata har Cikin mota.

A hanya Mysha ta kalli ya Ahmad, why this changes ? I mean this cars? He smiled☺️just guess ya fada yana kallonta, she frowned her face a little, "common Brother just say it" ta fada Tana wasa da fingers dinsa. Ki sa ido kiga inda zamu sae Ki tabbatar da kanki. Daga fuskar da zata yi taga sun shiga government house, zaro ido tayi "don't tell me daddy ya ci zabe" kashe mata ido daya yayi "yes!" Wani irin ihu tayi "gobe sae Kowa da ke garin nan yasan daddy's girl ta dawo Kano, nayi iskanci na babu hujja balle yanzu da nake the one and the only daughter to the governor of Kano state.

Bayan ta huta ta fito parlor, security ta Kira yana shigowa tace ya shirya mata motoci Benz 10 prado 10 zata shiga shoprite.
Nikam nace shadaudau

To be continued
Shadaudau Writers ✨

Meenal Where stories live. Discover now