Episode 3

623 34 0
                                    

MEENAL✨
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
EPISODE 3
Mamaki neh ya hanashi furta komae har ta bar gurin, Amma duk da haka ba karamin bala'in birgeshi tayi bah, babu abinda yake so a rayuwar sa irin yaga mace masifaffiya, kyakkyawa, mafadaciya, balarabiya, me dimple hade da hushiriya, doguwa and of course chubby, absolute figure 8, wadda kuma ta kware a iya yarensaaa ma'ana Arabic da kuma English, in short wadda ta fito daga jinsin larabawa. Hannunsa rike da kuncinsa, babu abinda yake maimaitawa sai sunanta da ya ji ta fadi, something like Mysha! Kamar haka yaji tace, ya kalli Abid yana mai murmushin takaici, "ba dae ta shigo kasar bah, zan ta nemanta har zuwa ranar da zan dau fansa" abinda ya iya cewa kenan daga bisani suka bar gurin.

Washe gari da safe, Ammar ya shirya tsaf Cikin wata bakar suit me ratsin fari, comb ya dauko ya taje sumarsa, Ammar kyakkyawan saurayi neh Wanda ya amsa sunansa namiji, kai tsaye ya tafi harabar hotel din da yake zaune, wata bakar mota naga ya shiga within few seconds ya tashi motar straight to prince Naïf ibn abdulazeez, Al-jamiah, medina Saudi Arabia.

Zaune yake a office dinsa dake faculty of shariah, mutane sae shige da fice suke harkar registration. Yana Cikin typing wani document yaji anyi knocking door din, Cikin siririyar muryarsa ya furta "Yes! Come in!" A hankali ta murda murfin kofar hade da shiga Cikin office din, gaban ta neh ya yanke ya fadi ganin fuskar wanda bata taba tsammani bah, mutumin da ta Mara a Airport shine one of the staffs na makarantar da zata fara, developing confidence tayi Cikin nutsuwa tace Assalamu Alayk!, ba tare da ya dago bah ya amsa "wa alayk Salam ya uktee" cike da confidence take magana, "Sir, course din da nayi applying ba shi kuka bani bah, nayi applying Arabic kun bani Law/shariah and seriously I am not interested in....kafin ta karasa maganar ta wayar ta ta hau ringing, kamar bazata daga va sae taji yace "feel free, pick your call" still bai dago bah balle yasan da wa yake magana. Cikin nutsuwa ta daga Kiran, "Assalamu Alayk ya habebaty!" Daga chan daya bangaren friend din ta ta, ta amsa Cikin harshen Arabic hade da tambayartaaa yanda take, mysha ta amsa "Ana bi kyar Alhamdulilah ya uktee, mafy mishkila" larabcin da yaji yarinyar Tana yi neh yasa shi dagowa domin kallon fuskarta, mikewa tsaye yayi Cikin mamakin ganin fuskar da ba zai taba
Mantawa bah, fuskar wadda ta wulakanta sa, ita kuwa Ko a jikinta, tayi sallama da friend dinta, ta cigaba da maganarta "Like I was saying, banason Law din da aka bani, I prefer Arabic than...bai bari ta karasa maganarta bah, "please! Is not possible a miki changing course, you can leave and ..... knocking kofar da akai neh yasa yae shiru, ita kuwa ganin Ana ta knocking yaki magana kawae tace "yes! Come in" confidence din mysha har mamaki yake basa, wani guy neh ya shigo sanye da farar riga, ji tai yace "Assalamu Alayk ya Ammar, sae kuma ya fuskanto ta "wa ukte" hararsa tayi "do I look like your sister? Tsaki tayi ta bar office din hade da buga kofar.

A chan gida Nigeria kuwa, Meenal na gani kwance a kan gado tana waya da kakarta, fada ta shiga yi mata Akan rashin zuwa gaida su tunda suka tafi, da kyar ta samu ta shawo kanta hade da yi mata alkawarin Cikin satin nan xata xo, sun dade suna wayar daga bisani ta kashe wayar hade da Jan blanket ta rufe jikinta bacci mai nauyi ya dauke ta.

2days after, meenal ta hada kayanta kala 7 domin kuwa sati daya daya zata yi a chan, karfe 8 bayan sallar isha tayi sallama da yen gida driver ya kaita har airport bai dawo bah har sai da jirginsu ya tashi zuwa Egypt, Cairo. Murmushi neh dauke a fuskarta lokacin da suka sauka, farin ciki ya mamaye ta Jin kamshin kasarta ta haihuwa, a hankali take saukowa daga Cikin jirgin, passport hade da wani abu kamar wallet ta gani sun fado daga hannun wani saurayi, tsugunawa tayi ta dauka Cikin nutsuwa ta bude passport din, Ahmad ta ga an rubuta, don haka ta nufi gurin Wanda taga ya yarda passport din, "Assalamu Alayk" ta furta, juyowa yayi suka hada ido, "Fatabarakallahu Ahsanil Kaliqin" abinda ta furta kenan Cikin ranta. tsayawa yayi yana kallon halittar ubangiji, gaba daya ta kwance masa tunani, kyanta ya haukata sa, ganin basa da niyyar amsa mata illa kura mata idanuwa da yayi babu Ko kiftawa, yasa tayi gyaran murya, "Dama naga ka yarda passport Dinka neh" ta fada Cikin harshen larabci, bai fahimci abinda take fada bah, saboda shi in Banda sallama da wasu surori a Quran tho bai iya komae bah dangane da wannan harshen, Ko zaginsa xaka yi bah bazai San kana yi bah. Still gani tayi bai amsa mata bah, sae kawae ta mika masa passport din ya karba ta juya ta nufi parking lot. He stood there speechless, bai taba Jin yana son wata mace a rayuwar sa kamar meenal bah, gashi Ko sunanta bai sani bah.

To be continued

Meenal Where stories live. Discover now