MEENAL✨
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
EPISODE 6
Kara kura mata kallo yayi, tabbas Meenal dinsa ce, take ya fadi kasa yana me wa Allah sujjada, Allah ya karbi adduarsa, ya nuna masa uwar yaran sa a zahiri, dagowar da zai yi, yaga babu ita babu alamar ta, does that mean na Kara rasa matata? Abinda yake Kara tambayar kansa kenan. It's all my fault, na dinga rokan Allah ya nuna min ke a zahiri instead of ya mallaka min ke. Wani dogon tsaki yaja, ya dan samu relief babu laifi, tunda yanzu ya tabbatar ta dawo Nigeria.A kwana a tashi kullun Ahmad sae yaje Airport Ko zae ga Meenal, duk Sanda jirgi zae tashi zuwa Egypt sae yaje ya duba faces din mutanen da zasu tafi for almost a month kenan.
Kwance yake a falo yana Shan potato porridge with garlic sauce mummy ta shigo falon, Ahmad! Ta Kira sunansa Tana kokarin zama, nikam Ahmad yaushe zaka je Egypt neh, akwae wasu kaya da nakeso ka siyo min. Kallonta kawae Ahmad yayi, ya danyi yake "mummy me zanje nayi a Egypt kuma for god sake ?" Lokaci daya ta bata rai, wace irin magana kake Ahmad? Da ubanka kake zuwa yi sai yanzu don nawa Aiken ya tashi sai ka wani ce min me zaka je kayi?" Mummmyyyy! Abinda nake zuwa nema Egypt din ya dawo Kano, ni bazan Kara zuwa bah. Yana fadin haka ya fice daga falon.
Ahmad yayi niyyar tafiya Makkah Amma daddy ya hanasa saboda ganin lokacin Zabe yayi, alhaji ismaeel Hydar shi ya tsaya a takarar governor and Alhamdulilah ya ci. Bayan kwanaki da yin zaben Ahmad ya tafi Makkah domin gabatar da umrah. Kamar yanda yayi wanchan karon kwana daya a Jedda, 2 a Makkah 2 a medina, yafi son yin haka saboda ya tashi ta medina.
Wannan karon Ahmad ya biya makarantar su mysha suka gaisa before ya wuce Airport.
Meenal!! ta'al eelaa huna! Ammar neh ke Kiran Meenal Cikin daga murya, da Sauri ta karasa inda yake Tana yafa mayafi, hannu ta nuna masa alamar su tafi, ko kallonta bai yi bah sae ma wani dan tsaki da yayi, parking lot suka nufa ita dashi within seconds suka bar gidan. Aminu Kano international airport suka wuce domin kuwa Yau neh Ammar zae Koma gurin aikinsa dake madina.
Jiniya kawae ce take tashi a Airport din Kano, wasu irin motoci neh black suke ta faman wucewa, domin tarar dan governor Ismaeel Hydar wato AHMAD! A hankali ya fito bodyguards suna take masa baya, a daedae lokacin Meenal ta fito daga raka ya Ammar zata koma mota, red carpet ta gani, she was confused saboda bata taba ganin hakan bah tunda suka xo kasar, ba tare da ta kula bah ta bangaje bodyguard din dake gefen Ahmad, dagowa yayi Cikin fushi, fuskar sa baka ce kamar charcoal, Why are you so very stupid ? Tunda muka shigo kin ga wani yayi motsi? Sae keh? Keh yar gidan uban waye? Sam bata fahimci me yake fada tunda ita ba gane hausar take bah, abu daya ta gane, cewar da yayi "why are you so very stupid" murmushi kawae tayi ta kallesa "Ana Asaf!" Dan kallon gefen sa Ahmad yayi, Cikin hanzari ya sauke shade din da ke zagaye da idanunsa, hakika Ahmad ya girgiza, yarinyar da ya dade yana nema ita ce yau a gabansa. Allah kenan me yin yanda yaso. Sannu baiwar Allah! Ya fada yana kallonta. Ji yayi tayi shiru kamar ba da ita yake vah, hello! What's your name please? Ya Kara tambaya. Wannan karon ta dan fahimta sae tace Ana ismee Meenal! Abinda ta furta masa kenan ta juya zata tafi Cikin Sauri yace hold on! Wait!. Ta tsaya Chak ba tare da ta juyo bah. Ya karasa gaban ta "there was a time in Cairo international airport, I am Ahmad, I mistakenly lost my passport... you give..I mean gave me back? Do you recall?" Ya fadi hakan muryarsa na rawa Ko turancin ma baya fita. Chak Meenal ta tsaya Tana kallonsa Cikin zuciyarta tace "Ana bahibbak! ( I love you in Egyptian Arabic )
A fili kuwa girgiza kai tayi kamar bata gane abinda yake nufi bah tace me? Egypt? Airport? Passport? Ahmad? La!" Da gudu ta tafi mota ta shige iska ta dukan gashin kanta.To be continued

YOU ARE READING
Meenal
RomansMEENAL✨ ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Meenal yarinya ce mai matukar Kyan gaske, wadda ta taso Cikin gata, samun yarinya mai gatan meenal sae an duba. Ta kasance Tana da shekaru 18. Iyayenta yan asalin Egypt neh, as a result of that she was born and raised in Egypt...