Zeenarth's POV
Washe gari da daddare bayan sallan isha'i, zeena da innata suna zaune kan tabar a tsakar gida suna cin tuwon dare, inna ta dago bayan ta cire hannun ta daga kwanon tuwon tayi hamdala ta mike ta wanke hannu, sannan ta dawo ta zauna, tace "autan inna nayi tunani mai zufi akan maganan aikin nan da mukayi jiya, nakuma yanke shawarar zaakiyi aikin, amma bisa sharaadi daya zaki rike mutun cinki a duk indaa kike sannan zaki rike talauci da marai cin ki, ki tsaya iya matsayin ki, karki bari shedan la'ananne ya rijayeki ki aekata abinda zai zubar miki da kima da mutun ci a idon duniya, kiji tsoron Allah, nasan nabaki tarbiya iya iyawataa sannan na kuma yarda dake dari bisa dari, naasan bazaki bani kunya ba"..
Zeena ta cire hannunta daga kwanon tuwon ta maida hankali da nutsuwar ta duka ga inna, bayan ta kammala sauraron innaa tace "inna nagode, InshaAllah bazaki yi nadaman barina yin wannan aikin ba, kuma da ikon Allah sai kinyi alfahari da wannan aekin nawa InshaAllah badai kiyi kuka dani ba, kuma zan rike mutunci, da matsayi na InshaAllah, nagode sosai innata."
Ta rungime innan tana hawayen farin ciki...Bayan sun dan taba hira kadan inna ta mike tama zeena sai da safe sannan ta shige dakin ta, zeena ko mikewa tayi ta tattare kwannukan da suka ci abinci ta kai kitchen sannan itama ta shiga dakin ta dau brush dinta ta fita tsakar kida tayi brushing bakinta, tayi alwala sannan ta dawo daki ta rufo kofar ta changer kaya zuwa night gown dinta sannan ta kwanta, adda'an bacci tayi ta kashe wuta, bacci ne yaki daukan ta sai tunanin da ya ki barinta cikin kwananin nan na yadda zata iya yin aeki da mutumin da ta mato akan sa, wanda son shi yahanata ganin kowani da namiji a matsayin na miji, taya-taya zata iya,
Wani bangare na zuciyar ta ne ya bata amsa da ta yadda kika iya yin shekara hudu da son wanda bai San dake ba, dole ne ki dauki wannan kaunar da kike mai kisa shi cikin akwatin karfe ki rufe shi daa kwadon kuba, ki jefashi cikin kar kashin zuciyarki yadda ko kin ganshi ba zaki nuna wani effect ba, to tahaka ne kawai zaki iya yin aeki a kasan sa, kai ta girgiza cike da gamsuwa da shawarar da zuciyar ta ta bata tace haka ne dole sai na kawar dashi a raina, basa aekina first before anything,
A haka bacci ya dauketa....Washegari da sassafe ta tashi ta share tsakar gida tayi wanke wanke, sannan ta dama musu kunu ta shiga wanka, bayan ta shiya lokacin karfe 7:30 ta fito ta shigaa dakin inna ta yi mata sallama ta fita, ta tari mai ADDS ta fada mai address din da zata, abakin A.A fashion design empire ya sauketa bayan ta sallame shi, ta nufi ciki, yau kai tsaye wajen general elevator tanufa bayan ta d'agama receptionist din wajen hannu 👋🏽, shima waving 👋🏽 yamata yana murmushi, Dan ya gane ta, tana shiga ta danna 5th floor, lift din yana budewa ta nufi wajen receptionists din dake floor din ta mata sallama, matar ta amsa mata da "hi what can i help you with"
Zeena ta fada mata gun wacce tazo, matar ta nuna mata office din wannan matar sannan ta shiga, zaune kan office chair ta tarar da matan ranan, waje tanema ta zauna sannan ta mika mata hannu sukayi shaking 🤝🤝
Sannan matan tace "glad you're back, hope you have a good news?"
Zeena tai murmushi tace yeah kind of,"
Matar tace "good hope she let's you take the job?"
Zeena tace "yeah, glory be to Allah, i can say the job is now mine😊,"
Matar tace "good, so here are some papers you need to fill up and sign 📋"
Zeena ta sa hannu ta karba ta karanta sannan ta filling tayi signing ta mikawa matar
Matar tace karba tace "welcome to the club girl 😊🤝"
Zeena tace "thank you"
Bayan matar ta adana paper din a cikin wani file 📁 ta dago tacewa zeena "so now i have to tell you his every rule and regulation, and how your work works, I hope everything will work out fine with you,"
Zeena tace "I hope so too"
Matar tace "As I believe you know the history of this company, and the name of the owner and the owners son who's now the C.E.O of the empire and your new boss, so lemme Just take you straight to the point, Mr.Adams is a 29year old bachelor billionaire, youngest business man ever, but not only the youngest but the smallest, careless, arrogant and a very moody one, he is smart when it comes to his company, but unfortunately when it comes to women and social life he's not the brightest, love is a joke to him, caring too is a big joke to him, he is a very cold hearted person, who makes his work his first priority, that's why almost all of his secretaries A.K.A personal assistants doesn't last long, because they think that they can't handle his arrogance attitudes, so some fired them self's while the other got fired from him, and that makes it even harder to get him a personal assistant nowadays, and i hope you can make a difference".
Zeena ta sauke ajiyar nunfashi bayan gama sauraron dogon jawabin nan a kan boss dinta kuba crush din ta.
Tace "InshaAllah i will make a difference because me too this work is my first priority, it means a lot to me, i can't take any risk to lose my job".
Matar tace "good, I think i made a wise move by giving you this job, you're just the perfect person for it, don't disappoint me"
Zeena takalli yar taddi juwar matar da bazata wuce in her early 50s ba, taji matar ta kara kwanta mata a rai tace "InshaAllah i will never disappoint you"....
YOU ARE READING
BAI SAN DANI BA (THE GIRL HE NEVER NOTICED)
RomanceHe's rich, she's poor, he have it all, she have nothing, he's a multimillionaire, the CEO of A.A FASHION DESIGN EMPIRE, she's just a girl with big dreams.. They meet by accident, she loves him so much, she's the girl he never noticed, she dedicated...