Chapter 10

1.6K 158 23
                                    

Zeenarth's POV

Tsaye take bakin building din tana kallo, hannu ta daga sama tana tace Alhamdulillah ya Allah da ka nuna min wannan rana a rayuwa ta, bismillah tayi hade da tura kofar main entrance din building din...

Direct 36th floor ta wuce, tana isa bata tsaya ko inaba sai cikin cafeteria, zama tayi tana jiran time ya cika, sanye take da ash color dress 👗 tai rolling kanta da black vail hanun ta rike da black mini bag 👝 jikin sa anyi ado da ash stones, ta sa black shoes 🥿, wayar ta, ta dauko daga cikin jarkar ta, yar karama kirar Nokia ta duba time 9:00am dot, mikewa tayi ta matsa jikin coffee ☕️ machine din ta fara hada mai black coffee, kamar yadda miss Britney ta fada mata haka ta hada, ta daura cup ☕️ din a kan tray ta nufi office din Aryan dashi....

Aryan's POV

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.



Aryan's POV

Ya na isowa packing motar sa yayi a packing space2 din dake cikin building din, ya fito ya bude baya ya dauko briefcase 💼 din sa ya rufe motar ya nufi kofar personal elevator din sa dake cikin wajen ya shiga..
Yan isa floor din sa direct office din sa ya nufa, shiga yayi ya zauna hade da daura briefcase din nasa bisa desks din gaban sa, hanu yasa yana shirin daukan landline ☎️ din dake kan table din, knocking a kayi jikin kofar office din, hannun sa ya maida kan wani dan karamin button dake kijin table din, kofar ce ta bude, ya juya ya fara ciro documents din dake cikin briefcase dinsa batare da ya ko kalli wanda zai shigo ba....

Zeenarth's POV

Ta kusan 3mints a bakin kofar office din, amma ta kasa d'aga hannu tayi knocking, zuciyar ta ce take harbawa tamkar zata tsago kirjin ta ta fito, hasbinallahu wani'imal wakil, ta shiga waran towa cikin zuciyarta, sai da ta dan samu nutsuwa tukun ta sa hannu tai knocking kofar, bisa ga mamakin ta sai gani tayi kofar ta bude da kanta, mai da kallon ta, tayi cikin office din kallo tabi room din dashi sakamakon irin k'ayatuwar da yayi, in kana ciki bazaka ce a Nigeria kake ba, idon ta ta sauke kansa yana ta harkar gaban sa kamar ma bai sanda tsayuwar mutum bakin kofar ba, ido ta zuba mai tana kallonsa kirjin ta sai faman bugawa yake, she can't believe wai yau itace tsaye a gaban mutumin da ta rayu tana tattalin son sa, kuma wai a matsyin ta na employee din sa, Lallai ba yadda Allah bayayi a rayuwar dan adam.. tayi nisa cikin tunani bata an kara ba sai ji tayi yace "if you're not coming in, you better get lost before you ruin my mood"
Duk magana da yake har yanzu bai d'ago ya kalle ta ba, jan kafar ta tayi a hankali dan ji take tamkar bazata iya daukan ta ba, any minute from now gani take kamar zata iya faduwa, ta shiga cikin office din, bakin table din sa ta tsaya hannun ta rike da tray din coffee din,
A hankali cikin wani kasalalliyar murya ta furta "morning mr Adams, where should i place the coffee ☕️?",
Har yanzu bai dogo ya kalleta ko sau daya ba ya dan matsar da wasu takardu gefe, ya kara mai da hankalin sa kan aekin da yake, hakan da yayin ne ya kabbatar mata da yana nufin a nan zata aje masa, cikin sanyin jiki ta aje masa cup din coffee ☕️ din a wajen tadan matsa gefe ta tsaya, ji tayi yace "have a seat"
Ba musu ta zauna a daya daga cikin kujerun da suke gaban table din nasa, shiru tayi tana jiran taji mai zai ce amma kusan mintuna 15 dazamanta har yan zu bai ce komai ba, kuma bata ga alamun yana da niyar yin magana nan kusa ba, hanu tasa ta bude jakar ta, ta ciro chewing gum ta bude ta sa a bakin ta ta shiga taunawa, kusan 5minutes amma still har yanzu bai dago ba kuma bai ce mata komai ba, time to time dai yakan dauki coffee din sa yayi sipping, ita dai ta zauna tana cin chewing gum din ta tana kallon ikon Allah, azuciyar ta tace mutum sai shegen ego 😏, ta sahannu ajaka ta dauko yar wayar ta tashiga latsawa abun ta...

Aryan's POV

Tun da ya bude kofar ya cigaba da harkar gaban sa bai dago ba, jin shiru ba'a shigo bane yasa yadan dago ya kalli kofar, tsaye take hannun ta rike da tray da cup din coffee a kai, ko ba a fada masa ba itace sabuwar P.A din sa wacce miss Britney ta fada mai ta sama, kallon ta yayi sama da kasa, kakkyawa ce ajin farko, dugowa ce, fara, sanye take da ash color long dress 👗, yayi matukar mata kyau, dressing dinta so decent bakamar sauran personal assistants din dayayi abaya ba, masu fidda tsirai cin su don su ja attention din sa, duk da kuwa kaf din su Christians ne, wannan itace musulma ta farko, wani abu yaji ya tsaya mai a zuciya game da ita, wanda shi kansan sai san ko menene ba, idon sa ya maida kan takar dun gaban sa yace "If you're not coming in, you better get lost before you ruin my mood".,
Shigowa tayi ta tsaya gaban table din sa hanun ta rike da tray din cikin sanyin murya irin wanda bai taba jiba tace "morning mr Adams, where should i place the coffee,
Kirjin sane yayi wani wawan bugawa sakamakon jin saukar muryar ta tamkar wani melody a dodon kunnen sa, SubhanaAllah ya furta cikin ransa, documents din gefen sa ya dage ya maidasu daya side din batare da ya bata amsa ba dan baya da energy din da zai iya magan a yanayin da yake jin kansa, ya cigaba da abunda yake bawai don hanlakin sa yana kan abinda yake ba, kokari yake ya samu nutsuwar zuciya wanda hakan ya gagara, yana ji ta bude ledar chewing gum tasa a baki ta fara ci, har yanzu zuciyar sa bai gama dai dai ta ba shiyasa bai mata magana ba, jin irin yadda take taunar chewing gum din ne ya fara bata mai rai dan ya tsani yaki mutum yana tauna cingum yana Kara's k'aras, cike da bacin rai ya daka mata tsawa yana cewa "Will you please stop thet, damn it you're so irritating😠, SubhanaAllah!", hade da buga saman teble din, coffee din da yake gefen sa ne ya watse masa a kan kannu, zafin ruwan yasa yai saurin mikewa hade da fadin wash! SubhanaAllah,
Cikin sauri yaga ta mike ta kallo sa, ganin hannun sa da yake ta faman yarfewa yasa ta mai da idon ta kan table din inda cup din yake, ganin shine ya zuba mai a hanu nan take ta kidime ta nufe shi, har ta kai hannu zata rike hanun nasa, sai kuma ta fasa ta nufi wajen fridge din dake cikin office din, ta bude ta dauko ruwa mai sanyi na roba, ta karaso inda yake cikin sauri ta bude hade da kama hanun nasa ta shiga zuba mai ruwan, tana hura hanun da bakin ta, tsayawa yayi kamar statue yana kallon yadda tabi ta kidime tashiga damuwa wanda ko shi da ya kone bai shiga ba....



Xoxo 💋🥰💋🥰💋🥰

BAI SAN DANI BA (THE GIRL HE NEVER NOTICED) Where stories live. Discover now