Chapter 13

881 76 34
                                    

Aryan POV

Yana isa gida wanka yayi ya shiga "Walk in closet" dinsa ya dauko gajeren wandon jeans na "vans Hannon" da tank top din "WUAI-Men fashion" yasa yaje ya dauko designer slippers na "HOT Rivet" ya feshe jikinsa da turaren clinic for men.

Vans Hannon  designer jeans short

 WUAL-Men fashion designer tank top

¡Ay! Esta imagen no sigue nuestras pautas de contenido. Para continuar la publicación, intente quitarla o subir otra.

WUAL-Men fashion designer tank top.

 WUAL-Men fashion designer tank top

¡Ay! Esta imagen no sigue nuestras pautas de contenido. Para continuar la publicación, intente quitarla o subir otra.

HOT Rivet designer slippers.

Kitchen yashiga ya bude fridge ya dauko leftover bugger sauran wanda yaci jiya yayi worming disa a Oven, ya dauko potatoes yayi filling din su, yayi slicing dinsu, bayan ya gama ya wanke ya soya, ya dauko robber coca cola ya jute cikin glass cup y...

¡Ay! Esta imagen no sigue nuestras pautas de contenido. Para continuar la publicación, intente quitarla o subir otra.

Kitchen yashiga ya bude fridge ya dauko leftover bugger sauran wanda yaci jiya yayi worming disa a Oven, ya dauko potatoes yayi filling din su, yayi slicing dinsu, bayan ya gama ya wanke ya soya, ya dauko robber coca cola ya jute cikin glass cup yasa ice cubes a ciki,  kan Dining table yaje ya zauna ya dauko newspaper yana dubawa yana cin abincin.

ARYAN's dinner

Bayan ya kammala cin abincin yasa plate din cikin Dishwasher ya rufe, daya daga cikin kitchen cabinet na kitchen din ya bude ya dauko fastaid box daga ciki ya dauko panadol extra ya balla ya dauruwa yasha ya maida aids din Inda yadauko

¡Ay! Esta imagen no sigue nuestras pautas de contenido. Para continuar la publicación, intente quitarla o subir otra.

Bayan ya kammala cin abincin yasa plate din cikin Dishwasher ya rufe, daya daga cikin kitchen cabinet na kitchen din ya bude ya dauko fastaid box daga ciki ya dauko panadol extra ya balla ya dauruwa yasha ya maida aids din Inda yadauko.

Home office dinsa yashiga dan yarage wasu aeyukan, bai gama  ba sai wajen 11:30 na dare sallah kawai ke tsayar dashi,
Daki yashiga ya cire kaya yasa Pyjamas, shiga bathroom yayi, yayi brush da Alwala ya hau gado yayi addu'a ya kwanta.

Zeenarth's POV

Kwance take kan katifar ta sai juyi take bacci yaki daukar ta tunani duk ya addabi kwakwalwar ta, duk juyin da tayi shi take tunawa in ta kulle idon ta ma shi take gani, tsayuwar sa, maganar sa, kirar hallittan sa, da kuma zati da izzar sa, isa, gadara da kuma ajin sa, komai nasa burgeta yake, duk wani motsi da zatayi shine makale cikin ranta, so, kwaunar sa da kuma begen sa, kara ginuwa suke cikin ranta, A kullum son sa kara narka zuciyar ta yake, tasan ya mata nisa ya kuma fi karfin ta amma bata tunanin zata iya hakura da son da take masa ta saurari wani, ji take a jikinta da jinin ta tamkar dan shi kadai Allah ya halicce ta, sosai soyyayyarsa ke nukurkusan zuciyarta, bata ankara ba sai jin wani dummammen hawaye tayi yana gangarowa kan kuncinta, tabbas son wannan bawan Allah na dab da yimata illa, gaba daya ji tayi duniyar tai mata zafi, kunci ya mai mayeta ta rasa nutsuwa da sukunin ta.

Mikewa tayi ta dau wayarta ta duba time, karfe 2:30am na dare, mikewa tayi tafita ta zaga bayi tayi tsarki ta fito ta yi alwala, daki ta koma ta dau hijabin ta, ta shimfida sallaya, nafila tayi raka'a biyu, sannan ta zauna tayi tasbihi, ta karanta Ayatul kursi, Amanar rasulu, lakaqja akum, da sunayen Allah kyawawa 99, sannan ta karanta fatiha tace: ya Allah ina tawassali da wannan karatun fatiha danayi dakuma sunayen ka kyawawa, kasa Aryan ya zama alkairi na, ka kaddara aure tsakanin mu, ka sanya so da kwaunata cikin zuciyar sa, ka sa ya fiskan ceni yasan da zamana da kuma irin soyyayyar da nake masa,  Allah ka karkato min da tunanin sa da hankalin sa gareni, kasa yasoni ya kyaunace ni, yaji kaina, ya girmama ni, ya ji kan duk wani nawa, ya kwaunaci duk wani nawa, ya girmama mahaifiyata ya kwaunace ta kwatan kwacin yadda yake kaunar mahaifiyar sa, Allah ka daddara tsabta tacciyar soyayya tsakanin mu, kasa ya zamo mijina abin dogaro na, uban yaya na, Allah in yana da wani mugayen dabi'u wanda kai dashi ne kawai kuka sani, Allah kashiryesa kasa ya gyra ya gane gaskiya, Allah kasa nazamo dalilin shiriyar sa shima ya zana dalilin shiriya ta, Allah ka kareshi da ga sharrin mahassada, makiya da kuma duk wanda yake nemansa da sharri, Allah ka sanya Alkairi a duk abinda ya sa gaba ka bashi sa'a, ka kara daukaka shi. Ameen 

Sannan tayiwa iyayen ta addu'a da ma ita kanta, bayan ta idar addu'ar sai ta karan ta wannan Addu'an

Du'a for marrage

رَبِّ إِنِّى لِمَآ أَنزَلْتَ إِلَىَّ مِنْ خَيْرٍۢ فَقِيرٌۭ
Rabbi inni lima anzalta ilayya min khairin faqir

Sannan ta karanta wannan addu'an
Addu'ar samun duniya da lahira mai kyau
ربنا آتنا في الدنيا حسنة وفي الآخرة حسنة، وقنا عذاب النار
Rabbana atina fid dunya hasanah wa fil akhirati hasanah wa qina 'adhaban nar

Sannan takaranta suratul Ikhlaas, falaq da naas, tayi salatin Annabi da istigfari ta shafa. Mikewa tayi ta hau katifar ta, ta kwanta, nan take taji ta samu nitsuwar zuci da kwaciyar hankali, batasan sanda bacci yayi awun gaba da ita ba.




XoXo 🖤❤️

Has llegado al final de las partes publicadas.

⏰ Última actualización: Nov 06, 2020 ⏰

¡Añade esta historia a tu biblioteca para recibir notificaciones sobre nuevas partes!

BAI SAN DANI BA (THE GIRL HE NEVER NOTICED) Donde viven las historias. Descúbrelo ahora